< Hosiya 13 >
1 Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki; an girmama shi a cikin Isra’ila. Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.
Cuando hablaba Efraím temblaban (los otros), así se ensalzó en Israel, pero se hizo culpable por Baal, y murió.
2 Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”
Y ahora pecan más todavía; de su plata se han hecho imágenes fundidas, ídolos según su propio concepto, todos ellos obra de artífice; y a tales las dicen: “Sacrificadores de hombres besan a becerros.”
3 Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.
Por eso serán como la nube de la mañana, y como el rocío matutino que desaparece, como el tamo que el viento se lleva de la era, y como el humo que sale por la ventana.
4 “Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni.
Pero Yo soy Yahvé, tu Dios, desde la tierra de Egipto, y tú no has de reconocer a otro Dios fuera de Mí; no hay otro salvador sino Yo.
5 Na lura da ku a hamada, cikin ƙasar mai ƙunar zafi.
Yo te conocí en el desierto, en la tierra de sequedad.
6 Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi; sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama; sai suka manta da ni.
Se saciaron de sus pastos, se hartaron, y se engrió su corazón, por eso me echaron en olvido.
7 Saboda haka zan hau kansu kamar zaki, zan ɓuya a bakin hanya kamar damisa.
Mas Yo seré para ellos como león, cual leopardo acecharé en el camino.
8 Kamar beyar da aka ƙwace mata’ya’yanta, zan fāɗa musu in ɓarke su. Kamar zaki zan cinye su; kamar naman jeji zan yayyage su.
Me precipitaré sobre ellos como una osa privada de sus cachorros; destrozaré hasta la envoltura de su corazón, y los devoraré allí cual león; las fieras del campo los despedazarán.
9 “An hallaka ku, ya Isra’ila, domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku.
Tu ruina, oh Israel, viene de ti, y solo de Mí tu socorro.
10 Ina sarkinku, da zai cece ku? Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku, waɗanda kuka ce, ‘Ba mu sarki da shugabanni’?
¿Dónde está tu rey que te salve en todas tus ciudades? ¿Y tus jueces, puesto que dijiste: “Dame rey y príncipes”?
11 Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki, kuma cikin hasalata na ɗauke shi.
Yo te doy rey en mi ira, y te lo quito en mi indignación.
12 An yi ajiyar laifin Efraim, aka lissafta zunubansa.
Atada está la iniquidad de Efraím, y bien guardado su pecado.
13 Naƙuda ta zo masa kamar a mace mai haihuwa, amma shi yaro ne marar hikima; sa’ad da lokaci ya kai, ba ya zuwa inda mahaifa ta buɗe.
Dolores de parturienta vendrán sobre él; es un hijo necio, pues no sale a luz al abrirse la matriz.
14 “Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba, (Sheol )
Yo los rescataré del poder del scheol, los redimiré de la muerte. ¿Dónde están tus plagas, oh muerte? ¿dónde tu destrucción, oh scheol? Mis ojos no ven arrepentimiento alguno. (Sheol )
15 ko da ma ya ci gaba cikin’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima.
Aunque (Efraím) crezca entre sus hermanos, vendrá un viento solano, un soplo de Yahvé; del desierto saldrá, y se secará su fuente, se agotará su manantial; y será saqueado su tesoro, todo cuanto tiene de precioso.
16 Dole mutanen Samariya su ɗauki laifinsu, domin sun tayar wa Allahnsu. Za a kashe su da takobi; za a fyaɗa ƙananansu da ƙasa, za a ɓarke matansu masu ciki.”
Samaria será castigada, porque se ha rebelado contra su Dios; caerán a espada; serán estrellados sus niños, y será abierto el vientre de sus mujeres encintas.