< Farawa 39 >
1 To, aka kai Yusuf Masar, Fotifar wani mutumin Masar wanda yake ɗaya daga cikin hafsoshin Fir’auna, shugaban masu tsaro, ya saye shi daga mutanen Ishmayel waɗanda suka kai shi can.
ヨセフ挈へられてエジプトにくだりしがエジプト人ポテパル、パロの臣侍衞の長なる者彼を其處にたづさへくだれるイシマエル人の手よりこれを買ふ
2 Ubangiji kuwa yana tare da Yusuf, Yusuf kuwa yi nasara, ya zauna a gidan mutumin Masar maigidansa.
ヱホバ、ヨセフとともに在す彼享通者となりてその主人なるエジプト人の家にをる
3 Sa’ad da maigidansa ya ga cewa Ubangiji yana tare da Yusuf, kuma cewa Ubangiji ya ba shi nasara a kome da ya yi,
その主人ヱホバの彼とともにいますを見またヱホバがかれの手の凡てなすところを享通しめたまふを見たり
4 sai Yusuf ya sami tagomashi a idanunsa, ya kuma zama mai hidimarsa. Fotifar ya sa shi yă zama shugaba a gidansa, ya kuma danƙa masa kome da yake da shi.
是によりてヨセフ彼の心にかなひて其近侍となる彼ヨセフにその家を宰どらしめその所有を盡くその手に委たり
5 Daga lokacin da ya sa shi shugaban gidansa da kuma a kan dukan abin da yake da shi, sai Ubangiji ya albarkaci gidan mutumin Masar saboda Yusuf. Albarkar Ubangiji tana a kan kome da Fotifar yake da shi a gida da kuma a jeji.
彼ヨセフにその家とその有る凡の物をつかさどらせし時よりしてヱホバ、ヨセフのために其エジプト人の家を祝みたまふ即ちヱホバの祝福かれが家と田に有る凡の物におよぶ
6 Saboda haka sai ya bar kome a ƙarƙashin kulawar Yusuf, bai dame kansa a wani abu ba sai dai abincin da yake ci. To, fa, Yusuf ƙaƙƙarfa ne, kyakkyawa kuma,
彼その有る物をことごとくヨセフの手にゆだねその食ふパンの外は何もかへりみざりき夫ヨセフは容貌麗しくして顏美しかりき
7 bayan an ɗan jima sai matar maigidansa ta fara sha’awar Yusuf, sai ta ce, “Zo ka kwana da ni!”
これらの事の後その主人の妻ヨセフに目をつけて我と寢よといふ
8 Amma ya ƙi. Ya ce mata, “Ga shi kome yana a ƙarƙashina, don haka ne ma maigidana bai dami kansa da wani abu a cikin gidan nan ba; kome da ya mallaka, ya danƙa ga kulawata.
ヨセフ拒みて主人の妻にいひけるは視よわが主人の家の中の物をかへりみずその有るものことごとくわが手に委ぬ
9 Babu wani da ya fi ni a wannan gida. Maigidana bai hana ni kome ba sai ke, saboda ke matarsa ce. Yaya fa, zan yi irin wannan mugun abu, in yi zunubi wa Allah?”
この家には我より大なるものなし又主人何をも我に禁ぜず只汝を除くのみ汝はその妻なればなり然ば我いかで此おほいなる惡をなして神に罪ををかすをえんや
10 Ko da yake ta yi ta yin wa Yusuf maganar kowace rana, amma ya ƙi yă kwana da ita, ko ma yă zauna da ita.
彼日々にヨセフに言よりたれどもヨセフきかずして之といねず亦與にをらざりき
11 Wata rana, ya shiga cikin gida don yă yi ayyukansa, ba wani daga cikin bayin gidan da yake ciki.
當時ヨセフその職をなさんとて家にいりしが家の人一箇もその内にをらざりき
12 Sai ta cafke shi a riga, ta ce, “Zo ka kwana da ni!” Amma ya bar rigarsa a hannunta, ya gudu ya fita daga gidan.
時に彼婦その衣を執て我といねよといひければヨセフ衣を彼の手に棄おきて外に遁いでたり
13 Sa’ad da ta ga ya bar rigarsa a hannunta ya gudu ya fita daga gidan,
彼ヨセフがその衣を己の手に棄おきて遁いでしを見て
14 sai ta kira bayin gidan ta ce musu, “Duba, an kawo mana wannan mutumin Ibraniyawa don yă ci mutuncinmu! Ya zo nan don yă kwana da ni, amma na yi ihu.
その家の人々を呼てこれにいふ視よヘブル人を我等の所につれ來りて我等にたはむれしむ彼我といねんとて我の所にいり來りしかば我大聲によばはれり
15 Sa’ad da ya ji na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
彼わが聲をあげて呼はるを聞しかばその衣をわが許にすておきて外に遁いでたりと
16 Ta ajiye rigar kusa da ita sai da maigidansa ya dawo gida.
其衣を傍に置て主人の家に歸るを待つ
17 Sa’an nan ta faɗa masa wannan labari, “Mutumin Ibraniyawan, bawan da ka kawo mana, ya zo wurina don yă ci mutuncina.
かくて彼是言のごとく主人につげていふ汝が我らに携へきたりしヘブルの僕われにたはむれんとて我許にいりきたりしが
18 Amma da zarar na yi ihu neman taimako, sai ya bar rigarsa kusa da ni, ya gudu ya fita daga gida.”
我聲をあげてよばはりしかばその衣を我許にすておきて遁いでたり
19 Sa’ad da maigidansa ya ji labarin da matarsa ta faɗa masa cewa, “Ga yadda bawanka ya yi da ni,” sai ya husata.
主人その妻が己につげて汝の僕斯のごとく我になせりといふ言を聞て怒を發せり
20 Maigidan Yusuf ya ɗauke shi ya sa a kurkuku, wurin da ake tsare’yan kurkukun sarki. Amma yayinda Yusuf yake can a cikin kurkuku,
是に於てヨセフの主人彼を執へて獄にいる其獄は王の囚徒を繋ぐ所なりヨセフ彼處にて獄にをりしが
21 Ubangiji ya kasance tare da shi; ya nuna masa alheri, ya kuma sa ya sami tagomashi a idanun mai gadin kurkukun.
ヱホバ、ヨセフとともに在して之に仁慈を加へ典獄の恩顧をこれにえさせたまひければ
22 Saboda haka mai gadin ya sa Yusuf ya zama shugaban dukan waɗanda aka tsare a kurkukun, Yusuf ne kuma yake lura da dukan abin da ake yi a can.
典獄獄にある囚人をことごとくヨセフの手に付せたり其處になす所の事は皆ヨセフこれをなすなり
23 Mai gadin ba ya sa kansa game da kome da yake ƙarƙashin kulawar Yusuf, gama Ubangiji yana tare da Yusuf, ya kuma ba shi nasara a cikin dukan abin da ya yi.
典獄そのまかせたる所の事は何をもかへりみざりき其はヱホバ、ヨセフとともにいませばなりヱホバかれのなすところをさかえしめたまふ