< Hosiya 8 >

1 “Ka sa kakaki a leɓunanka! Gaggafa tana a bisan gidan Ubangiji domin mutane sun tā da alkawarina suka kuma tayar wa dokata.
אל חכך שפר כנשר על בית יהוה יען עברו בריתי ועל תורתי פשעו׃
2 Isra’ila ta yi mini kuka, ‘Ya Allahnmu, mun yarda da kai!’
לי יזעקו אלהי ידענוך ישראל׃
3 Amma Isra’ila sun ƙi abin da yake mai kyau; abokin gāba zai fafare su.
זנח ישראל טוב אויב ירדפו׃
4 Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.
הם המליכו ולא ממני השירו ולא ידעתי כספם וזהבם עשו להם עצבים למען יכרת׃
5 Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?
זנח עגלך שמרון חרה אפי בם עד מתי לא יוכלו נקין׃
6 Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.
כי מישראל והוא חרש עשהו ולא אלהים הוא כי שבבים יהיה עגל שמרון׃
7 “Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.
כי רוח יזרעו וסופתה יקצרו קמה אין לו צמח בלי יעשה קמח אולי יעשה זרים יבלעהו׃
8 An haɗiye Isra’ila; yanzu tana cikin al’ummai kamar abin da ba shi da amfani.
נבלע ישראל עתה היו בגוים ככלי אין חפץ בו׃
9 Gama sun haura zuwa Assuriya kamar jakin jejin da yake yawo shi kaɗai. Efraim ya sayar da kansa ga maza.
כי המה עלו אשור פרא בודד לו אפרים התנו אהבים׃
10 Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai, yanzu zan tattara su wuri ɗaya. Za su fara lalacewa a ƙarƙashi danniyar babban sarki.
גם כי יתנו בגוים עתה אקבצם ויחלו מעט ממשא מלך שרים׃
11 “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.
כי הרבה אפרים מזבחת לחטא היו לו מזבחות לחטא׃
12 Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata, amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.
אכתוב לו רבו תורתי כמו זר נחשבו׃
13 Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar.
זבחי הבהבי יזבחו בשר ויאכלו יהוה לא רצם עתה יזכר עונם ויפקד חטאותם המה מצרים ישובו׃
14 Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa ya kuma gina fadodi; Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa. Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu da zai cinye kagaransu.”
וישכח ישראל את עשהו ויבן היכלות ויהודה הרבה ערים בצרות ושלחתי אש בעריו ואכלה ארמנתיה׃

< Hosiya 8 >