< Farawa 4 >

1 Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.”
Adam vero cognovit Havam uxorem suam quae concepit et peperit Cain dicens possedi hominem per Dominum
2 Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila. Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi.
rursusque peperit fratrem eius Abel fuit autem Abel pastor ovium et Cain agricola
3 Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji.
factum est autem post multos dies ut offerret Cain de fructibus terrae munera Domino
4 Amma Habila ya kawo mafi kyau daga’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo,
Abel quoque obtulit de primogenitis gregis sui et de adipibus eorum et respexit Dominus ad Abel et ad munera eius
5 amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.
ad Cain vero et ad munera illius non respexit iratusque est Cain vehementer et concidit vultus eius
6 Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace?
dixitque Dominus ad eum quare maestus es et cur concidit facies tua
7 Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”
nonne si bene egeris recipies sin autem male statim in foribus peccatum aderit sed sub te erit appetitus eius et tu dominaberis illius
8 To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
dixitque Cain ad Abel fratrem suum egrediamur foras cumque essent in agro consurrexit Cain adversus Abel fratrem suum et interfecit eum
9 Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
et ait Dominus ad Cain ubi est Abel frater tuus qui respondit nescio num custos fratris mei sum
10 Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.
dixitque ad eum quid fecisti vox sanguinis fratris tui clamat ad me de terra
11 Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka.
nunc igitur maledictus eris super terram quae aperuit os suum et suscepit sanguinem fratris tui de manu tua
12 In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”
cum operatus fueris eam non dabit tibi fructus suos vagus et profugus eris super terram
13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina.
dixitque Cain ad Dominum maior est iniquitas mea quam ut veniam merear
14 Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
ecce eicis me hodie a facie terrae et a facie tua abscondar et ero vagus et profugus in terra omnis igitur qui invenerit me occidet me
15 Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi.
dixitque ei Dominus nequaquam ita fiet sed omnis qui occiderit Cain septuplum punietur posuitque Dominus Cain signum ut non eum interficeret omnis qui invenisset eum
16 Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod a gabashin Eden.
egressusque Cain a facie Domini habitavit in terra profugus ad orientalem plagam Eden
17 Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok.
cognovit autem Cain uxorem suam quae concepit et peperit Enoch et aedificavit civitatem vocavitque nomen eius ex nomine filii sui Enoch
18 Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.
porro Enoch genuit Irad et Irad genuit Maviahel et Maviahel genuit Matusahel et Matusahel genuit Lamech
19 Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla.
qui accepit uxores duas nomen uni Ada et nomen alteri Sella
20 Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi.
genuitque Ada Iabel qui fuit pater habitantium in tentoriis atque pastorum
21 Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa.
et nomen fratris eius Iubal ipse fuit pater canentium cithara et organo
22 Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe.’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.
Sella quoque genuit Thubalcain qui fuit malleator et faber in cuncta opera aeris et ferri soror vero Thubalcain Noemma
23 Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla, “Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata. Na kashe wani saboda ya yi mini rauni, na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.
dixitque Lamech uxoribus suis Adae et Sellae audite vocem meam uxores Lamech auscultate sermonem meum quoniam occidi virum in vulnus meum et adulescentulum in livorem meum
24 Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai, lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”
septuplum ultio dabitur de Cain de Lamech vero septuagies septies
25 Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.”
cognovit quoque adhuc Adam uxorem suam et peperit filium vocavitque nomen eius Seth dicens posuit mihi Deus semen aliud pro Abel quem occidit Cain
26 Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh. A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.
sed et Seth natus est filius quem vocavit Enos iste coepit invocare nomen Domini

< Farawa 4 >