< Habakkuk 3 >
1 Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont.
2 Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.
3 Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. (Sela) Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.
4 Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.
5 Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.
6 Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.
7 Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.
8 Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?
9 Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. (Sela) Ka raba duniya da koguna;
10 duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.
11 Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.
12 Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.
13 Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. (Sela)
14 Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye.
15 Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.
16 Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.
17 Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,
18 duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.
19 Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.