< Haggai 1 >

1 A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.
in anno secundo Darii regis in mense sexto in die una mensis factum est verbum Domini in manu Aggei prophetae ad Zorobabel filium Salathihel ducem Iuda et ad Iesum filium Iosedech sacerdotem magnum dicens
2 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Waɗannan mutane sun ce, ‘Lokaci bai yi ba tukuna da za a gina gidan Ubangiji.’”
haec ait Dominus exercituum dicens populus iste dicit nondum venit tempus domus Domini aedificandae
3 Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai cewa,
et factum est verbum Domini in manu Aggei prophetae dicens
4 “Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi da rufin katako, amma haikalin nan yana zaman kufai?”
numquid tempus vobis est ut habitetis in domibus laqueatis et domus ista deserta
5 To, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku.
et nunc haec dicit Dominus exercituum ponite corda vestra super vias vestras
6 Kun shuka da yawa, amma kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha, amma ba ku kashe ƙishirwa ba. Kun sa tufafi, amma ba ku ji ɗumi ba. Kuna karɓar albashi, ya zama sai ka ce kuna zuba a hudajjen aljihu.”
seminastis multum et intulistis parum comedistis et non estis satiati bibistis et non estis inebriati operuistis vos et non estis calefacti et qui mercedes congregavit misit eas in sacculum pertusum
7 Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Ku lura da al’amuranku.
haec dicit Dominus exercituum ponite corda vestra super vias vestras
8 Ku haura zuwa kan duwatsu ku sauko da katakai don ku gina gidan, don ni ma in ji daɗinsa, in kuma sami ɗaukaka,” in ji Ubangiji.
ascendite in montem portate lignum et aedificate domum et acceptabilis mihi erit et glorificabor dicit Dominus
9 “Ga shi, kukan sa rai za ku sami da yawa, amma sai ku ga kun sami kaɗan. Ɗan kaɗan ɗin ma da kukan kawo gida, nakan hura shi yă tafi. Me ya sa yake faruwa haka?” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda gidana da yake zaman kango, yayinda kowannenku yana faman gina gidansa.
respexistis ad amplius et ecce factum est minus et intulistis in domum et exsuflavi illud quam ob causam dicit Dominus exercituum quia domus mea deserta est et vos festinatis unusquisque in domum suam
10 Shi ya sa, saboda ku sammai sun ƙi saukar da raɓa, ƙasa kuma ta ƙi ba da amfani.
propter hoc super vos prohibiti sunt caeli ne darent rorem et terra prohibita est ne daret germen suum
11 Na kawo fări a ƙasar, da a kan duwatsu, da a kan hatsi, da a kan dukan abin da yake tsirowa daga ƙasa, da a kan mutane, da a kan dabbobi da kuma a kan wahalar hannuwanku.”
et vocavi siccitatem super terram et super montes et super triticum et super vinum et super oleum et quaecumque profert humus et super homines et super iumenta et super omnem laborem manuum
12 Sa’an nan sai Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, wanda yake babban firist, da kuma dukan raguwar jama’ar suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu da kuma saƙon annabi Haggai, domin Ubangiji Allahnsu ne ya aiko shi. Mutane kuwa suka ji tsoron Ubangiji.
et audivit Zorobabel filius Salathihel et Iesus filius Iosedech sacerdos magnus et omnes reliquiae populi vocem Dei sui et verba Aggei prophetae sicut misit eum Dominus Deus eorum ad ipsos et timuit populus a facie Domini
13 Sai Haggai, ɗan saƙon Ubangiji, ya ba da wannan saƙo na Ubangiji ga mutane cewa, “Ina tare da ku” in ji Ubangiji.
et dixit Aggeus nuntius Domini de nuntiis Domini populo dicens ego vobiscum dicit Dominus
14 Saboda haka Ubangiji ya motsa zuciyar Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, wanda yake gwamna a Yahuda, da kuma zuciyar Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da kuma zukatan dukan raguwar jama’ar. Suka zo suka fara aiki a gidan Ubangiji Maɗaukaki, Allahnsu,
et suscitavit Dominus spiritum Zorobabel filii Salathihel ducis Iuda et spiritum Iesu filii Iosedech sacerdotis magni et spiritum reliquorum de omni populo et ingressi sunt et faciebant opus in domo Domini exercituum Dei sui
15 a ranar ashirin da huɗu ga watan shida. A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus,
in die vicesima et quarta mensis in sexto mense in anno secundo Darii regis

< Haggai 1 >