< Ibraniyawa 1 >
1 A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,
2 amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. (aiōn )
3 Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.
4 Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.
5 Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”?
6 Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”
7 Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce, “Ya mai da mala’ikunsa iska, bayinsa kuma harsunan wuta.”
8 Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka. (aiōn )
9 Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”
10 Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
11 Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga.
12 Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
13 Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka”?
14 Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?