< Farawa 35 >

1 Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”
ויאמר אלהים אל יעקב קום עלה בית אל ושב שם ועשה שם מזבח--לאל הנראה אליך בברחך מפני עשו אחיך
2 Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku.
ויאמר יעקב אל ביתו ואל כל אשר עמו הסרו את אלהי הנכר אשר בתככם והטהרו והחליפו שמלתיכם
3 Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.”
ונקומה ונעלה בית אל ואעשה שם מזבח לאל הענה אתי ביום צרתי ויהי עמדי בדרך אשר הלכתי
4 Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem.
ויתנו אל יעקב את כל אלהי הנכר אשר בידם ואת הנזמים אשר באזניהם ויטמן אתם יעקב תחת האלה אשר עם שכם
5 Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.
ויסעו ויהי חתת אלהים על הערים אשר סביבותיהם ולא רדפו אחרי בני יעקב
6 Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana.
ויבא יעקב לוזה אשר בארץ כנען--הוא בית אל הוא וכל העם אשר עמו
7 A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel, gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.
ויבן שם מזבח ויקרא למקום אל בית אל כי שם נגלו אליו האלהים בברחו מפני אחיו
8 To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.
ותמת דברה מינקת רבקה ותקבר מתחת לבית אל תחת האלון ויקרא שמו אלון בכות
9 Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram, sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi.
וירא אלהים אל יעקב עוד בבאו מפדן ארם ויברך אתו
10 Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.” Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.
ויאמר לו אלהים שמך יעקב לא יקרא שמך עוד יעקב כי אם ישראל יהיה שמך ויקרא את שמו ישראל
11 Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.
ויאמר לו אלהים אני אל שדי פרה ורבה--גוי וקהל גוים יהיה ממך ומלכים מחלציך יצאו
12 Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.”
ואת הארץ אשר נתתי לאברהם וליצחק--לך אתננה ולזרעך אחריך אתן את הארץ
13 Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.
ויעל מעליו אלהים במקום אשר דבר אתו
14 Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa.
ויצב יעקב מצבה במקום אשר דבר אתו--מצבת אבן ויסך עליה נסך ויצק עליה שמן
15 Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.
ויקרא יעקב את שם המקום אשר דבר אתו שם אלהים--בית אל
16 Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai.
ויסעו מבית אל ויהי עוד כברת הארץ לבוא אפרתה ותלד רחל ותקש בלדתה
17 Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.”
ויהי בהקשתה בלדתה ותאמר לה המילדת אל תיראי כי גם זה לך בן
18 Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.
ויהי בצאת נפשה כי מתה ותקרא שמו בן אוני ואביו קרא לו בנימין
19 Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem).
ותמת רחל ותקבר בדרך אפרתה הוא בית לחם
20 Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
ויצב יעקב מצבה על קברתה--הוא מצבת קברת רחל עד היום
21 Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder.
ויסע ישראל ויט אהלה מהלאה למגדל עדר
22 Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari. Yaƙub ya haifi’ya’ya maza goma sha biyu.
ויהי בשכן ישראל בארץ ההוא וילך ראובן וישכב את בלהה פילגש אביו וישמע ישראל ויהיו בני יעקב שנים עשר
23 ’Ya’yan Liyatu maza, Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub. Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.
בני לאה בכור יעקב ראובן ושמעון ולוי ויהודה ויששכר וזבלון
24 ’Ya’yan Rahila maza su ne, Yusuf da Benyamin.
בני רחל יוסף ובנימן
25 ’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne, Dan da Naftali.
ובני בלהה שפחת רחל דן ונפתלי
26 ’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne, Gad da Asher. Waɗannan su ne’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.
ובני זלפה שפחת לאה גד ואשר אלה בני יעקב אשר ילד לו בפדן ארם
27 Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna.
ויבא יעקב אל יצחק אביו ממרא קרית הארבע--הוא חברון אשר גר שם אברהם ויצחק
28 Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin,
ויהיו ימי יצחק--מאת שנה ושמנים שנה
29 sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru.’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.
ויגוע יצחק וימת ויאסף אל עמיו זקן ושבע ימים ויקברו אתו עשו ויעקב בניו

< Farawa 35 >