< Hosiya 5 >

1 “Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.
שמעו זאת הכהנים והקשיבו בית ישראל ובית המלך האזינו כי לכם המשפט כי פח הייתם למצפה ורשת פרושה על תבור׃
2 ’Yan tawaye sun yi zurfi cikin kisan gilla. Zan hore su duka.
ושחטה שטים העמיקו ואני מוסר לכלם׃
3 Na san Efraim ƙaf; Isra’ila ba a ɓoye take a gare ni ba. Efraim, yanzu ka juya ka shiga karuwanci; Isra’ila ta lalace.
אני ידעתי אפרים וישראל לא נכחד ממני כי עתה הזנית אפרים נטמא ישראל׃
4 “Ayyukansu ba su ba su dama su koma ga Allahnsu ba. Halin karuwanci yana cikin zuciyarsu; ba su yarda da Ubangiji ba.
לא יתנו מעלליהם לשוב אל אלהיהם כי רוח זנונים בקרבם ואת יהוה לא ידעו׃
5 Girmankan Isra’ila yana ba da shaida a kansu; Isra’ilawa, har ma Efraim, sun yi tuntuɓe a cikin zunubinsu; Yahuda ma ya yi tuntuɓe tare da su.
וענה גאון ישראל בפניו וישראל ואפרים יכשלו בעונם כשל גם יהודה עמם׃
6 Sa’ad da suka tafi tare da garkunan shanu, tumaki da awakinsu don su nemi Ubangiji, ba za su same shi ba; ya janye kansa daga gare su.
בצאנם ובבקרם ילכו לבקש את יהוה ולא ימצאו חלץ מהם׃
7 Su marasa aminci ne ga Ubangiji; suna haihuwar shegu. Yanzu bukukkuwar Sabon Watansu za su cinye su da gonakinsu.
ביהוה בגדו כי בנים זרים ילדו עתה יאכלם חדש את חלקיהם׃
8 “Amon kakaki a Gibeya, ƙaho a Rama. Ku yi kirarin yaƙi a Bet-Awen; ku ja gaba, ya Benyamin.
תקעו שופר בגבעה חצצרה ברמה הריעו בית און אחריך בנימין׃
9 Efraim za tă zama kango a ranar hukunci. A cikin kabilan Isra’ila na yi shelar abin da yake tabbatacce.
אפרים לשמה תהיה ביום תוכחה בשבטי ישראל הודעתי נאמנה׃
10 Shugabannin Yahuda suna kamar waɗanda suke matsar da duwatsun shaidar da aka sa a kan iyaka ne. Zan zubo musu da fushina a kansu kamar rigyawar ruwa.
היו שרי יהודה כמסיגי גבול עליהם אשפוך כמים עברתי׃
11 An danne Efraim, an murƙushe ta a shari’a ta ƙudura ga bin gumaka.
עשוק אפרים רצוץ משפט כי הואיל הלך אחרי צו׃
12 Na zama kamar asu ga Efraim, kamar ruɓa ga mutanen Yahuda.
ואני כעש לאפרים וכרקב לבית יהודה׃
13 “Sa’ad da Efraim ya ga ciwonsa, Yahuda kuwa miyakunta, sai Efraim ya juya ga Assuriya, ya aika wurin babban sarki don neman taimako. Amma bai iya warkar da kai ba, bai iya warkar da miyakunka ba.
וירא אפרים את חליו ויהודה את מזרו וילך אפרים אל אשור וישלח אל מלך ירב והוא לא יוכל לרפא לכם ולא יגהה מכם מזור׃
14 Gama zan zama kamar zaki ga Efraim, kamar babban zaki ga Yahuda. Zan yage su kucu-kucu in tafi; zan kwashe su, ba wanda zai kuɓutar da su.
כי אנכי כשחל לאפרים וככפיר לבית יהודה אני אני אטרף ואלך אשא ואין מציל׃
15 Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.”
אלך אשובה אל מקומי עד אשר יאשמו ובקשו פני בצר להם ישחרנני׃

< Hosiya 5 >