< Hosiya 4 >

1 Ku ji maganar Ubangiji, ku Isra’ilawa, gama Ubangiji yana da tuhumar da zai kawo a kan ku waɗanda suke zama a ƙasar. “Babu aminci, babu ƙauna, babu yarda da Allah a cikin ƙasar.
שמעו דבר יהוה בני ישראל כי ריב ליהוה עם יושבי הארץ--כי אין אמת ואין חסד ואין דעת אלהים בארץ
2 Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.
אלה וכחש ורצח וגנב ונאף פרצו ודמים בדמים נגעו
3 Saboda wannan ƙasar tana makoki, kuma dukan waɗanda suke zama a cikinta sun lalace; namun jeji da tsuntsayen sararin sama da kuma kifin teku suna mutuwa.
על כן תאבל הארץ ואמלל כל יושב בה בחית השדה ובעוף השמים וגם דגי הים יאספו
4 “Amma kada wani mutum yă kawo tuhuma, kada wani mutum yă zargi wani, gama mutanenka suna kama da waɗanda suke kawo tuhume-tuhume a kan firist ne.
אך איש אל ירב ואל יוכח איש ועמך כמריבי כהן
5 Kuna tuntuɓe dare da rana, annabawa ma suna tuntuɓe tare da ku. Saboda haka zan hallaka mahaifiyarku,
וכשלת היום וכשל גם נביא עמך לילה ודמיתי אמך
6 mutanena suna hallaka saboda jahilci. “Domin kun ƙi neman sani, ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina; domin kun ƙyale dokar Allahnku, ni ma zan ƙyale’ya’yanku.
נדמו עמי מבלי הדעת כי אתה הדעת מאסת ואמאסאך (ואמאסך) מכהן לי ותשכח תורת אלהיך אשכח בניך גם אני
7 Yawan ƙaruwar firistoci, haka suke yawan zunubi a kaina; sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.
כרבם כן חטאו לי כבודם בקלון אמיר
8 Suna ciyar da kansu a kan zunuban mutanena suna kuma haɗamar muguntarsu.
חטאת עמי יאכלו ואל עונם ישאו נפשו
9 Zai kuwa zama, kamar yadda mutane suke, haka firistoci suke. Zan hukunta dukansu saboda al’amuransu in kuma sāka musu saboda ayyukansu.
והיה כעם ככהן ופקדתי עליו דרכיו ומעלליו אשיב לו
10 “Za su ci amma ba za su ƙoshi ba; za su shiga karuwanci amma ba za su ƙaru ba, gama sun rabu da Ubangiji don su ba da kansu
ואכלו ולא ישבעו הזנו ולא יפרצו כי את יהוה עזבו לשמר
11 ga karuwanci, ga tsoho da kuma sabon ruwan inabi, waɗanda suka ɗauke ganewar mutanena.
זנות ויין ותירוש יקח לב
12 Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu.
עמי בעצו ישאל ומקלו יגיד לו כי רוח זנונים התעה ויזנו מתחת אלהיהם
13 Suna miƙa hadaya a kan ƙwanƙolin duwatsu suna kuma ƙone hadayu a kan tuddai, a ƙarƙashin itatuwa oak, aduruku da katambiri, inda inuwa take da daɗi. Saboda haka’ya’yanku mata suka juya wa karuwanci surukanku mata kuma suka shiga yin zina.
על ראשי ההרים יזבחו ועל הגבעות יקטרו תחת אלון ולבנה ואלה כי טוב צלה על כן תזנינה בנותיכם וכלותיכם תנאפנה
14 “Ba zan hukunta’ya’yanku mata sa’ad da suka juya ga yin karuwanci ba, balle surukanku mata, sa’ad da suka yi zina, gama mazan da kansu suna ma’amala da karuwai suna kuma miƙa hadaya tare da karuwai na masujada, mutane marasa ganewa za su lalace!
לא אפקוד על בנותיכם כי תזנינה ועל כלותיכם כי תנאפנה--כי הם עם הזנות יפרדו ועם הקדשות יזבחו ועם לא יבין ילבט
15 “Ko da yake kun yi zina, ya Isra’ila, kada Yahuda ya yi laifi. “Kada ku tafi Gilgal; kada ku haura zuwa Bet-Awen. Kuma kada ku rantse cewa, ‘Muddin Ubangiji yana a raye!’
אם זנה אתה ישראל אל יאשם יהודה ואל תבאו הגלגל ואל תעלו בית און ואל תשבעו חי יהוה
16 Isra’ilawa masu taurinkai ne, kamar karsana mai taurinkai. Yaya Ubangiji zai iya kiwonsu kamar tumaki a makiyaya mai ɗanyar ciyawa?
כי כפרה סררה סרר ישראל עתה ירעם יהוה ככבש במרחב
17 Efraim ya haɗa kai da gumaka; ku ƙyale shi kurum!
חבור עצבים אפרים הנח לו
18 Ko ma sa’ad da abin shansu ya ƙare, sai suka ci gaba da karuwancinsu; masu mulkinsu suna ƙaunar abin kunya.
סר סבאם הזנה הזנו אהבו הבו קלון מגניה
19 Guguwa za tă share su, hadayunsu kuma za su jawo musu abin kunya.
צרר רוח אותה בכנפיה ויבשו מזבחותם

< Hosiya 4 >