< Farawa 37 >

1 Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.
雅各住在迦南地,就是他父親寄居的地。
2 Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub. Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da’yan’uwansa, wato,’ya’yan Bilha maza da kuma’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da’yan’uwansa.
雅各的記略如下。 約瑟十七歲與他哥哥們一同牧羊。他是個童子,與他父親的妾辟拉、悉帕的兒子們常在一處。約瑟將他哥哥們的惡行報給他們的父親。
3 Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.
以色列原來愛約瑟過於愛他的眾子,因為約瑟是他年老生的;他給約瑟做了一件彩衣。
4 Sa’ad da’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
約瑟的哥哥們見父親愛約瑟過於愛他們,就恨約瑟,不與他說和睦的話。
5 Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
約瑟做了一夢,告訴他哥哥們,他們就越發恨他。
6 Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi.
約瑟對他們說:「請聽我所做的夢:
7 Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
我們在田裏捆禾稼,我的捆起來站着,你們的捆來圍着我的捆下拜。」
8 Sai’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
他的哥哥們回答說:「難道你真要作我們的王嗎?難道你真要管轄我們嗎?」他們就因為他的夢和他的話越發恨他。
9 Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
後來他又做了一夢,也告訴他的哥哥們說:「看哪,我又做了一夢,夢見太陽、月亮,與十一個星向我下拜。」
10 Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?”
約瑟將這夢告訴他父親和他哥哥們,他父親就責備他說:「你做的這是甚麼夢!難道我和你母親、你弟兄果然要來俯伏在地,向你下拜嗎?」
11 ’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
他哥哥們都嫉妒他,他父親卻把這話存在心裏。
12 To,’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem.
約瑟的哥哥們往示劍去放他們父親的羊。
13 Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani,’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.” Ya ce, “To.”
以色列對約瑟說:「你哥哥們不是在示劍放羊嗎?你來,我要打發你往他們那裏去。」約瑟說:「我在這裏。」
14 Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron. Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem,
以色列說:「你去看看你哥哥們平安不平安,群羊平安不平安,就回來報信給我」;於是打發他出希伯崙谷,他就往示劍去了。
15 sai wani mutum ya same shi yana yawo a cikin jeji, sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
有人遇見他在田野走迷了路,就問他說:「你找甚麼?」
16 Yusuf ya amsa ya ce, “Ina neman’yan’uwana ne. Za ka iya faɗa mini inda suke kiwon garkunansu?”
他說:「我找我的哥哥們,求你告訴我,他們在何處放羊。」
17 Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’” Saboda haka Yusuf ya bi bayan’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan.
那人說:「他們已經走了,我聽見他們說要往多坍去。」約瑟就去追趕他哥哥們,遇見他們在多坍。
18 Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.
他們遠遠地看見他,趁他還沒有走到跟前,大家就同謀要害死他,
19 Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa!
彼此說:「你看!那做夢的來了。
20 Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
來吧!我們將他殺了,丟在一個坑裏,就說有惡獸把他吃了。我們且看他的夢將來怎麼樣。」
21 Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa.
呂便聽見了,要救他脫離他們的手,說:「我們不可害他的性命」;
22 Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
又說:「不可流他的血,可以把他丟在這野地的坑裏,不可下手害他。」呂便的意思是要救他脫離他們的手,把他歸還他的父親。
23 Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa,
約瑟到了他哥哥們那裏,他們就剝了他的外衣,就是他穿的那件彩衣,
24 suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
把他丟在坑裏;那坑是空的,裏頭沒有水。
25 Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
他們坐下吃飯,舉目觀看,見有一夥米甸 的以實瑪利人從基列來,用駱駝馱着香料、乳香、沒藥,要帶下埃及去。
26 Yahuda ya ce wa’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa?
猶大對眾弟兄說:「我們殺我們的兄弟,藏了他的血有甚麼益處呢?
27 Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai’yan’uwansa suka yarda.
我們不如將他賣給以實瑪利人,不可下手害他;因為他是我們的兄弟,我們的骨肉。」眾弟兄就聽從了他。
28 Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
有些米甸的商人從那裏經過,哥哥們就把約瑟從坑裏拉上來,講定二十舍客勒銀子,把約瑟賣給以實瑪利人。他們就把約瑟帶到埃及去了。
29 Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa.
呂便回到坑邊,見約瑟不在坑裏,就撕裂衣服,
30 Ya koma wurin’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”
回到兄弟們那裏,說:「童子沒有了。我往哪裏去才好呢?」
31 Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin.
他們宰了一隻公山羊,把約瑟的那件彩衣染了血,
32 Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”
打發人送到他們的父親那裏,說:「我們撿了這個;請認一認是你兒子的外衣不是?」
33 Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
他認得,就說:「這是我兒子的外衣。有惡獸把他吃了,約瑟被撕碎了!撕碎了!」
34 Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa.
雅各便撕裂衣服,腰間圍上麻布,為他兒子悲哀了多日。
35 Dukan’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi. (Sheol h7585)
他的兒女都起來安慰他,他卻不肯受安慰,說:「我必悲哀着下陰間,到我兒子那裏。」約瑟的父親就為他哀哭。 (Sheol h7585)
36 Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin’yan gadin fadar Fir’auna.
米甸人帶約瑟到埃及,把他賣給法老的內臣-護衛長波提乏。

< Farawa 37 >