< Hosiya 14 >
1 Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku. Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!
2 Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu.
3 Assuriya ba za su iya cece mu ba; ba za mu hau dawakan yaƙi ba. Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’ wa abin da hannuwanmu suka yi ba, gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”
4 “Zan gyara ɓatancinsu in kuma ƙaunace su a sake, gama fushina ya juya daga gare su.
5 Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila zai yi fure kamar lili. Kamar al’ul na Lebanon zai sa saiwarsa zuwa ƙasa;
6 tohonsa za su yi girma. Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun, ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.
7 Mutane za su sāke zauna a inuwarsa. Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi. Zai yi fure kamar kuringa, zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.
8 Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka? Zan amsa masa in kuma lura da shi. Ni kamar koren itacen fir ne; amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”
9 Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa. Hanyoyin Ubangiji daidai ne; masu adalci sukan yi tafiya a kansu, amma’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.