< Ibraniyawa 8 >

1 Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama,
Now a summation about the things being spoken is, we have such a high priest who was seated at the right hand of the throne of the Majesty in the heavens,
2 wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.
a minister of the holy things, and of the true tabernacle, which the Lord erected and not man.
3 Da yake dole kowane babban firist da aka naɗa yă miƙa baye-baye da hadayu, haka ma wannan ya bukaci yă kasance da abin da zai miƙa.
For every high priest is appointed in order to offer both gifts and sacrifices, whereupon it is necessary for this man also to have something that he may offer.
4 Da a ce yana a duniya ne, da bai zama firist ba, domin a nan akwai mutanen da doka ta naɗa don su miƙa baye-baye.
For certainly if he were on earth, he would not even be a priest, there being the priests who offer the gifts according to the law,
5 Suna hidima a cikin tsattsarkan wuri wanda yake hoto da kuma siffar abin da yake cikin sama. Shi ya sa aka gargaɗi Musa sa’ad da yana dab da gina tabanakul cewa, “Ka lura fa, ka yi kome daidai bisa ga zānen da aka nuna maka a kan dutsen.”
who serve for an example and shadow of the heavenly things. Just as Moses who was divinely warned while going to complete the tabernacle, for he says, See thou make all things according to the pattern that was shown thee on the mountain.
6 Amma hidimar da Yesu ya karɓa tana da fifiko a kan tasu, kamar yadda alkawarin da shi ne yake matsakanci ya fi na dā fifiko nesa, an kuma kafa shi a kan alkawura mafi kyau.
But now he has obtained a superior ministry, by so much as he is also the mediator of a superior covenant, which has been enacted upon superior promises.
7 Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba.
For if that first one was faultless, no place would have been sought for a second.
8 Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
For, finding fault with them, he says, Behold, the days come, says the Lord, and I will perfect a new covenant with the house of Israel and with the house of Judah.
9 Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.
Not according to the covenant that I made with their fathers in the day when I took them by my hand to lead them out of the land of Egypt. Because they did not continue in my covenant, and I disregarded them, says the Lord.
10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.
Because this is the covenant that I will ordain with the house of Israel after those days, says the Lord, giving my laws into their mind, and I will write them on their hearts. And I will be to them for a God, and they will be to me for a people.
11 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.
And they will, no, not teach each man his fellow citizen, and each man his brother, saying, Know the Lord, because all will know me, from their small as far as their great.
12 Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”
Because I will be merciful to their iniquities, and their sins and their lawlessness I will no, not further remember.
13 Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.
In saying, New, he has made the first old. And what is becoming old and obsolete is near disappearance.

< Ibraniyawa 8 >