< Hosiya 11 >

1 “Sa’ad da Isra’ila yake yaro, na ƙaunace shi, daga Masar kuma na kira ɗana.
When Israel was a child, I loved him, And called my son out of Egypt,
2 Amma yawan kiran da na yi wa Isra’ila haka nesa da ni da suke ta yi. Suka miƙa hadaya ga Ba’al suka kuma ƙona turare ga siffofi.
But they turned away from those that called them. They sacrificed to images of Baal; They burned incense to idols.
3 Ni ne na koya wa Efraim tafiya ina kama su da hannu; amma ba su gane cewa ni ne na warkar da su ba.
I helped Ephraim to go, Yea, I took them up in my arms; Yet they marked not that I healed them.
4 Na bishe su da linzamin alheri da tausayi, da ragamar ƙauna; Na cire karkiya daga wuyansu na kuma rusuna na ciyar da su.
I drew them with human cords, with bands of love; I was to them as those who lift up the yoke from their jaws; I dealt gently with them, and gave them food.
5 “Ba za su koma Masar ba Assuriya kuma ba za tă yi mulki a bisansu ba saboda sun ƙi su tuba ba?
They shall no more go down to Egypt; For the Assyrian shall be their king, Because they refuse to return to me.
6 Takuba za su yi ta wulgawa a biranensu, za su hallaka sandunan ƙarafan ƙofofinsu su kuma kawo ƙarshen ƙulle-ƙullensu.
The sword shall fall upon their cities, It shall consume their bars, and devour Because of their devices.
7 Mutanena sun ƙudura su juye daga gare ni. Ko da ma suka yi kira ga Mafi Ɗaukaka, ta ko ƙaƙa ba zai girmama su ba.
For my people persevere in turning away from me; Though they are called to the Most High, None will exalt him.
8 “Yaya zan ba da kai, Efraim? Yaya zan miƙa ka, Isra’ila? Yaya zan yi da kai kamar Adma? Yaya zan yi da kai kamar Zeboyim? Zuciyata ta canja a cikina; dukan tausayina ya huru.
How shall I give thee up, Ephraim? How shall I abandon thee, Israel? How shall I make thee as Admah? How shall I set thee as Zeboim? My heart is changed within me; Yea, my compassion is kindled.
9 Ba zan zartar da fushina mai zafi ba, ba kuwa zan juya in ragargaza Efraim ba. Gama ni Allah ne, ba mutum ba, Mai Tsarki a cikinku. Ba zan zo cikin fushi ba.
I will not execute the fierceness of mine anger; I will not again destroy Ephraim; For I am God, and not man, The Holy One in the midst of thee, And I will not come in anger.
10 Za su bi Ubangiji; zai yi ruri kamar zaki. Sa’ad da ya yi ruri,’ya’yansa za su zo da rawan jiki daga yamma.
They shall walk after Jehovah, when he shall roar like a lion, When he shall roar, then shall their sons hasten from the west;
11 Za su zo da rawan jiki kamar tsuntsaye daga Masar, kamar kurciyoyi daga Assuriya. Zan zaunar da su a cikin gidajensu,” in ji Ubangiji.
They shall hasten as a bird from Egypt, And as a dove from the land of Assyria, And I will place them in their houses, saith Jehovah.
12 Mutanen Efraim sun kewaye ni da ƙarairayi, gidan Isra’ila da ruɗu. Mutanen Yahuda kuma suna yi wa Allah ƙin ji, har ma a kan Mai Tsarkin nan mai aminci.
Ephraim compasseth me about with falsehood, And the house of Israel with deceit; Judah also is inconstant toward God, Toward the holy and faithful one.

< Hosiya 11 >