< Ishaya 1 >

1 Wahayi game da Yahuda da Urushalima wanda Ishaya ɗan Amoz ya gani a zamanin da Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya, suka yi mulkin Yahuda.
חזון ישעיהו בן אמוץ אשר חזה על יהודה וירושלם--בימי עזיהו יותם אחז יחזקיהו מלכי יהודה
2 Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya! Gama Ubangiji ya yi magana, “Na yi renon’ya’ya, na kuma raya su, amma sun tayar mini.
שמעו שמים והאזיני ארץ כי יהוה דבר בנים גדלתי ורוממתי והם פשעו בי
3 Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.”
ידע שור קנהו וחמור אבוס בעליו ישראל לא ידע עמי לא התבונן
4 Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta,’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya.
הוי גוי חטא עם כבד עון--זרע מרעים בנים משחיתים עזבו את יהוה נאצו את קדוש ישראל--נזרו אחור
5 Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.
על מה תכו עוד תוסיפו סרה כל ראש לחלי וכל לבב דוי
6 Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.
מכף רגל ועד ראש אין בו מתם פצע וחבורה ומכה טריה לא זרו ולא חבשו ולא רככה בשמן
7 Ƙasarku ta zama kufai, an ƙone biranenku da wuta; baƙi suna ƙwace gonakinku a idanunku, ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta.
ארצכם שממה עריכם שרפות אש אדמתכם לנגדכם זרים אכלים אתה ושממה כמהפכת זרים
8 An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.
ונותרה בת ציון כסכה בכרם כמלונה במקשה כעיר נצורה
9 Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra.
לולי יהוה צבאות הותיר לנו שריד כמעט--כסדם היינו לעמרה דמינו
10 Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!
שמעו דבר יהוה קציני סדם האזינו תורת אלהינו עם עמרה
11 Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.
למה לי רב זבחיכם יאמר יהוה שבעתי עלות אילים וחלב מריאים ודם פרים וכבשים ועתודים לא חפצתי
12 Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?
כי תבאו לראות פני--מי בקש זאת מידכם רמס חצרי
13 Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.
לא תוסיפו הביא מנחת שוא--קטרת תועבה היא לי חדש ושבת קרא מקרא לא אוכל און ועצרה
14 Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.
חדשיכם ומועדיכם שנאה נפשי היו עלי לטרח נלאיתי נשא
15 Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!
ובפרשכם כפיכם אעלים עיני מכם--גם כי תרבו תפלה אינני שמע ידיכם דמים מלאו
16 Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.
רחצו הזכו--הסירו רע מעלליכם מנגד עיני חדלו הרע
17 Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa.
למדו היטב דרשו משפט אשרו חמוץ שפטו יתום ריבו אלמנה
18 Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
לכו נא ונוכחה יאמר יהוה אם יהיו חטאיכם כשנים כשלג ילבינו אם יאדימו כתולע כצמר יהיו
19 In kuna da niyya kuna kuma yi mini biyayya, za ku ci abubuwa masu kyau daga ƙasar;
אם תאבו ושמעתם--טוב הארץ תאכלו
20 amma in kuka yi tsayayya kuka kuma yi tayarwa, za a kashe ku da takobi.” Ni Ubangiji na faɗa.
ואם תמאנו ומריתם--חרב תאכלו כי פי יהוה דבר
21 Dubi yadda amintacciyar birni ta zama karuwa! Dā ta cika da yin gaskiya; dā masu adalci a can suke zama, amma yanzu sai masu kisankai kaɗai!
איכה היתה לזונה קריה נאמנה מלאתי משפט צדק ילין בה--ועתה מרצחים
22 Azurfarki ta zama jebu, an gauraye ruwan inabinki mafi kyau da ruwa.
כספך היה לסיגים סבאך מהול במים
23 Masu mulkinki’yan tawaye ne, abokan ɓarayi; dukansu suna ƙaunar cin hanci suna bin kyautai. Ba sa taɓa tsare marayu a ɗakin shari’a; ba sa taimakon gwauruwa.
שריך סוררים וחברי גנבים--כלו אהב שחד ורדף שלמנים יתום לא ישפטו וריב אלמנה לא יבוא אליהם
24 Saboda haka Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, Mai Iko nan na Isra’ila, ya furta, “Kai, zan sami hutu daga maƙiyana in kuma yi ramuwa a kan abokan gābana.
לכן נאם האדון יהוה צבאות--אביר ישראל הוי אנחם מצרי ואנקמה מאויבי
25 Zan juye hannuna a kanki; zan wanke ke sarai in fitar da dukan ƙazantarki.
ואשיבה ידי עליך ואצרף כבר סיגיך ואסירה כל בדיליך
26 Zan maido da alƙalanki kamar yadda suke a dā can, mashawartanki kamar yadda suke da fari. Bayan haka za a ce da ke Birnin Masu Adalci, Amintacciyar Birni.”
ואשיבה שפטיך כבראשנה ויעציך כבתחלה אחרי כן יקרא לך עיר הצדק--קריה נאמנה
27 Za a fanshi Sihiyona da adalci, masu tubanta kuma da aikin gaskiya.
ציון במשפט תפדה ושביה בצדקה
28 Amma za a karye’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.
ושבר פשעים וחטאים יחדו ועזבי יהוה יכלו
29 “Za ku ji kunya saboda masujadan ƙarƙashin itatuwan oak da kuka yi farin ciki; za a kunyata ku saboda lambun da kuka zaɓa.
כי יבשו מאילים אשר חמדתם ותחפרו--מהגנות אשר בחרתם
30 Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa.
כי תהיו כאלה נבלת עלה וכגנה אשר מים אין לה
31 Mutum mai ƙarfi zai zama kamar rama, aikinsa kuma kamar tartsatsin wuta; duka za su ƙone tare, ba kuwa wanda zai kashe wutar.”
והיה החסן לנערת ופעלו לניצוץ ובערו שניהם יחדו ואין מכבה

< Ishaya 1 >