< Hosiya 2 >
1 “Ka ce da’yan’uwanka maza, ‘Mutanena,’ ka kuma ce da’yan’uwanka mata, ‘Ƙaunatacciyata.’
2 “Ka tsawata wa mahaifiyarka, ka tsawata mata, gama ita ba matata ba ce, ni kuma ba mijinta ba ne. Ku roƙe ta tă daina karuwancinta da kuma rashin aminci a tsakanin nononta.
3 In ba haka ba zai tuɓe ta tsirara in bar ta kamar yadda take a ranar da aka haife ta; zan sa ta zama kamar hamada, in mayar da ita busasshiyar ƙasar, in kashe ta da ƙishirwa.
4 Ba zan nuna wa’ya’yanta ƙaunata ba, domin su’ya’yan zina ne.
5 Mahaifiyarsu ta yi rashin aminci ta kuma ɗauki cikinsu ta wurin yi abin kunya. Ta ce, ‘Zan bi kwartayena, waɗanda suke ba ni abinci da ruwa, ulu nawa da lilina, mai nawa da kuma abin sha na.’
6 Saboda haka zai tare hanyarta da ƙaya; zan yi mata katanga don kada tă sami hanya.
7 Za tă bi kwartayenta amma ba za tă kama su ba; za tă neme su amma ba za tă same su ba. Sa’an nan za tă ce, ‘Zan koma ga mijina na fari, gama dā ya fi mini yadda nake a yanzu.’
8 Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.
9 “Saboda haka zan ƙwace hatsina sa’ad da ya nuna, da sabon ruwan inabina sa’ad da ya ƙosa. Zan karɓe ulu nawa da lilina, da take niyya ta rufe tsiraicinta.
10 Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta a idanun kwartayenta; ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.
11 Zan tsayar da dukan bukukkuwarta, bukukkuwarta na shekara-shekara, da kuma kiyaye bikin Sababbin Wata nata, kwanakin Asabbacinta, dukan ƙayyadaddun bukukkuwarta.
12 Zan lalatar da inabinta da kuma itatuwan ɓaurenta, waɗanda take cewa su ne abin da kwartayenta suka biya; zan mayar da su kurmi, namun jeji kuwa za su ci su.
13 Zan hukunta ta saboda kwanakin da ta ƙone turare wa Ba’al; ta yi wa kanta ado da zobai da duwatsu masu daraja, ta bi kwartayenta, amma ta manta da ni,” in ji Ubangiji.
14 “Saboda haka yanzu zan rarrashe ta; zan bishe ta zuwa hamada in kuma yi mata magana a hankali.
15 A can zan mayar mata da gonakin inabinta, zan kuma sa Kwarin Akor yă zama ƙofar bege. A can za tă rera kamar a kwanakin ƙuruciyarta, kamar a lokacin da ta fita daga Masar.
16 “A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba.
17 Zan cire sunayen Ba’al daga leɓunanta; ba za a ƙara kira sunayensu ba.
18 A waccan rana zan yi alkawari dominsu da namun jeji da kuma tsuntsayen sararin sama da dukan halittu masu rarrafe a ƙasa. Baka da takobi da yaƙi zan sa su ƙare a ƙasar, domin duk su zauna lafiya.
19 Zan ɗaura aure da ke har abada; zan ɗaura aure da yake cikin adalci da gaskiya, cikin ƙauna da jinƙai.
20 Zan ɗaura aure da yake cikin aminci za ki kuwa yarda cewa ni ne Ubangiji.
21 “A waccan rana zan amsa,” in ji Ubangiji, “zan amsa wa sararin sama, za su kuwa amsa wa ƙasa;
22 ƙasa kuma za tă amsa wa hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai, su kuma za su amsa wa Yezireyel.
23 Zan dasa ta wa kaina a ƙasar; zan shuka ƙaunata ga wanda na ce ‘Ba ƙaunatacciyata ba.’ Zan faɗa wa waɗanda a ce ‘Ba mutanena ba,’ ‘Ku mutanena ne’; za su kuwa ce, ‘Kai ne Allahna.’”