< Ishaya 11 >

1 Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da’ya’ya.
ויצא חטר מגזע ישי ונצר משרשיו יפרה
2 Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
ונחה עליו רוח יהוה--רוח חכמה ובינה רוח עצה וגבורה רוח דעת ויראת יהוה
3 zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba;
והריחו ביראת יהוה ולא למראה עיניו ישפוט ולא למשמע אזניו יוכיח
4 amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
ושפט בצדק דלים והוכיח במישור לענוי ארץ והכה ארץ בשבט פיו וברוח שפתיו ימית רשע
5 Adalci ne zai zama abin ɗamararsa aminci kuma igiyar da zai ɗaura kewaye da gindinsa.
והיה צדק אזור מתניו והאמונה אזור חלציו
6 Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago damisa za tă kwanta tare da akuya, ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare; ɗan yaro ne zai lura da su.
וגר זאב עם כבש ונמר עם גדי ירבץ ועגל וכפיר ומריא יחדו ונער קטן נהג בם
7 Saniya da beyar za su yi kiwo tare, ƙananansu za su kwanta tare, zaki kuma zai ci ciyawa kamar saniya.
ופרה ודב תרעינה יחדו ירבצו ילדיהן ואריה כבקר יאכל תבן
8 Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa, ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.
ושעשע יונק על חר פתן ועל מאורת צפעוני גמול ידו הדה
9 Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
לא ירעו ולא ישחיתו בכל הר קדשי כי מלאה הארץ דעה את יהוה כמים לים מכסים
10 A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.
והיה ביום ההוא שרש ישי אשר עמד לנס עמים אליו גוים ידרשו והיתה מנחתו כבוד
11 A wannan rana Ubangiji zai miƙa hannunsa sau na biyu don yă maido da raguwar da ta rage na mutanensa daga Assuriya, daga Masar ta Ƙasa, daga Masar ta Bisa, daga Kush, daga Elam, daga Babiloniya, daga Hamat da kuma daga tsibiran teku.
והיה ביום ההוא יוסיף אדני שנית ידו לקנות את שאר עמו--אשר ישאר מאשור וממצרים ומפתרוס ומכוש ומעילם ומשנער ומחמת ומאיי הים
12 Zai tā da tuta saboda al’ummai yă kuma tattara masu zaman bauta na Isra’ila; zai tattara mutanen Yahuda da suke a warwatse kusurwoyi huɗu na duniya.
ונשא נס לגוים ואסף נדחי ישראל ונפצות יהודה יקבץ מארבע כנפות הארץ
13 Kishin Efraim zai ɓace, za a kuma kau da abokan gāban Yahuda; Efraim ba zai yi kishin Yahuda ba, haka ma Yahuda ba zai yi gāba da Efraim ba.
וסרה קנאת אפרים וצררי יהודה יכרתו אפרים לא יקנא את יהודה ויהודה לא יצר את אפרים
14 Tare za su fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi daga yamma; tare za su washe mutane wajen gabas. Za su ɗibiya hannuwa a kan Edom da Mowab, Ammonawa kuma za su yi musu biyayya.
ועפו בכתף פלשתים ימה יחדו יבזו את בני קדם אדום ומואב משלוח ידם ובני עמון משמעתם
15 Ubangiji zai busar da bakin tekun Masar; da iska mai zafi zai share hannunsa a bisa Kogin Yuferites Zai rarraba shi yă zama ƙanana rafuffuka bakwai saboda mutane su iya hayewa da ƙafa.
והחרים יהוה את לשון ים מצרים והניף ידו על הנהר בעים רוחו והכהו לשבעה נחלים והדריך בנעלים
16 Za a yi babbar hanya saboda raguwa mutanensa da ta rage daga Assuriya, kamar yadda ta kasance wa Isra’ila sa’ad da suka fito daga Masar.
והיתה מסלה--לשאר עמו אשר ישאר מאשור כאשר היתה לישראל ביום עלתו מארץ מצרים

< Ishaya 11 >