< Ibraniyawa 6 >
1 Dole mu yi ƙoƙarin zama balagaggu mu kuma fara tunani game da abubuwan da suka fi koyarwan nan mai sauƙi game da Kiristi. Bai kamata mu ci gaba da magana game da me ya sa dole mu juye daga ayyukan da suke kawo mutuwa da kuma me ya sa za mu kasance da bangaskiya a cikin Allah ba.
因此,讓我們擱下論基督的初級教理,而努力向成全的課程邁進;不必再樹立基礎,就是講論悔改,死亡的行為,信賴天主
2 Kuma bai kamata mu ci gaba da koyar da umarnai game da baftisma, ɗibiya hannuwa, tashin matattu, da kuma madawwamin hukunci ba. (aiōnios )
及各種的洗禮,覆手,死者復活和永遠審判的道理。 (aiōnios )
3 Da yardar Allah, za mu ci gaba ga ƙarin ganewa.
如果天主准許,我們就這育樣去作。
4 Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki,
的確,那些曾一次被光照,嘗過天上的恩賜,成了有分於聖神,
5 waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, (aiōn )
並嘗過天主甘美的言語,及未來世代德能的人 (aiōn )
6 ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a.
如果背棄了正道,再叫衪們自新悔改,是不可能的,因為衪們親自又把天主子釘在十字架上,公開加以凌辱。
7 Ƙasar da take shan ruwan sama da yake fāɗi a kanta kullum da kuma take ba da hatsin da yake da amfani ga waɗanda ake noma dominsu, takan sami albarkar Allah.
就如一塊田地,時有雨水降於其上,時受潤澤:若出產有益於那種植者的蔬菜,就必蒙受天主的祝福;
8 Amma ƙasar da take ba da ƙaya da sarƙaƙƙiya ba ta da amfani tana kuma cikin hatsarin la’ana. A ƙarshe za a ƙone ta.
但若生出荊棘疾藜來,就必被廢棄,必要受詛咒,它的結局就市焚燒。
9 Abokaina, ko da yake muna irin maganan nan, mun tabbata kuna yi abubuwan nan masu kyau da waɗanda suka sami ceto suke yi.
可是,親愛的諸位,我們雖這樣說,但對你們,我們確信你們將有更好的表現,更近於救恩,
10 Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai manta da aikinku da kuma ƙaunar da kuka nuna masa wajen taimakon mutanensa da kuma ci gaba da taimakonsu da kuke yi ba.
因為天主不是不公義的,甚至於忘掉了你們的善工和愛德,即你們為了衪的名,在過去和現在,在服事聖徒的事上所表現的愛德。
11 Muna so kowannenku yă nuna ƙwazon nan har zuwa ƙarshe, domin ku tabbatar da begenku.
我們只願你們每一位表現同樣的熱,心以答達成你們的希望,一直到底。
12 Ba ma so ku zama masu ƙyuya, sai dai ku yi koyi da waɗanda ta wurin bangaskiya da haƙuri suka gāji abin da aka yi alkawari.
這樣,你們不但不會懈怠,而且還會效法那些因信德和耐心而繼承恩許的人。
13 Babu wanda ya fi Allah, saboda haka sa’ad da ya yi alkawari ga Ibrahim, sai ya rantse da sunansa,
當天主應許亞巴郎的時後,因為沒有一個比天主大而能指著起誓的,就指著自己起誓,
14 cewa, “Tabbatacce zan albarkace ka in kuma ba ka zuriya mai yawa.”
說:『我必多多祝福你,使你的後裔繁多。
15 Haka kuwa bayan Ibrahim ya jira da haƙuri, sai ya karɓi abin da aka yi alkawari.
這樣亞巴郎因耐心等待,而獲得了恩許。
16 In mutane za su yi rantsuwa sukan yi haka da wanda ya fi su ne, rantsuwar kuwa takan tabbatar da abin da aka faɗa ta kuma kawo ƙarshen dukan gardama.
人都是指著比自己大的起誓;以起誓作擔保,了結一切爭端。
17 Saboda haka da Allah ya so yă bayyana nufinsa marar canjawa a sarari ga magādan abin da aka yi alkawari, sai ya tabbatar da shi da rantsuwa.
為此天主願意向繼承恩許的人,充分顯示自己不可更改的旨意,就以起誓來自作擔保,
18 Allah ba ya karya! Haka ma alkawuransa da rantsuwarsa abubuwa biyu ne da ba a iya canjawa. Mun gudu zuwa wurin Allah domin kāriya. Ya kamata alkawuransa su ƙarfafawa sosai mu riƙe begen nan da yake gabanmu.
好叫我們這些尋求避難所的人,因這兩種不可更改的事----在這些事上天主決不會撒謊----得到一種強有力的鼓勵,去抓住那擺在目前的希望。
19 Muna da wannan bege kamar anka na rai, kafaffe da kuma tabbatacce. Yana shiga tsattsarkan wuri na can ciki a bayan labule,
我們拿這希望,當作靈魂的安全而又堅固的錨,深深地拋入帳幔的內部。
20 inda Yesu, wanda ya sha gabanmu, ya shiga a madadinmu. Ya zama babban firist na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek. (aiōn )
作前驅的耶穌已為我們進入了那帳幔內部,按照默基瑟德品位做了永遠的大司祭。 (aiōn )