< Farawa 45 >

1 Yusuf bai ƙara iya daurewa a gaban dukan masu yi masa hidima ba, sai ya yi kuka da ƙarfi ya ce, “Kowa yă tashi daga gabana!” Saboda haka ba kowa a wurin sa’ad da Yusuf ya sanar da kansa ga’yan’uwansa.
ולא יכל יוסף להתאפק לכל הנצבים עליו ויקרא הוציאו כל איש מעלי ולא עמד איש אתו בהתודע יוסף אל אחיו
2 Sai ya yi kuka da ƙarfi har Masarawa suka ji, har labarin ya kai gidan Fir’auna.
ויתן את קלו בבכי וישמעו מצרים וישמע בית פרעה
3 Yusuf kuwa ya ce wa’yan’uwansa, “Ni ne Yusuf! Mahaifina yana nan da rai har yanzu?” Amma’yan’uwansa ba su iya amsa masa ba, gama sun firgita ƙwarai a gabansa.
ויאמר יוסף אל אחיו אני יוסף העוד אבי חי ולא יכלו אחיו לענות אתו כי נבהלו מפניו
4 Sa’an nan Yusuf ya ce wa’yan’uwansa, “Ku zo kusa da ni.” Da suka yi haka, sai ya ce, “Ni ne ɗan’uwanku Yusuf, wannan da kuka sayar zuwa Masar!
ויאמר יוסף אל אחיו גשו נא אלי ויגשו ויאמר אני יוסף אחיכם אשר מכרתם אתי מצרימה
5 Yanzu dai, kada ku damu, kada kuma ku yi fushi da kanku saboda kun sayar da ni a nan, gama Allah ya aiko ni gabanku ne don in ceci rayuka.
ועתה אל תעצבו ואל יחר בעיניכם כי מכרתם אתי הנה כי למחיה שלחני אלהים לפניכם
6 Ga shi shekaru biyu ke nan ake yunwa a ƙasar, kuma da sauran shekara biyar masu zuwa da ba za a yi noma ko girbi ba.
כי זה שנתים הרעב בקרב הארץ ועוד חמש שנים אשר אין חריש וקציר
7 Amma Allah ya aiko ni gabanku ne don in adana muku raguwa a duniya, in kuma ceci rayukanku ta wurin ceto mai girma.
וישלחני אלהים לפניכם לשום לכם שארית בארץ ולהחיות לכם לפליטה גדלה
8 “Saboda haka fa, ba ku ba ne kuka aiko ni nan, Allah ne. Ya mai da ni mahaifi ga Fir’auna, shugaban dukan gidansa da kuma mai mulkin dukan Masar.
ועתה לא אתם שלחתם אתי הנה כי האלהים וישימני לאב לפרעה ולאדון לכל ביתו ומשל בכל ארץ מצרים
9 Yanzu sai ku gaggauta zuwa wurin mahaifina ku faɗa masa, ‘Abin da ɗanka Yusuf ya ce; Allah ya mai da ni shugaban dukan Masar. Gangaro wurina; kada ka jinkirta.
מהרו ועלו אל אבי ואמרתם אליו כה אמר בנך יוסף שמני אלהים לאדון לכל מצרים רדה אלי אל תעמד
10 Za ka yi zama a yankin Goshen, ka kasance kusa da ni. Kai,’ya’yanka da kuma jikokinka, garkunanka da shanunka, da kuma dukan abin da kake da shi.
וישבת בארץ גשן והיית קרוב אלי--אתה ובניך ובני בניך וצאנך ובקרך וכל אשר לך
11 Zan tanada maka a nan, domin akwai saura shekaru biyar na yunwa masu zuwa. In ba haka ba, kai da gidanka da dukan mallakarka za ku zama gajiyayyu.’
וכלכלתי אתך שם כי עוד חמש שנים רעב פן תורש אתה וביתך וכל אשר לך
12 “Ku kanku kun gani, haka ma ɗan’uwana Benyamin, cewa tabbatacce ni ne nake magana da ku.
והנה עיניכם ראות ועיני אחי בנימין כי פי המדבר אליכם
13 Faɗa wa mahaifina game da dukan girman da aka ba ni a Masar, da kuma game da kome da kuka gani. Ku kuma kawo mahaifina a nan da sauri.”
והגדתם לאבי את כל כבודי במצרים ואת כל אשר ראיתם ומהרתם והורדתם את אבי הנה
14 Sa’an nan ya rungume ɗan’uwansa Benyamin ya yi kuka, sai Benyamin ya rungume shi yana kuka.
ויפל על צוארי בנימן אחיו ויבך ובנימן--בכה על צואריו
15 Ya sumbaci dukan’yan’uwansa, ya kuma yi kuka a kansu. Bayan haka sai’yan’uwansa suka yi masa magana.
וינשק לכל אחיו ויבך עלהם ואחרי כן דברו אחיו אתו
16 Sa’ad da labarin ya kai fadan Fir’auna cewa’yan’uwan Yusuf sun zo, sai Fir’auna da dukan hafsoshin suka ji daɗi.
והקל נשמע בית פרעה לאמר באו אחי יוסף וייטב בעיני פרעה ובעיני עבדיו
17 Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Faɗa wa’yan’uwanka, ‘Yi wannan; ku jibge dabbobinku ku koma zuwa ƙasar Kan’ana,
ויאמר פרעה אל יוסף אמר אל אחיך זאת עשו טענו את בעירכם ולכו באו ארצה כנען
18 Ku kawo mahaifinku da iyalanku zuwa wurina. Zan ba ku mafi kyau na ƙasar Masar, za ku kuwa ci moriyar ƙasar.’
וקחו את אביכם ואת בתיכם ובאו אלי ואתנה לכם את טוב ארץ מצרים ואכלו את חלב הארץ
19 “An kuma umarce ka, ka faɗa musu, ‘Ku yi wannan, ku ɗauki wagonu daga Masar domin’ya’yanku da matanku, ku ɗauki mahaifinku ku zo.
ואתה צויתה זאת עשו קחו לכם מארץ מצרים עגלות לטפכם ולנשיכם ונשאתם את אביכם ובאתם
20 Kada ku damu da mallakarku, gama mafi kyau na Masar za su zama naku.’”
ועינכם אל תחס על כליכם כי טוב כל ארץ מצרים לכם הוא
21 Sai’ya’yan Isra’ila maza suka yi haka. Yusuf ya ba su wagonu kamar yadda Fir’auna ya umarta, ya kuma ba su guzuri don tafiyarsu.
ויעשו כן בני ישראל ויתן להם יוסף עגלות על פי פרעה ויתן להם צדה לדרך
22 Ya ba da sababbin riguna ga kowannensu amma ga Benyamin ya ba shi shekel ɗari uku na azurfa da riguna kashi biyar.
לכלם נתן לאיש חלפות שמלת ולבנימן נתן שלש מאות כסף וחמש חלפת שמלת
23 Ga kuma abin da ya aika wa mahaifinsa, jakuna goma da aka jibge da abubuwa mafi kyau na Masar, da jakuna mata guda goma ɗauke da hatsi da burodi da waɗansu tanade-tanade don tafiyarsa.
ולאביו שלח כזאת עשרה חמרים נשאים מטוב מצרים ועשר אתנת נשאת בר ולחם ומזון לאביו--לדרך
24 Sa’an nan ya sallami’yan’uwansa, yayinda suke barin wurin ya ce musu, “Kada ku yi faɗa a hanya!”
וישלח את אחיו וילכו ויאמר אלהם אל תרגזו בדרך
25 Saboda haka suka haura, suka fita daga Masar, suka zo wurin maihaifinsu Yaƙub a ƙasar Kan’ana.
ויעלו ממצרים ויבאו ארץ כנען אל יעקב אביהם
26 Suka faɗa masa, “Yusuf yana da rai! Gaskiya, shi ne mai mulkin dukan Masar.” Gaban Yaƙub ya fāɗi, domin bai gaskata su ba.
ויגדו לו לאמר עוד יוסף חי וכי הוא משל בכל ארץ מצרים ויפג לבו כי לא האמין להם
27 Amma sa’ad da suka faɗa masa kome da Yusuf ya faɗa musu, da kuma sa’ad da ya ga wagonun da Yusuf ya aika don a ɗauke shi a kai da shi can, sai ya farfaɗo, ya dawo cikin hankalinsa.
וידברו אליו את כל דברי יוסף אשר דבר אלהם וירא את העגלות אשר שלח יוסף לשאת אתו ותחי רוח יעקב אביהם
28 Sai Yaƙub ya ce, “Na yarda! Ɗana Yusuf yana da rai har yanzu. Zan tafi in gan shi kafin in mutu.”
ויאמר ישראל רב עוד יוסף בני חי אלכה ואראנו בטרם אמות

< Farawa 45 >