< Farawa 49 >
1 Sai Yaƙub ya kira’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.
Then Jacob summoned his sons, and said: "Gather yourselves together so that I may tell you what will happen to you in the days to come.
2 “Ku tattaru, ku saurara,’ya’yan Yaƙub maza; ku saurari mahaifinku, Isra’ila.
Assemble yourselves and hear, you sons of Jacob. Listen to Israel, your father.
3 “Ruben, kai ne ɗan farina, ƙarfina, alamar farko ta ƙarfina, mafi matsayi, kuma mafi iko.
Reuben, you are my firstborn, my strength, and the the firstfruits of my virility, preeminent in dignity and preeminent in power.
4 Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba, gama ka hau gadon mahaifinka ka hau kujerata, ka kuma ƙazantar da shi.
Uncontrolled as the waters, you will not have excel, because you went up to your father's bed, you went up and defiled my couch.
5 “Simeyon da Lawi’yan’uwa ne, takubansu makamai ne na tā da hankali.
Simeon and Levi are brothers. Their swords are weapons of violence.
6 Ba zan shiga shawararsu ba, ba zan shiga taronsu ba, gama sun kashe maza cikin fushinsu cikin ganin dama suka kashe bijimai.
May I never enter their council. May my honor never be joined with their assembly. For in their anger they killed men, and for pleasure they hamstrung oxen.
7 La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai, hasalarsu kuwa, muguwa ce ƙwarai! Zan warwatsa su cikin Yaƙub in kuma daidaita su cikin Isra’ila.
Cursed be their anger, for it has been fierce, and their fury, for it was cruel. I will divide them in Jacob, and scatter them in Israel.
8 “Yahuda,’yan’uwanka za su yabe ka; hannuwanka za su kasance a wuyan abokan gābanka,’ya’yan mahaifinka maza za su rusuna maka.
Judah, your brothers will praise you. Your hand will be on the neck of your enemies. Your father's sons will bow down before you.
9 Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda, ka dawo daga farauta, ɗana. Kamar zaki, yakan kwanta a miƙe, kamar zakanya, wa yake da ƙarfin halin tashe shi?
Judah is a lion's cub. From the prey, my son, you rise up. Like a lion he crouches and lies down, as a lioness. Who will rouse him up?
10 Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba, ba kuwa sandan mulki daga tsakani ƙafafunsa ba, sai ya zo ga wanda yake mai shi. Biyayyar al’umma kuwa tasa ce.
The scepter will not depart from Judah, nor the ruler's staff from between his feet, until he comes to whom it belongs. And it is he whom the peoples will obey.
11 Zai daure jakinsa a kuringa, aholakinsa a rassa mafi kyau; zai wanke tufafinsa cikin ruwan inabi rigunansa cikin inabi ja wur kamar jini.
Binding his foal to the vine, and his donkey's colt to the choice vine. He will wash his garments in wine, and his robes in the blood of grapes.
12 Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi, haƙorarsa farare kamar madara.
His eyes will be darker than wine, and his teeth whiter than milk.
13 “Zebulun zai zauna a bakin teku, yă zama tasar jiragen ruwa; iyakarsa za tă nausa zuwa Sidon.
Zebulun will dwell at the seashore, and he will be a harbor for ships, and his border will be at Sidon.
14 “Issakar doki mai ƙarfi, kwance tsakanin buhunan sirdi.
Issachar is a strong donkey lying down between the saddlebags.
15 Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau da kuma daɗin da ƙasarsa take, zan tanƙware kafaɗarsa ga nauyi yă miƙa kai ga aikin dole.
When he sees a good resting place, that the land is pleasant, he will bend his back to the burden, and become a slave doing forced labor.
16 “Dan zai tanada adalci wa mutanensa kamar ɗaya cikin kabilan Isra’ila.
Dan will judge his people as one of the tribes of Israel.
17 Dan zai zama maciji a gefen hanya, kububuwa a bakin hanya, da take saran ɗiɗɗigen doki domin mahayinsa yă fāɗi da baya.
Dan will be a serpent on the road, a viper by the path, that bites the horse's heels so that his rider falls backward.
18 “Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.
I wait for your salvation, God.
19 “Masu fashi za su fāɗa wa Gad, amma zai runtume su.
Gad will be attacked by raiders, but he will raid at their heels.
20 “Abincin Asher zai zama a wadace, zai yi tanadin abinci iri-iri da suka dace don sarki.
Asher's food will be rich, and he will provide royal delicacies.
21 “Naftali sakakkiyar barewa ce da take haihuwar kyawawan’ya’ya.
Naphtali is a doe set free that bears beautiful fawns.
22 “Yusuf kuringa ce mai ba da amfani. Kuringa mai ba da amfani kusa da rafi wadda rassanta na hawan bango.
Joseph is a fruitful son, a fruitful son by a spring. His branches run over a wall.
23 Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa; suka harbe shi babu tausayi.
The archers will attack him with bitterness, and shoot at him, and harass him.
24 Amma bakansa yana nan daram hannuwansa masu ƙarfi ba sa jijjiguwa saboda hannun Maɗaukaki na Yaƙub, saboda Makiyayi, Dutsen Isra’ila,
Yet his bow will remain steady, and his arms will be made agile by the hands of the Mighty One of Jacob, by the name of the Shepherd, the Rock of Israel,
25 saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka, saboda Maɗaukaki, wanda yake albarkace ka da albarkar sama da take bisa albarkun zurfafa da suke ƙarƙashin ƙasa albarkun mama da kuma mahaifa.
by the God of your father, who will help you, and El Shaddai, who will bless you with blessings of the sky above, blessings of the deep that lies below, and blessings of the breasts and of the womb.
26 Albarkun mahaifi suna da girma fiye da albarkun daɗaɗɗun duwatsu fiye da yalwar madawwaman tuddai. Bari dukan waɗannan su zauna a kan Yusuf, a goshin ɗan sarki a cikin’yan’uwansa.
The blessings of your father are greater than the blessings of the ancient mountains, and the bounty of the everlasting hills. They will be on the head of Joseph, and on the brow of the prince among his brothers.
27 “Benyamin kyarkeci ne mai kisa; da safe yakan cinye abin da ya farauto da yamma yakan raba ganima.”
Benjamin is a ravenous wolf. In the morning he will devour the prey, and at evening he will divide the plunder."
28 Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.
All these are the twelve tribes of Israel, and this is what their father said to them when he blessed them. He blessed each one with his own individual blessing.
29 Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,
Then he instructed them, and said to them, "I am to be gathered to my people. Bury me with my fathers in the cave that is in the field of Ephron the Hethite,
30 kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.
in the cave that is in the field of Machpelah, which is near Mamre in the land of Canaan, which Abraham bought along with the field from Ephron the Hethite as a burial place.
31 A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.
There they buried Abraham and his wife Sarah. There they buried Isaac and his wife Rebekah, and there I buried Leah.
32 Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”
The field and the cave that is in it were purchased from the sons of Heth."
33 Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.
When Jacob finished instructing his sons, he drew his legs up into the bed and breathed his last, and was gathered to his people.