< Ishaya 13 >
1 Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.
This is the message Isaiah, son of Amoz, received about Babylon.
2 A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma.
Set up a banner on a bare hilltop; shout out to them; wave your hand to encourage them to enter the palaces of princes.
3 Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata.
I have ordered the ones I have chosen to attack; I have called my warriors to execute my furious judgment and to celebrate my triumph.
4 Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
A noise comes from the mountains, sounding like that of a huge crowd! It's the roaring sound from the kingdoms, from nations gathering together! The Lord Almighty is calling up an army for war.
5 Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar.
They are coming from distant lands, from beyond the far horizons—the Lord and the weapons of his fury—coming to destroy the whole country.
6 Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.
Howl in fear, for the day of the Lord is approaching—the time when the Almighty destroys.
7 Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
Everyone's hands will fall limp, and everyone will lose their minds in panic.
8 Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace.
They will be terrified; pain and anguish will seize them; they will suffer like a woman giving birth. They will look in shock at each other, their faces burning in fear.
9 Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
Look! The day of the Lord is coming—cruel, with fury and fierce anger—to devastate the land and to wipe out its sinners.
10 Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
The stars in the constellations of heaven above will not shine. When the sun rises it will stay dark. The moon will give no light.
11 Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
I will punish the world for its evil, and the wicked for their sin, says the Lord. I will put an end to the conceit of the arrogant, and I will humiliate tyrants and their pride.
12 Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
I will make people scarcer than pure gold, rarer than the gold of Ophir.
13 Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
So I will shake the heavens and make the earth jump out of its place because of the fury of the Lord Almighty, at the time when his anger burns.
14 Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
Like a gazelle being hunted, or like sheep without a shepherd, the Babylonians will return to their own people, they will run away to their own land.
15 Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
Anyone who is captured will be stabbed to death; anyone who is caught will be killed by the sword.
16 Za a fyaɗa’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
Their little children will be dashed to pieces as they watch, their houses will be looted, and their wives will be raped.
17 Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya.
I'm going to get the Medes to attack them, people who don't care about silver or gold.
18 Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga’yan yara ba.
Their bows will slaughter their young men; they will show no mercy to babies; they will have no pity on children.
19 Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
Babylon, the most marvelous city of any kingdom, the greatest pride of the Babylonian people, will be demolished by God like Sodom and Gomorrah.
20 Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
No one will ever live in Babylon again. It will be deserted—no desert nomad will set up a tent there, no shepherd will bring a flock to rest there.
21 Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
Only desert animals will make their homes there, and the ruined houses will be inhabited by wild dogs. Owls will live there, and wild goats will leap around.
22 Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.
Hyenas will howl in her fortresses and jackals in her lavish palaces. Babylon's time is coming soon—they will not last much longer.