< Habakkuk 2 >
1 Zan tsaya wurin tsarona in kuma zauna a kan katanga; zan jira in ga abin da zai ce mini, da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka.
2 Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai.
3 Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.
4 “Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai; sha’awarsa ba daidai ba ce, amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa,
5 ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu. (Sheol )
6 “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’
7 Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.
8 Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
9 “Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba don yă kafa sheƙarsa can bisa, don yă tsere wa zama kango!
10 Ka ƙulla lalacin mutane masu yawa, ta haka ka kunyatar da gidanka ka kuma hallaka ranka.
11 Duwatsun katanga za su yi kuka, ginshiƙan katako kuma za su amsa.
12 “Kaiton mutumin da ya gina birni da jinin da ya zubar ya kuma kafa gari ta wurin mugun aiki!
13 Ba Ubangiji Maɗaukaki ne ya ƙudura cewa wahalar mutane ta zama mai kawai don wuta ba, cewa al’ummai su gajiyar da kansu a banza ba?
14 Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku.
15 “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha, yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu, don dai yă ga tsiraicinsu.
16 Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka! Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai, abin kunya kuma zai rufe darajarka.
17 Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
18 “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.
19 Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.”
20 Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki; bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.