< Ibraniyawa 9 >
1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.
Mělať pak i první ona smlouva ustanovení z strany služeb a svatyni světskou.
2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.
Nebo udělán byl stánek první, v kterémž byl svícen, a stůl, a posvátní chlebové, a ten sloul svatyně.
3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,
Za druhou pak oponou byl stánek, kterýž sloul svatyně svatých,
4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.
Zlatou maje kadidlnici, a truhlu smlouvy, všudy obloženou zlatem, kdežto bylo věderce zlaté, mající v sobě mannu, a hůl Aronova, kteráž byla zkvetla, a dsky zákona,
5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.
Nad truhlou pak byli dva cherubínové slávy, zastěňujíci slitovnici. O kterýchž věcech není potřebí nyní vypravovati o jedné každé obzvláštně.
6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.
To vše když tak jest zřízeno, do prvního stánku vždycky vcházejí kněží, služby vykonávajíce,
7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.
Do druhého pak jedinou v rok sám nejvyšší kněz, ne bez krve, kterouž obětuje sám za sebe, i za lidské nevědomosti.
8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.
Èímž Duch svatý ukazuje to, že ještě nebyla zjevena cesta k svatyni, dokudž první stánek trval.
9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.
Kterýž byl podobenstvím na ten přítomný čas, v němžto darové a oběti se obětují, kteréž nemohou dokonalého v svědomí učiniti toho, kdož obětuje,
10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.
Toliko v pokrmích a v nápojích, a v rozličných umýváních a ospravedlňováních tělesných, až do času napravení, záležející.
11 Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.
Ale Kristus přišed, nejvyšší kněz budoucího dobrého, skrze větší a dokonalejší stánek, ne rukou udělaný, to jest ne tohoto stavení,
12 Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. (aiōnios )
Ani skrze krev kozlů a telat, ale skrze svou vlastní krev, všel jednou do svatyně, věčné vykoupení nalezl. (aiōnios )
13 In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
Nebo jestližeť krev býků a kozlů, a popel jalovice, pokropující poskvrněných, posvěcuje jich k očištění těla,
14 balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! (aiōnios )
Èím více krev Kristova, kterýžto skrze Ducha věčného samého sebe obětoval nepoškvrněného Bohu, očistí svědomí vaše od skutků mrtvých k sloužení Bohu živému? (aiōnios )
15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. (aiōnios )
A pro tu příčinu nové smlouvy prostředník jest, aby, když by smrt mezi to vkročila k vyplacení přestoupení těch, kteráž byla za první smlouvy, zaslíbení věčného dědictví přijali ti, jenž jsou povoláni. (aiōnios )
16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,
Nebo kdež se děje kšaft, potřebí jest, aby k tomu smrt přikročila toho, kdož činí kšaft.
17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.
Kšaft zajisté těch, kteříž zemřeli, pevný jest, poněvadž ještě nemá moci, dokudž živ jest ten, jenž kšaft činil.
18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.
Protož ani první onen kšaft bez krve nebyl posvěcován.
19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.
Nebo když Mojžíš všecka přikázaní podle Zákona všemu lidu předložil, vzav krev telat a kozlů, s vodou a s vlnou červenou a s yzopem, tak spolu i knihy i všeho lidu pokropil,
20 Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”
Řka: Tatoť jest krev Zákona, kterýž vám Bůh vydal.
21 Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.
Ano i stánku i všech nádob k službě náležitých rovně též krví pokropil.
22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
A téměř všecko podle Zákona krví očišťováno bývá, a bez krve vylití nebývá odpuštění vin.
23 Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.
Protož potřebí bylo, aby věcí nebeských příkladové těmi věcmi očišťováni byli, nebeské pak věci lepšími obětmi, nežli jsou ty.
24 Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
Neboť nevšel Kristus do svatyně rukou udělané, kteráž by byla příklad s pravou svatyní se srovnávající, ale právě v nebe všel, aby nyní přítomný byl tváři Boží za nás.
25 Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.
Ne aby častokrát obětoval sebe samého, jako nejvyšší kněz vcházel do svatyně každý rok se krví cizí,
26 Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. (aiōn )
(Sic jinak byl by musil častokrát trpěti od počátku světa, ) ale nyní jednou při skonání věků, na shlazení hřícha skrze obětování sebe samého, zjeven jest. (aiōn )
27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,
A jakož uloženo lidem jednou umříti, a potom bude soud,
28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
Tak i Kristus jednou jest obětován, k shlazení mnohých lidi hříchů; podruhé pak bez hříchu ukáže se těm, kteříž ho čekají k spasení.