< Ishaya 14 >

1 Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
כי ירחם יהוה את יעקב ובחר עוד בישראל והניחם על אדמתם ונלוה הגר עליהם ונספחו על בית יעקב
2 Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
ולקחום עמים והביאום אל מקומם והתנחלום בית ישראל על אדמת יהוה לעבדים ולשפחות והיו שבים לשביהם ורדו בנגשיהם
3 A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,
והיה ביום הניח יהוה לך מעצבך ומרגזך--ומן העבדה הקשה אשר עבד בך
4 za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
ונשאת המשל הזה על מלך בבל--ואמרת איך שבת נגש שבתה מדהבה
5 Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,
שבר יהוה מטה רשעים--שבט משלים
6 wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa.
מכה עמים בעברה מכת בלתי סרה רדה באף גוים מרדף בלי חשך
7 Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.
נחה שקטה כל הארץ פצחו רנה
8 Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
גם ברושים שמחו לך ארזי לבנון מאז שכבת לא יעלה הכרת עלינו
9 Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. (Sheol h7585)
שאול מתחת רגזה לך--לקראת בואך עורר לך רפאים כל עתודי ארץ--הקים מכסאותם כל מלכי גוים (Sheol h7585)
10 Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.”
כלם יענו ויאמרו אליך גם אתה חלית כמונו אלינו נמשלת
11 An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka. (Sheol h7585)
הורד שאול גאונך המית נבליך תחתיך יצע רמה ומכסיך תולעה (Sheol h7585)
12 Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
איך נפלת משמים הילל בן שחר נגדעת לארץ חולש על גוים
13 Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.
ואתה אמרת בלבבך השמים אעלה--ממעל לכוכבי אל ארים כסאי ואשב בהר מועד בירכתי צפון
14 Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
אעלה על במתי עב אדמה לעליון
15 Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami. (Sheol h7585)
אך אל שאול תורד אל ירכתי בור (Sheol h7585)
16 Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,
ראיך אליך ישגיחו אליך יתבוננו הזה האיש מרגיז הארץ מרעיש ממלכות
17 mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
שם תבל כמדבר ועריו הרס אסיריו לא פתח ביתה
18 Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace, kowa a kabarinsa.
כל מלכי גוים כלם--שכבו בכבוד איש בביתו
19 Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
ואתה השלכת מקברך כנצר נתעב--לבש הרגים מטעני חרב יורדי אל אבני בור כפגר מובס
20 ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.
לא תחד אתם בקבורה כי ארצך שחת עמך הרגת לא יקרא לעולם זרע מרעים
21 A shirya wuri don a yayyanka’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.
הכינו לבניו מטבח בעון אבותם בל יקמו וירשו ארץ ומלאו פני תבל ערים
22 “Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta,’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.
וקמתי עליהם נאם יהוה צבאות והכרתי לבבל שם ושאר ונין ונכד--נאם יהוה
23 “Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
ושמתיה למורש קפד ואגמי מים וטאטאתיה במטאטא השמד נאם יהוה צבאות
24 Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
נשבע יהוה צבאות לאמר אם לא כאשר דמיתי כן היתה וכאשר יעצתי היא תקום
25 Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
לשבר אשור בארצי ועל הרי אבוסנו וסר מעליהם עלו וסבלו מעל שכמו יסור
26 Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
זאת העצה היעוצה על כל הארץ וזאת היד הנטויה על כל הגוים
27 Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
כי יהוה צבאות יעץ ומי יפר וידו הנטויה ומי ישיבנה
28 Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
בשנת מות המלך אחז היה המשא הזה
29 Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso,’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
אל תשמחי פלשת כלך כי נשבר שבט מכך כי משרש נחש יצא צפע ופריו שרף מעופף
30 Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo, mabukata kuma za su kwana lafiya. Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa; za tă kashe naka da suka rage da rai.
ורעו בכורי דלים ואביונים לבטח ירבצו והמתי ברעב שרשך ושאריתך יהרג
31 Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni! Ku razana, dukanku Filistiyawa! Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa, kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
הילילי שער זעקי עיר נמוג פלשת כלך כי מצפון עשן בא ואין בודד במועדיו
32 Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”
ומה יענה מלאכי גוי כי יהוה יסד ציון ובה יחסו עניי עמו

< Ishaya 14 >