< Farawa 5 >

1 Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah.
این است شرح پیدایش آدم و نسل او. هنگامی که خدا خواست انسان را بیافریند، او را شبیه خود آفرید.
2 Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.”
او آنها را مرد و زن خلق فرموده، برکت داد و از همان آغاز خلقت، ایشان را انسان نامید.
3 Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
آدم: وقتی آدم ۱۳۰ ساله بود، پسرش شیث به دنیا آمد. او شبیه پدرش آدم بود. بعد از تولد شیث، آدم ۸۰۰ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. آدم در سن ۹۳۰ سالگی مرد.
4 Bayan an haifi Set, Adamu ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
5 Gaba ɗaya dai, Adamu ya yi shekaru 930, sa’an nan ya mutu.
6 Sa’ad da Set ya yi shekara 105, sai ya haifi Enosh.
شیث: وقتی شیث ۱۰۵ ساله بود، پسرش انوش به دنیا آمد. بعد از تولد انوش، شیث ۸۰۷ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. شیث در سن ۹۱۲ سالگی مرد.
7 Bayan ya haifi Enosh, Set ya yi shekara 807, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
8 Gaba ɗaya dai, Set ya yi shekaru 912, sa’an nan ya mutu.
9 Sa’ad da Enosh ya yi shekara 90, sai ya haifi Kenan.
انوش: وقتی انوش نود ساله بود، پسرش قینان به دنیا آمد. بعد از تولد قینان، انوش ۸۱۵ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. انوش در سن ۹۰۵ سالگی مرد.
10 Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya yi shekara 815, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
11 Gaba ɗaya dai, Enosh ya yi shekaru 905, sa’an nan ya mutu.
12 Sa’ad da Kenan ya yi shekara 70, sai ya haifi Mahalalel.
قینان: وقتی قینان هفتاد ساله بود، پسرش مهلل‌ئیل به دنیا آمد. بعد از تولد مهلل‌ئیل، قینان ۸۴۰ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. او در سن ۹۱۰ سالگی مرد.
13 Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekara 840, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata
14 Gaba ɗaya dai, Kenan ya yi shekara 910, sa’an nan ya mutu.
15 Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara 65, sai ya haifi Yared.
مهلل‌ئیل: وقتی مهلل‌ئیل شصت و پنج ساله بود، پسرش یارد به دنیا آمد. پس از تولد یارد، مهلل‌ئیل ۸۳۰ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. او در سن ۸۹۵ سالگی مرد.
16 Bayan ya haifi Yared, Mahalalel ya yi shekara 830, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata
17 Gaba ɗaya dai, Mahalalel ya yi shekara 895, sa’an nan ya mutu.
18 Sa’ad da Yared ya yi shekara 162, sai ya haifi Enok.
یارد: وقتی یارد ۱۶۲ ساله بود، پسرش خنوخ به دنیا آمد. بعد از تولد خنوخ، یارد ۸۰۰ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. یارد در سن ۹۶۲ سالگی مرد.
19 Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru 800, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
20 Gaba ɗaya dai, Yared ya yi shekara 962, sa’an nan ya mutu.
21 Sa’ad da Enok ya yi shekara 65, sai ya haifi Metusela.
خنوخ: وقتی خنوخ شصت و پنج ساله بود، پسرش متوشالح به دنیا آمد. بعد از تولد متوشالح، خنوخ ۳۰۰ سال دیگر با خدا زیست. او صاحب پسران و دخترانی شد و ۳۶۵ سال زندگی کرد. خنوخ با خدا می‌زیست و خدا او را به حضور خود به بالا برد و دیگر کسی او را ندید.
22 Bayan ya haifi Metusela, Enok ya kasance cikin zumunci da Allah shekaru 300, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
23 Gaba ɗaya dai, Enok ya yi shekaru 365.
24 Enok ya kasance cikin zumunci da Allah, sa’an nan ba a ƙara ganinsa ba. Saboda Allah ya ɗauke shi.
25 Sa’ad da Metusela ya yi shekara 187, sai ya haifi Lamek.
متوشالح: وقتی متوشالح ۱۸۷ ساله بود، پسرش لمک به دنیا آمد. بعد از تولد لمک، متوشالح ۷۸۲ سال دیگر زندگی کرد و صاحب پسران و دختران شد. متوشالح در سن ۹۶۹ سالگی مرد.
26 Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
27 Gaba ɗaya dai, Metusela ya yi shekaru 969, sa’an nan ya mutu.
28 Sa’ad da Lamek ya yi shekara 182, sai ya haifi ɗa.
لمک: وقتی لمک ۱۸۲ ساله بود، پسرش نوح به دنیا آمد. لمک گفت: «این پسر، ما را از کار سختِ زراعت که در اثر لعنت خداوند بر زمین، دامنگیر ما شده، آسوده خواهد کرد.» پس لمک اسم او را نوح (یعنی «آسودگی») گذاشت. بعد از تولد نوح، لمک ۵۹۵ سال دیگر عمر کرد و صاحب پسران و دختران شد. او در سن ۷۷۷ سالگی مرد.
29 Ya ba shi suna Nuhu ya kuma ce, “Zai yi mana ta’aziyya a cikin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”
30 Bayan an haifi Nuhu, Lamek ya yi shekara 595, yana kuma da’ya’ya maza da mata.
31 Gaba ɗaya dai, Lamek ya yi shekaru 777, sa’an nan ya mutu.
32 Bayan Nuhu ya yi shekara 500, sai ya haifi Shem, Ham da Yafet.
نوح: نوح در سن ۵۰۰ سالگی صاحب سه پسر به نامهای سام، حام و یافث بود.

< Farawa 5 >