< Farawa 6 >
1 Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu’ya’ya mata,
當人在世上多起來、又生女兒的時候,
2 sai’ya’yan Allah maza suka ga cewa’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.
上帝的兒子們看見人的女子美貌,就隨意挑選,娶來為妻。
3 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.”
耶和華說:「人既屬乎血氣,我的靈就不永遠住在他裏面;然而他的日子還可到一百二十年。」
4 Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da’ya’yan Allah suka kwana da’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.
那時候有偉人在地上,後來上帝的兒子們和人的女子們交合生子;那就是上古英武有名的人。
5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
耶和華見人在地上罪惡很大,終日所思想的盡都是惡,
6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai.
耶和華就後悔造人在地上,心中憂傷。
7 Saboda haka Ubangiji ya ce, “Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su.”
耶和華說:「我要將所造的人和走獸,並昆蟲,以及空中的飛鳥,都從地上除滅,因為我造他們後悔了。」
8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.
惟有挪亞在耶和華眼前蒙恩。
9 Ga tarihin Nuhu. Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.
挪亞的後代記在下面。挪亞是個義人,在當時的世代是個完全人。挪亞與上帝同行。
10 Nuhu yana da’ya’ya maza uku, Shem, Ham da Yafet.
挪亞生了三個兒子,就是閃、含、雅弗。
11 Duniya dai ta lalace sosai a gaban Allah, ta kuma cika da tashin hankali.
世界在上帝面前敗壞,地上滿了強暴。
12 Allah ya ga yadda duniya ta lalace, gama dukan mutane a duniya sun lalatar da rayuwarsu.
上帝觀看世界,見是敗壞了;凡有血氣的人在地上都敗壞了行為。
13 Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, “Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya.
上帝就對挪亞說:「凡有血氣的人,他的盡頭已經來到我面前;因為地上滿了他們的強暴,我要把他們和地一併毀滅。
14 Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires, ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje.
你要用歌斐木造一隻方舟,分一間一間地造,裏外抹上松香。
15 Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45.
方舟的造法乃是這樣:要長三百肘,寬五十肘,高三十肘。
16 Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin. Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
方舟上邊要留透光處,高一肘。方舟的門要開在旁邊。方舟要分上、中、下三層。
17 Ga shi zan aiko da ambaliya ruwa a duniya, in hallaka dukan mai rai da yake a ƙarƙashin sama, kowace halittar da take numfashi a cikinta. Dukan abin da yake a duniya zai hallaka.
看哪,我要使洪水氾濫在地上,毀滅天下;凡地上有血肉、有氣息的活物,無一不死。
18 Amma zan kafa alkawarina da kai, kai kuma za ka shiga jirgin, kai da’ya’yanka maza da matarka da matan’ya’yanka tare da kai.
我卻要與你立約;你同你的妻,與兒子兒婦,都要進入方舟。
19 Za ka shigar da biyu na dukan halittu masu rai, namiji da ta mace a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai.
凡有血肉的活物,每樣兩個,一公一母,你要帶進方舟,好在你那裏保全生命。
20 Biyu na kowane irin tsuntsu, kowace irin dabba da kuma kowace irin halitta mai rarrafe a ƙasa, za su zo wurinka domin a bar su da rai.
飛鳥各從其類,牲畜各從其類,地上的昆蟲各從其類,每樣兩個,要到你那裏,好保全生命。
21 Za ka ɗauki kowane irin abinci wanda za a ci, ka adana don yă zama abincinka da nasu.”
你要拿各樣食物積蓄起來,好作你和牠們的食物。」
22 Nuhu ya yi kome kamar yadda Allah ya umarce shi.
挪亞就這樣行。凡上帝所吩咐的,他都照樣行了。
![The World is Destroyed by Water](/resources/Gustave-Dore-La-Grande-Bible-de-Tours/web/Gustave-Dore-Bible-Tour-Hebrew-OT-006-The-World-is-Destroyed-by-Water.jpg)
The World is Destroyed by Water