< Hosiya 9 >

1 Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila; kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai. Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku; kuna son hakkokin karuwa a kowace masussuka.
אל תשמח ישראל אל גיל כעמים כי זנית מעל אלהיך אהבת אתנן על כל גרנות דגן
2 Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba; sabon ruwan inabi zai kāsa musu.
גרן ויקב לא ירעם ותירוש יכחש בה
3 Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba; Efraim zai koma Masar yă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.
לא ישבו בארץ יהוה ושב אפרים מצרים ובאשור טמא יאכלו
4 Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba, ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba. Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki; duk wanda ya ci su zai ƙazantu. Wannan abincin zai zama na kansu ne; ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
לא יסכו ליהוה יין ולא יערבו לו--זבחיהם כלחם אונים להם כל אכליו יטמאו כי לחמם לנפשם לא יבוא בית יהוה
5 Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku, a ranakun bikin Ubangiji?
מה תעשו ליום מועד וליום חג יהוה
6 Ko da sun kuɓuta daga hallaka, Masar za tă tattara su, Memfis kuma za tă binne su. Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu, ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.
כי הנה הלכו משד מצרים תקבצם מף תקברם מחמד לכספם קמוש יירשם חוח באהליהם
7 Kwanakin hukunci suna zuwa, kwanakin ba da lissafi suna a kusa. Bari Isra’ila su san da wannan. Saboda zunubanku sun yi yawa ƙiyayyarku kuma ta yi yawa, har ake ɗauka annabi wawa ne, mutumin da aka iza kuwa mahaukaci.
באו ימי הפקדה באו ימי השלם--ידעו ישראל אויל הנביא משגע איש הרוח--על רב עונך ורבה משטמה
8 Annabi, tare da Allahna, su ne masu tsaro a bisa Efraim, duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi, da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.
צפה אפרים עם אלהי נביא פח יקוש על כל דרכיו--משטמה בבית אלהיו
9 Sun nutse da zurfi cikin lalaci, kamar a kwanakin Gibeya. Allah zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta su saboda zunubansu.
העמיקו שחתו כימי הגבעה יזכור עונם יפקוד חטאותם
10 “Sa’ad da na sami Isra’ila, ya zama kamar samun inabi a hamada; sa’ad da na ga kakanninku, ya zama kamar ganin’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure. Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor, suka keɓe kansu wa gumaka bankunya sai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.
כענבים במדבר מצאתי ישראל--כבכורה בתאנה בראשיתה ראיתי אבותיכם המה באו בעל פעור וינזרו לבשת ויהיו שקוצים כאהבם
11 Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu, ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.
אפרים כעוף יתעופף כבודם מלדה ומבטן ומהריון
12 Ko da sun yi renon’ya’ya, zan sa su yi baƙin cikin kowannensu. Kaitonsu sa’ad da na juya musu baya!
כי אם יגדלו את בניהם ושכלתים מאדם כי גם אוי להם בשורי מהם
13 Na ga Efraim, kamar birnin Taya, da aka kafa a wuri mai daɗi. Amma Efraim zai fitar da’ya’yansu ga masu yanka.”
אפרים כאשר ראיתי לצור שתולה בנוה ואפרים להוציא אל הרג בניו
14 Ka ba su, ya Ubangiji Me za ka ba su? Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin ciki da busassun nono.
תן להם יהוה מה תתן תן להם רחם משכיל ושדים צמקים
15 “Saboda dukan muguntarsu a Gilgal, na ƙi su a can. Saboda ayyukansu na zunubi, zan kore su daga gidana. Ba zan ƙara ƙaunace su ba; dukan shugabanninsu’yan tawaye ne.
כל רעתם בגלגל כי שם שנאתים על רע מעלליהם מביתי אגרשם לא אוסף אהבתם כל שריהם סררים
16 An ka da Efraim, saiwarsu ta bushe, ba sa ba da amfani. Ko da sun haifi’ya’ya zan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
הכה אפרים--שרשם יבש פרי בלי (בל) יעשון גם כי ילדון והמתי מחמדי בטנם
17 Allahna zai ƙi su saboda ba su yi masa biyayya ba; za su zama masu yawo a cikin al’ummai.
ימאסם אלהי כי לא שמעו לו ויהיו נדדים בגוים

< Hosiya 9 >