< Ishaya 15 >
1 Abin da Allah ya yi magana a kan Mowab shi ne, An lalatar da Ar a Mowab, an hallaka ta da dare! An lalatar da Kir a Mowab, an hallaka ta da dare!
モアブにかかる重負のよげん曰く モアブのアルは一夜の間にあらされて亡びうせモアブのキルは一夜のまに荒されてほろびうせん
2 Dibon ya haura zuwa haikalinta, zuwa masujadan kan tudu don tă yi kuka; Mowab ta yi ihu a kan Nebo da Medeba. An aske kowane kai an kuma yanke kowane gemu.
かれバイテおよびデボンの高所にのぼりて哭きモアブはネボ及びメデバの上にてなげきさけぶおのおのその頭を禿にしその鬚をことごとく剃たり
3 A tituna sun sa tsummoki a jikunansu; a kan rufin ɗakuna da kuma dandalin taruwa dukansu sai makoki suke yi, sun kwanta suna kuka.
かれら麁服をきてその衢にあり屋蓋または廣きところにて皆なきさけび悲しむこと甚だし
4 Heshbon da Eleyale sun yi kuka da ƙarfi, aka ji muryoyinsu ko’ina har zuwa Yahaz. Saboda haka mayaƙan Mowab suka yi kuka da ƙarfi, har zuciyarsu ta karai.
ヘシボンとエレアレと叫びてその聲ヤハズにまで聞ゆこの故にモアブの軍兵こゑをあげその靈魂うちに在てをののけり
5 Zuciyata ta yi kuka a kan Mowab; mutanenta sun gudu har zuwa Zowar, har zuwa Eglat Shelishiya. Sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka; a kan hanyar zuwa Horonayim suna makoki saboda hallakawarsu.
わが心モアブのために叫びよばはれりその貴族はゾアルおよびヱグラテシリシヤにのがれ哭つつルヒテの坂をのぼりホロナイムの途にて敗亡の聲をあぐ
6 Ruwayen Nimrim sun ƙafe ciyayin kuma sun bushe; tsire-tsire duk sun ɓace babu sauran ɗanyen abu.
ニムリムの水はかわき草はかれ苗はつきて緑蔬あらず
7 Saboda haka dukiyar da suka tara suka kuma ajiye sun ɗauka suka ƙetare Rafin Arabim da su.
このゆゑに彼等はその獲たる富とその藏めたる物をたづさへて柳の河をわたらん
8 Ƙugin kukansu ya kai ko’ina a iyakar Mowab; kururuwarsu ta kai har zuwa Eglayim, makokinsu ya kai har zuwa Beyer-Elim.
その泣號のこゑはモアブの境をめぐり悲歎のこゑはエグライムにいたりなげきの聲はべエルエリムにいたる
9 Ruwayen Dimon sun cika da jini, amma zan yi ƙari a kan Dimon, zan kawo zaki a kan masu gudu na Mowab da kuma a kan waɗanda suka ragu a ƙasar.
デモンの水は血にて充われデモンの上にひとしほ禍害をくはへモアブの遁れたる者とこの地の遺りたるものとに獅をおくらん