< Ishaya 10 >

1 Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya, waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,
הוי החקקים חקקי און ומכתבים עמל כתבו
2 don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace.
להטות מדין דלים ולגזל משפט עניי עמי--להיות אלמנות שללם ואת יתומים יבזו
3 Me za ku yi a ranan nan ta hukunci, sa’ad da masifa ta zo daga nesa? Ga wa za ku tafi don neman taimako? Ina za ku bar dukiyarku?
ומה תעשו ליום פקדה ולשואה ממרחק תבוא על מי תנוסו לעזרה ואנה תעזבו כבודכם
4 Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammu ko mutuwa cikin waɗanda aka kashe. Duk da haka, fushinsa bai huce ba, hannunsa har yanzu yana a miƙe.
בלתי כרע תחת אסיר ותחת הרוגים יפלו בכל זאת לא שב אפו ועוד ידו נטויה
5 “Kaiton Assuriya, sandar fushina, a hannun da kulkin fushina yake!
הוי אשור שבט אפי ומטה הוא בידם זעמי
6 Na aike shi gāba da al’umma marar sanin Allah, na tura shi gāba da mutanen da suka ba ni fushi, don yă kwashe ganima yă kuma yi wason ganima, yă tattake su kamar laka a tituna.
בגוי חנף אשלחנו ועל עם עברתי אצונו--לשלל שלל ולבז בז ולשימו (ולשומו) מרמס כחמר חוצות
7 Amma ba abin da ya yi niyya ke nan ba, ba abin da yake da shi a zuciya ba; manufarsa shi ne yă hallaka, yă kuma kawo ƙarshen al’ummai da yawa.
והוא לא כן ידמה ולבבו לא כן יחשב כי להשמיד בלבבו ולהכרית גוים לא מעט
8 Ya ce, ‘Dukan shugabannin yaƙina ba sarakuna ba ne?’
כי יאמר הלא שרי יחדו מלכים
9 ‘Kalno bai kasance kamar Karkemish ba? Hamat bai zama kamar Arfad Samariya kuma kamar Damaskus ba?
הלא ככרכמיש כלנו אם לא כארפד חמת אם לא כדמשק שמרון
10 Yadda hannuna ya ƙwace mulkokin gumaka, mulkokin da siffofinsu suka fi na Urushalima da Samariya,
כאשר מצאה ידי לממלכת האליל ופסיליהם מירושלם ומשמרון
11 ba zan yi da Urushalima da siffofinta yadda na yi da Samariya da gumakanta ba?’”
הלא כאשר עשיתי לשמרון--ולאליליה כן אעשה לירושלם ולעצביה
12 Sa’ad da Ubangiji ya gama dukan aikinsa gāba da Dutsen Sihiyona da Urushalima, zai ce, “Zan hukunta sarkin Assuriya saboda fariya na gangancin zuciyarsa da kuma kallon reni na idanunsa.
והיה כי יבצע אדני את כל מעשהו בהר ציון ובירושלם--אפקד על פרי גדל לבב מלך אשור ועל תפארת רום עיניו
13 Gama ya ce, “‘Ta wurin ƙarfin hannuna ne na aikata wannan, da kuma ta wurin hikimata, gama ina da fahimi. Na kau da iyakokin ƙasashe, na washe dukiyarsu; a matsayina na mai iko, na mamaye sarakunansu.
כי אמר בכח ידי עשיתי ובחכמתי כי נבנותי ואסיר גבולת עמים ועתידתיהם (ועתודתיהם) שושתי ואוריד כאביר יושבים
14 Kamar yadda mutum yakan miƙa hannu cikin sheƙar tsuntsu haka hannuna ya je ya washe dukiyar al’ummai; kamar yadda mutane sukan tattara ƙwai, haka na tattara dukan ƙasashe; ba tsuntsun da ya kakkaɓe fikafiki, ko yă buɗe baki don yă yi kuka.’”
ותמצא כקן ידי לחיל העמים וכאסף ביצים עזבות כל הארץ אני אספתי ולא היה נדד כנף ופצה פה ומצפצף
15 Gatari ya taɓa fin wanda yake amfani da shi girma, ko zarto yă yi wa wanda yake amfani da shi taƙama? Sanda za tă girgiza mutumin da yake riƙe da ita, ko kuwa kulki yă jijjiga mutumin da yake riƙe da katako!
היתפאר הגרזן על החצב בו אם יתגדל המשור על מניפו כהניף שבט ואת מרימיו כהרים מטה לא עץ
16 Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki, zai aukar da cuta mai kisa a kan ƙosassu jarumawa; a ƙarƙashin sansaninsa zai ƙuna wuta kamar harshen wuta.
לכן ישלח האדון יהוה צבאות במשמניו--רזון ותחת כבדו יקד יקד כיקוד אש
17 Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa.
והיה אור ישראל לאש וקדושו ללהבה ובערה ואכלה שיתו ושמירו--ביום אחד
18 Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi za a hallaka su ɗungum, kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.
וכבוד יערו וכרמלו מנפש ועד בשר יכלה והיה כמסס נסס
19 Sauran itatuwan jejinsa kuma za su ragu ko ɗan ƙaramin yaro ma zai iya ƙidaya su.
ושאר עץ יערו מספר יהיו ונער יכתבם
20 A wannan rana raguwar Isra’ila, waɗanda suka ragu na gidan Yaƙub, ba za su ƙara dogara ga wanda ya kusa hallaka su ba amma za su dogara ga Ubangiji, Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
והיה ביום ההוא לא יוסיף עוד שאר ישראל ופליטת בית יעקב להשען על מכהו ונשען על יהוה קדוש ישראל--באמת
21 Raguwa za tă komo, raguwar Yaƙub za su komo ga Maɗaukaki Allah.
שאר ישוב שאר יעקב--אל אל גבור
22 Ko da yake mutanenka, ya Isra’ila, sun zama kamar yashin bakin teku, raguwa ce kurum za tă komo. A ƙaddara hallaka, mai mamayewa da mai adalci.
כי אם יהיה עמך ישראל כחול הים--שאר ישוב בו כליון חרוץ שוטף צדקה
23 Ubangiji Maɗaukaki, zai sa hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasa ta faru.
כי כלה ונחרצה--אדני יהוה צבאות עשה בקרב כל הארץ
24 Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ya mutanena masu zama a Sihiyona, kada ku ji tsoron Assuriyawa, waɗanda suka dūke ku da sanda suka kuma ɗaga kulki a kanku, kamar yadda Masar ta yi.
לכן כה אמר אדני יהוה צבאות אל תירא עמי ישב ציון מאשור בשבט יככה ומטהו ישא עליך בדרך מצרים
25 Ba da daɗewa ba fushina a kanku zai zo ga ƙarshe hasalata kuma za tă koma ga hallakarsu.”
כי עוד מעט מזער וכלה זעם ואפי על תבליתם
26 Ubangiji Maɗaukaki zai bulale su da tsumagiya, kamar sa’ad da ya bugi Midiyan a dutsen Oreb; zai kuma ɗaga sandarsa a bisa ruwaye, yadda ya yi a Masar.
ועורר עליו יהוה צבאות שוט כמכת מדין בצור עורב ומטהו על הים ונשאו בדרך מצרים
27 A wannan rana zai ɗauke nauyi daga kafaɗarku, nauyinsu daga wuyanku; za a karye karkiya domin kun yi ƙiba ƙwarai.
והיה ביום ההוא יסור סבלו מעל שכמך ועלו מעל צוארך וחבל על מפני שמן
28 Sun shiga Ayiyat; sun bi ta Migron; sun adana tanade-tanade a Mikmash.
בא על עית עבר במגרון למכמש יפקיד כליו
29 Suka ƙetare ta hanya, suka kuma ce, “Za mu kwana a Geba.” Rama ta firgita; Gibeya ta Shawulu ta gudu.
עברו מעברה גבע מלון לנו חרדה הרמה--גבעת שאול נסה
30 Ki yi ihu, ya Diyar Gallim! Ki saurara, ya Layisha! Kayya, Anatot abin tausayi!
צהלי קולך בת גלים הקשיבי לישה עניה ענתות
31 Madmena tana gudu; mutanen Gebim sun ɓuya.
נדדה מדמנה ישבי הגבים העיזו
32 A wannan rana za su dakata a Nob; za su jijjiga ƙarfinsu a dutsen Diyar Sihiyona, a tudun Urushalima.
עוד היום בנב לעמד ינפף ידו הר בית (בת) ציון גבעת ירושלם
33 Duba, Ubangiji Maɗaukaki, zai ragargaza rassa da iko mai girma. Za a sassare itatuwa masu ganyaye, za a yanke dogayen itatuwa har ƙasa.
הנה האדון יהוה צבאות מסעף פארה במערצה ורמי הקומה גדועים והגבהים ישפלו
34 Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.
ונקף סבכי היער בברזל והלבנון באדיר יפול

< Ishaya 10 >