< Hosiya 10 >

1 Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da’ya’ya wa kansa. Yayinda’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.
גפן בוקק ישראל פרי ישוה לו כרב לפריו הרבה למזבחות--כטוב לארצו היטיבו מצבות
2 Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.
חלק לבם עתה יאשמו הוא יערף מזבחותם ישדד מצבותם
3 Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?”
כי עתה יאמרו אין מלך לנו כי לא יראנו את יהוה והמלך מה יעשה לנו
4 Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.
דברו דברים אלות שוא כרת ברית ופרח כראש משפט על תלמי שדי
5 Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.
לעגלות בית און יגורו שכן שמרון כי אבל עליו עמו וכמריו עליו יגילו--על כבודו כי גלה ממנו
6 Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.
גם אותו לאשור יובל מנחה למלך ירב בשנה אפרים יקח ויבוש ישראל מעצתו
7 Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye.
נדמה שמרון מלכה כקצף על פני מים
8 Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”
ונשמדו במות און חטאת ישראל--קוץ ודרדר יעלה על מזבחותם ואמרו להרים כסונו ולגבעות נפלו עלינו
9 “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila, a can kuwa kuka ci gaba. Yaƙi bai cimma masu aikata mugunta a Gibeya ba?
מימי הגבעה חטאת ישראל שם עמדו לא תשיגם בגבעה מלחמה על בני עלוה
10 Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su; al’ummai za su taru su yi gāba da su don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.
באותי ואסרם ואספו עליהם עמים באסרם לשתי עינתם (עונותם)
11 Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.
ואפרים עגלה מלמדה אהבתי לדוש ואני עברתי על טוב צוארה ארכיב אפרים יחרוש יהודה ישדד לו יעקב
12 Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.
זרעו לכם לצדקה קצרו לפי חסד נירו לכם ניר ועת לדרוש את יהוה עד יבוא וירה צדק לכם
13 Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa,
חרשתם רשע עולתה קצרתם אכלתם פרי כחש--כי בטחת בדרכך ברב גבוריך
14 hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku, saboda a ragargaza kagaranku, kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi, sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da’ya’yansu da ƙasa.
וקאם שאון בעמך וכל מבצריך יושד כשד שלמן בית ארבאל ביום מלחמה אם על בנים רטשה
15 Haka zai faru da kai, ya Betel, domin muguntarka ta yi yawa. Sa’ad da wannan rana ta zo, za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.
ככה עשה לכם בית אל מפני רעת רעתכם בשחר נדמה נדמה מלך ישראל

< Hosiya 10 >