< Habakkuk 1 >

1 Saƙon da annabi Habakkuk ya karɓa.
המשא אשר חזה חבקוק הנביא
2 Har yaushe, ya Ubangiji, zan yi kukan neman taimako, amma ka ƙi ji? Ina kuka a gare ka saboda zalunci amma ba ka ce ufam ba.
עד אנה יהוה שועתי ולא תשמע אזעק אליך חמס ולא תושיע
3 Me ya sa ka bari ina ta kallon rashin gaskiya? Me ya sa kake barin abin da ba daidai ba? Hallaka da tashin hankali suna a gabana; ga rashin jituwa da faɗa ko’ina.
למה תראני און ועמל תביט ושד וחמס לנגדי ויהי ריב ומדון ישא
4 Saboda haka ba a bin doka, shari’a kuma ba ta aiki. Mugaye sun kewaye masu adalci don a hana gaskiya tă yi aiki.
על כן תפוג תורה ולא יצא לנצח משפט כי רשע מכתיר את הצדיק על כן יצא משפט מעקל
5 “Ka dubi al’ummai, ka gani, ka sha mamaki. Ga shi zan yi wani abu a kwanakinka, wanda ko ma an faɗa maka ba za ka gaskata ba.
ראו בגוים והביטו והתמהו תמהו כי פעל פעל בימיכם לא תאמינו כי יספר
6 Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.
כי הנני מקים את הכשדים הגוי המר והנמהר ההולך למרחבי ארץ לרשת משכנות לא לו
7 Suna da bantsoro da firgitarwa; dokoki da ƙa’idodinsu ne kawai suka sani.
אים ונורא הוא ממנו משפטו ושאתו יצא
8 Dawakansu sun fi damisoshi sauri, sun fi kyarketan yamma zafin rai. Mahayansu suna zuwa a guje; mahayansu daga nesa suka fito. Suna firiya kamar ungulu mai sauka da gaggawa don yă ci mushe;
וקלו מנמרים סוסיו וחדו מזאבי ערב ופשו פרשיו ופרשיו מרחוק יבאו--יעפו כנשר חש לאכול
9 duk sukan zo da nufin tā-da-na-zaune-tsaye. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su iso suna tattara bayi kamar yashi.
כלה לחמס יבוא מגמת פניהם קדימה ויאסף כחול שבי
10 Sukan yi wa sarakuna ba’a su kuma rena masu mulki. Sukan yi wa dukan birane masu mafaka dariya; sukan tara ƙasa su hau, su cinye abokan gābansu da yaƙi.
והוא במלכים יתקלס ורזנים משחק לו הוא לכל מבצר ישחק ויצבר עפר וילכדה
11 Sa’an nan su wuce da sauri kamar iska, mutane ne masu laifi, waɗanda ƙarfinsu shi ne allahnsu.”
אז חלף רוח ויעבר ואשם זו כחו לאלהו
12 Ya Ubangiji, ba tun fil azal kake ba? Ya Allahna, Mai Tsarkina, ba za mu mutu ba. Ya Ubangiji ka sanya su su tabbatar da hukunci; Ya Dutse, ka naɗa su don su yi hukunci.
הלוא אתה מקדם יהוה אלהי קדשי--לא נמות יהוה למשפט שמתו וצור להוכיח יסדתו
13 Idanunka masu tsarki ne da suka fi gaban duban mugunta; ba ka amince da abin da ke ba daidai ba. To, don me ka ƙyale munafukai suna cin karensu ba babbaka? Me ya sa kake shiru sa’ad da mugaye suke haɗiye adalai da suka fi su adalci?
טהור עינים מראות רע והביט אל עמל לא תוכל למה תביט בוגדים--תחריש בבלע רשע צדיק ממנו
14 Ka mai da maza kamar kifin teku, kamar halittun tekun da ba su da shugaba.
ותעשה אדם כדגי הים--כרמש לא משל בו
15 Mugu abokin gāba yakan kama su duka da ƙugiya, yă jawo su waje da abin kamun kifinsa, yă tattara su cikin ragarsa, ta haka yakan yi murna da farin ciki.
כלה בחכה העלה--יגרהו בחרמו ויאספהו במכמרתו על כן ישמח ויגיל
16 Saboda haka yakan yi hadaya wa abin kamun kifinsa yă kuma ƙona turare wa ragarsa, domin ta wurin abin kamun kifinsa ne yake yin rayuwar jin daɗi yă kuma zaɓi irin abincin da yake so.
על כן יזבח לחרמו ויקטר למכמרתו כי בהמה שמן חלקו ומאכלו בראה
17 Zai ci gaba da juye abin kamun kifinsu ke nan, suna hallaka al’ummai ba tausayi?
העל כן יריק חרמו ותמיד להרג גוים לא יחמול

< Habakkuk 1 >