< Ibraniyawa 9 >

1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya.
ܒܩܕܡܝܬܐ ܕܝܢ ܐܝܬ ܗܘܐ ܒܗ ܦܘܩܕܐ ܕܬܫܡܫܬܐ ܘܒܝܬ ܩܘܕܫܐ ܥܠܡܢܝܐ
2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki.
ܡܫܟܢܐ ܓܝܪ ܩܕܡܝܐ ܕܐܬܥܒܕ ܐܝܬ ܗܘܐ ܒܗ ܡܢܪܬܐ ܘܦܬܘܪܐ ܘܠܚ ܐܦܐ ܘܡܬܩܪܐ ܗܘܐ ܒܝܬ ܩܘܕܫܐ
3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki,
ܡܫܟܢܐ ܕܝܢ ܓܘܝܐ ܕܠܓܘ ܡܢ ܐܦܝ ܬܪܥܐ ܕܬܪܝܢ ܡܬܩܪܐ ܗܘܐ ܩܕܘܫ ܩܘܕܫܐ
4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari.
ܘܐܝܬ ܗܘܐ ܒܗ ܒܝܬ ܒܤܡܐ ܕܕܗܒܐ ܘܩܒܘܬܐ ܕܕܝܬܩܐ ܕܩܪܝܡܐ ܟܠܗ ܒܕܗܒܐ ܘܐܝܬ ܒܗ ܩܤܛܐ ܕܕܗܒܐ ܗܝ ܕܐܝܬ ܗܘܐ ܒܗ ܡܢܢܐ ܘܫܒܛܐ ܕܐܗܪܘܢ ܗܘ ܕܐܦܪܥ ܘܠܘܚܐ ܕܕܝܬܩܐ
5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu. Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.
ܘܠܥܠ ܡܢܗ ܟܪܘܒܐ ܕܫܘܒܚܐ ܕܡܛܠܝܢ ܥܠ ܚܘܤܝܐ ܠܐ ܗܘܐ ܕܝܢ ܙܒܢܐ ܗܘ ܕܢܐܡܪ ܥܠ ܚܕܐ ܚܕܐ ܡܢ ܗܠܝܢ ܕܗܟܢܐ ܡܬܩܢܢ ܗܘܝ
6 Sa’ad da aka shirya kome haka, sai firistoci suka shiga kullum cikin ɗaki na waje don su yi hidimarsu.
ܘܠܡܫܟܢܐ ܒܪܝܐ ܒܟܠܙܒܢ ܥܐܠܝܢ ܗܘܘ ܟܘܡܪܐ ܘܡܫܠܡܝܢ ܗܘܘ ܬܫܡܫܬܗܘܢ
7 Amma babban firist ne kaɗai yakan shiga ɗaki na ciki-ciki, sau ɗaya tak a shekara, kuma sai da jini, wanda yakan miƙa domin zunubansa da kuma domin zunuban da mutane suka yi a cikin rashin sani.
ܠܡܫܟܢܐ ܕܝܢ ܕܠܓܘ ܡܢܗ ܚܕܐ ܗܘ ܒܫܢܬܐ ܒܠܚܘܕܘܗܝ ܥܐܠ ܗܘܐ ܪܒܟܘܡܪܐ ܒܕܡܐ ܗܘ ܕܡܩܪܒ ܗܘܐ ܚܠܦ ܢܦܫܗ ܘܚܠܦ ܤܟܠܘܬܗ ܕܥܡܐ
8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki ya nuna cewa ba a riga an bayyana hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin tabanakul na fari yana nan tsaye.
ܒܗܕܐ ܕܝܢ ܡܘܕܥܐ ܗܘܬ ܪܘܚܐ ܕܩܘܕܫܐ ܕܠܐ ܐܬܓܠܝܬ ܥܕܟܝܠ ܐܘܪܚܐ ܕܩܕܝܫܐ ܟܡܐ ܙܒܢܐ ܕܐܝܬ ܗܘܐ ܩܝܡܐ ܠܡܫܟܢܐ ܩܕܡܝܐ
9 Wannan ma yana da ma’ana wa mutane a yau. Ya nuna cewa ba za mu iya wanke lamirinmu ta wurin miƙa baye-baye da hadayu ba.
ܘܐܝܬܘܗܝ ܗܘܐ ܡܬܠܐ ܗܢܐ ܠܙܒܢܐ ܗܘ ܕܒܗ ܩܘܪܒܢܐ ܘܕܒܚܐ ܡܬܩܪܒܝܢ ܗܘܘ ܐܝܠܝܢ ܕܠܐ ܡܫܟܚܝܢ ܗܘܘ ܠܡܓܡܪ ܬܐܪܬܗ ܕܡܢ ܕܡܩܪܒ ܠܗܘܢ
10 Waɗannan ƙa’idodi sun shafi sha’anin abinci da abin sha ne kawai da kuma ƙa’idodi tsarkake kanmu. Dokoki game da abubuwa na waje da ake amfani da su za su kasance ne sai lokacin ya yi da za a kawo abu mafi kyau.
ܐܠܐ ܒܡܐܟܠܐ ܘܒܡܫܬܝܐ ܒܠܚܘܕ ܘܒܡܥܡܘܕܝܬܐ ܕܙܢܝܢ ܙܢܝܢ ܕܐܝܬܝܗܝܢ ܦܘܩܕܐ ܕܒܤܪܐ ܕܤܝܡܝܢ ܥܕܡܐ ܠܙܒܢܐ ܕܬܘܪܨܐ
11 Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba.
ܡܫܝܚܐ ܕܝܢ ܕܐܬܐ ܗܘܐ ܪܒܟܘܡܪܐ ܕܛܒܬܐ ܕܤܥܪ ܘܥܠ ܠܡܫܟܢܐ ܪܒܐ ܘܡܫܠܡܢܐ ܕܠܐ ܥܒܝܕ ܒܐܝܕܝܐ ܘܠܐ ܗܘܐ ܡܢ ܗܠܝܢ ܒܪܝܬܐ
12 Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa. (aiōnios g166)
ܘܠܐ ܥܠ ܒܕܡܐ ܕܨܦܪܝܐ ܘܕܥܓܠܐ ܐܠܐ ܒܕܡܐ ܕܢܦܫܗ ܥܠ ܚܕܐ ܙܒܢ ܠܒܝܬ ܡܩܕܫܐ ܘܐܫܟܚ ܦܘܪܩܢܐ ܕܠܥܠ (aiōnios g166)
13 In har akan yayyafa jinin awaki da na bijimai da kuma tokar karsanar a kan waɗanda suke marasa tsabta bisa ga al’ada, a tsarkake su yadda za su zama masu tsabta a waje,
ܐܢ ܓܝܪ ܕܡܐ ܕܨܦܪܝܐ ܘܕܥܓܠܐ ܘܩܛܡܐ ܕܥܓܠܬܐ ܡܬܪܤܤ ܗܘܐ ܥܠ ܐܝܠܝܢ ܕܡܬܛܡܐܝܢ ܗܘܘ ܘܡܩܕܫ ܠܗܘܢ ܠܕܘܟܝܐ ܕܒܤܪܗܘܢ
14 balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai! (aiōnios g166)
ܟܡܐ ܗܟܝܠ ܝܬܝܪܐܝܬ ܕܡܗ ܕܡܫܝܚܐ ܕܒܪܘܚܐ ܕܠܥܠ ܢܦܫܗ ܩܪܒ ܕܠܐ ܡܘ ܠܐܠܗܐ ܢܕܟܐ ܬܐܪܬܢ ܡܢ ܥܒܕܐ ܡܝܬܐ ܕܢܫܡܫ ܠܐܠܗܐ ܚܝܐ (aiōnios g166)
15 Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. (aiōnios g166)
ܡܛܠ ܗܢܐ ܗܘ ܗܘܐ ܡܨܥܝܐ ܕܕܝܬܩܐ ܚܕܬܐ ܕܒܡܘܬܗ ܗܘ ܗܘܐ ܦܘܪܩܢܐ ܠܐܝܠܝܢ ܕܥܒܪܘ ܥܠ ܕܝܬܩܐ ܩܕܡܝܬܐ ܕܢܤܒܘܢ ܡܘܠܟܢܐ ܐܝܠܝܢ ܕܐܬܩܪܝܘ ܠܝܪܬܘܬܐ ܕܠܥܠ (aiōnios g166)
16 Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta,
ܐܝܟܐ ܓܝܪ ܕܐܝܬ ܕܝܬܩܐ ܡܘܬܐ ܗܘ ܡܚܘܝܐ ܕܗܘ ܕܥܒܕܗ
17 domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai.
ܥܠ ܡܝܬܐ ܕܝܢ ܒܠܚܘܕ ܡܫܬܪܪܐ ܡܛܠ ܕܟܡܐ ܕܚܝ ܗܘ ܕܥܒܕܗ ܠܝܬ ܒܗ ܚܫܚܘ
18 Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.
ܡܛܠ ܗܢܐ ܐܦܠܐ ܩܕܡܝܬܐ ܕܠܐ ܕܡܐ ܐܫܬܪܪܬ
19 Sa’ad da Musa ya sanar wa dukan mutane kowane umarni na doka, sai ya ɗauki jinin maruƙa tare da ruwa, jan ulu da kuma rassan hizzob, ya yayyafa a kan naɗaɗɗen littafin da kuma a kan dukan mutanen.
ܟܕ ܐܬܦܩܕ ܓܝܪ ܟܠܗ ܦܘܩܕܢܐ ܡܢ ܡܘܫܐ ܠܥܡܐ ܟܠܗ ܒܢܡܘܤܐ ܢܤܒ ܗܘܐ ܡܘܫܐ ܕܡܐ ܕܥܓܠܬܐ ܘܡܝܐ ܒܥܡܪܐ ܕܙܚܘܪܝܬܐ ܘܙܘܦܐ ܘܪܤ ܥܠ ܤܦܪܐ ܘܥܠ ܥܡܐ ܟܠܗ
20 Ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Allah ya umarce ku ku kiyaye.”
ܘܐܡܪ ܠܗܘܢ ܗܢܐ ܗܘ ܕܡܐ ܕܕܝܬܩܐ ܗܝ ܕܐܬܦܩܕܬ ܠܟܘܢ ܡܢ ܐܠܗܐ
21 Ta haka ya yayyafa jinin a kan tabanakul da kuma a kan dukan kayayyakin da ake amfani da su don yin hidima.
ܐܦ ܥܠ ܡܫܟܢܐ ܘܥܠ ܟܠܗܘܢ ܡܐܢܐ ܕܬܫܡܫܬܐ ܡܢܗ ܡܢ ܕܡܐ ܪܤ
22 Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
ܡܛܠ ܕܟܠܡܕ ܒܕܡܐ ܗܘ ܡܬܕܟܐ ܒܢܡܘܤܐ ܘܕܠܐ ܫܘܦܥ ܕܡܐ ܠܝܬ ܫܘܒܩܢܐ
23 Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau.
ܐܢܢܩܐ ܗܝ ܓܝܪ ܕܗܠܝܢ ܕܕܡܘܬܐ ܐܢܝܢ ܕܫܡܝܢܝܬܐ ܒܗܠܝܢ ܡܬܕܟܝܢ ܗܠܝܢ ܕܝܢ ܫܡܝܢܝܬܐ ܒܕܒܚܐ ܕܡܝܬܪܝܢ ܡܢ ܗܠܝܢ
24 Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
ܠܐ ܗܘܐ ܓܝܪ ܠܒܝܬ ܡܩܕܫܐ ܕܥܒܝܕ ܒܐܝܕܝܐ ܥܠ ܡܫܝܚܐ ܕܐܝܬܘܗܝ ܕܡܘܬܐ ܕܗܘ ܫܪܝܪܐ ܐܠܐ ܠܗ ܠܫܡܝܐ ܥܠ ܕܢܬܚܙܐ ܩܕ ܦܪܨܘܦܗ ܕܐܠܗܐ ܚܠܦܝܢ
25 Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba.
ܐܦܠܐ ܕܢܩܪܒ ܢܦܫܗ ܙܒܢܬܐ ܤܓܝܐܬܐ ܐܝܟ ܕܥܒܕ ܗܘܐ ܪܒ ܟܘܡܪܐ ܘܥܐܠ ܒܟܠ ܫܢܐ ܠܒܝܬ ܡܩܕܫܐ ܒܕܡܐ ܕܠܐ ܕܝܠܗ
26 Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. (aiōn g165)
ܘܐܢ ܠܐ ܚܝܒ ܗܘܐ ܕܙܒܢܬܐ ܤܓܝܐܬܐ ܢܚܫ ܡܢ ܫܘܪܝܗ ܕܥܠܡܐ ܗܫܐ ܕܝܢ ܒܚܪܬܗ ܕܥܠܡܐ ܚܕܐ ܗܘ ܙܒܢ ܩܪܒ ܢܦܫܗ ܒܕܒܝܚܘܬܗ ܕܢܒܛܠܝܗ ܠܚܛܝܬܐ (aiōn g165)
27 Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,
ܘܐܝܟܢܐ ܕܤܝ ܠܒܢܝܢܫܐ ܕܚܕܐ ܙܒܢ ܢܡܘܬܘܢ ܘܡܢ ܒܬܪ ܡܘܬܗܘܢ ܕܝܢܐ
28 haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
ܗܟܢܐ ܐܦ ܡܫܝܚܐ ܚܕܐ ܙܒܢ ܐܬܩܪܒ ܘܒܩܢܘܡܗ ܕܒܚ ܚܛܗܐ ܕܤܓܝܐܐ ܕܬܪܬܝܢ ܕܝܢ ܙܒܢܝܢ ܕܠܐ ܚܛܗܝܢ ܡܬܚܙܐ ܠܚܝܝܗܘܢ ܕܐܝܠܝܢ ܕܡܤܟܝܢ ܠܗ

< Ibraniyawa 9 >