< Ibraniyawa 5 >
1 Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.
For every high priest taken from among men, is ordained for men in the things that appertain to God, that he may offer up gifts and sacrifices for sins:
2 Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.
Who can have compassion on them that are ignorant and that err: because he himself also is compassed with infirmity.
3 Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.
And therefore he ought, as for the people, so also for himself, to offer for sins.
4 Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.
Neither doth any man take the honour to himself, but he that is called by God, as Aaron was.
5 Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka.”
So Christ also did not glorify himself, that he might be made a high priest: but he that said unto him: Thou art my Son, this day have I begotten thee.
6 Ya kuma ya ce a wani wuri, “Kai firist ne na har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.” (aiōn )
As he saith also in another place: Thou art a priest for ever, according to the order of Melchisedech. (aiōn )
7 A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi.
Who in the days of his flesh, with a strong cry and tears, offering up prayers and supplications to him that was able to save him from death, was heard for his reverence.
8 Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala
And whereas indeed he was the Son of God, he learned obedience by the things which he suffered:
9 kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. (aiōnios )
And being consummated, he became, to all that obey him, the cause of eternal salvation. (aiōnios )
10 Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.
Called by God a high priest according to the order of Melchisedech.
11 Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa.
Of whom we have much to say, and hard to be intelligibly uttered: because you are become weak to hear.
12 Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba!
For whereas for the time you ought to be masters, you have need to be taught again what are the first elements of the words of God: and you are become such as have need of milk, and not of strong meat.
13 Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba.
For every one that is a partaker of milk, is unskillful in the word of justice: for he is a little child.
14 Amma abinci mai kauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta.
But strong meat is for the perfect; for them who by custom have their senses exercised to the discerning of good and evil.