< Hosiya 12 >

1 Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.
Ephraim herds the wind and hunts the sirocco. All day long they heap up falsehood and fraud, make a treaty with Assyria, and sends tribute of olive oil to Egypt.
2 Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda; zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa zai sāka masa bisa ga ayyukansa.
The Lord has a charge to bring against Israel, to punish Jacob for his acts, according to his deeds will he requite him,
3 A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa; a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.
In the womb he supplanted his brother, in manhood he wrestled with God,
4 Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can,
He wrestled with the angel and prevailed, he wept and sought his blessing. At Bethel the Lord found him, and there he spoke with us.
5 Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne!
And the Lord is the God of hosts, the Lord is his name!
6 Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.
So now, by the help of your God, return. Keep true love and justice. Trust in your God without ceasing.
7 Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta.
A merchant uses false scales: They love to defraud.
8 Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”
Ephraim says, “Yes, I have become rich, I have secured wealth for myself. But despite my gains no one will find a crime I can be convicted of!”
9 “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.
I am the Lord your God, ever since the land of Egypt. I will make you again dwell in tents, as in days of old.
10 Na yi magana da annabawa, na ba su wahayi da yawa na kuma ba da misalai ta wurinsu.”
I spoke continually by the prophets. It was I who multiplied visions, and spoke in parables through the prophets.
11 Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.
In Gilead is iniquity, they will come to nothing. In Gilgal they sacrifice bulls, so their altars will be as stone heaps, among the furrows of the field.
12 Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.
And Jacob fled to the territory of Aram, and Israel worked to earn a wife: for a wife he herded sheep.
13 Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.
The Lord brought Israel up from Egypt by a prophet, and by a prophet Israel was guarded.
14 Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.
Ephraim has given bitter provocation. His Lord will leave upon him his guilt of bloodshed, and for his contempt he will repay him.

< Hosiya 12 >