< Ibraniyawa 13 >

1 Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar’yan’uwa.
Let brotherly love continue.
2 Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.
Be not forgetful to entertain strangers: for by this some have entertained angels unawares.
3 Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.
Remember them that are in bonds, as bound with them; and them who suffer adversity, as being yourselves also in the body.
4 Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.
Marriage is honourable in all, and the bed undefiled: but fornicators and adulterers God will judge.
5 Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”
Let your manner of life be without covetousness; and be content with such things as ye have: for he hath said, I will never leave thee, nor forsake thee.
6 Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”
So that we may boldly say, The Lord is my helper, and I will not fear what man shall do to me.
7 Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.
Remember them who have the rule over you, who have spoken to you the word of God: whose faith follow, considering the end of their manner of life.
8 Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada. (aiōn g165)
Jesus Christ the same yesterday, and to day, and for ever. (aiōn g165)
9 Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu.
Be not carried about with various and strange doctrines. For it is a good thing that the heart be established with grace; not with meats, which have not profited them that have been occupied in them.
10 Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci.
We have an altar, of which they have no right to eat who serve the tabernacle.
11 Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani.
For the bodies of those beasts, whose blood is brought into the sanctuary by the high priest for sin, are burned outside the camp.
12 Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa.
Therefore Jesus also, that he might sanctify the people with his own blood, suffered outside the gate.
13 Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha.
Let us go forth therefore to him outside the camp, bearing his reproach.
14 Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
For here we have no continuing city, but we seek one to come.
15 Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa.
By him therefore let us offer the sacrifice of praise to God continually, that is, the fruit of our lips giving thanks to his name.
16 Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
But to do good and to share forget not: for with such sacrifices God is well pleased.
17 Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.
Obey them that have the rule over you, and submit yourselves: for they watch for your souls, as they that must give account, that they may do it with joy, and not with grief: for that is unprofitable for you.
18 Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya.
Pray for us: for we trust we have a good conscience, in all things willing to live honestly.
19 Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.
But I beseech you the rather to do this, that I may be restored to you the sooner.
20 Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, (aiōnios g166)
Now the God of peace, that brought again from the dead our Lord Jesus, that great shepherd of the sheep, through the blood of the everlasting covenant, (aiōnios g166)
21 yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin. (aiōn g165)
Make you perfect in every good work to do his will, working in you that which is wellpleasing in his sight, through Jesus Christ; to whom be glory for ever and ever. Amen. (aiōn g165)
22 ’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba.
And I beseech you, brethren, bear with this word of exhortation: for I have written a letter to you in few words.
23 Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.
Know ye that our brother Timothy is set at liberty; with whom, if he come shortly, I will see you.
24 Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah. Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.
Greet all them that have the rule over you, and all the saints. They of Italy greet you.
25 Alheri yă kasance da ku duka.
Grace be with you all. Amen. Written to the Hebrews from Italy, by Timothy.

< Ibraniyawa 13 >