< Farawa 32 >
1 Yaƙub shi ma ya kama hanyarsa, sai mala’ikun Allah suka sadu da shi.
茲にヤコブその途に進みしが神の使者これにあふ
2 Sa’ad da Yaƙub ya gan su sai ya ce, “Wannan sansanin Allah ne!” Saboda haka ya kira wannan wuri Mahanayim.
ヤコブこれを見て是は神の陣營なりといひてその處の名をマハナイム(二營)となづけたり
3 Sai Yaƙub ya aiki manzanni su sha gabansa zuwa wurin ɗan’uwansa Isuwa a ƙasar Seyir, a ƙauyen Edom.
かくてヤコブ己より前に使者をつかはしてセイルの地エドムの野にをる其兄エサウの所にいたらしむ
4 Ya umarce su, “Ga abin da za ku faɗa wa maigidana Isuwa, ‘Bawanka Yaƙub ya ce, na yi zama tare da Laban na kuwa kasance a can sai yanzu.
即ち之に命じて言ふ汝等かくわが主エサウにいふべし汝の僕ヤコブ斯いふ我ラバンの所に寄寓て今までとどまれり
5 Ina da shanu da jakuna, tumaki da awaki, bayi maza da mata. Yanzu ina aika da wannan saƙo zuwa ga ranka yă daɗe, don in sami tagomashi a idanunka.’”
我牛驢馬羊僕婢あり人をつかはしてわが主に告ぐ汝の前に恩をえんことを願ふなりと
6 Sa’ad da manzannin suka komo wurin Yaƙub, suka ce, “Mun tafi wurin ɗan’uwanka Isuwa, yanzu kuwa yana zuwa ya sadu da kai, da kuma mutum ɗari huɗu tare da shi.”
使者ヤコブにかへりて言けるは我等汝の兄エサウの許に至れり彼四百人をしたがへて汝をむかへんとて來ると
7 Da tsoro mai yawa da kuma damuwa, Yaƙub ya rarraba mutanen da suke tare da shi ƙungiyoyi biyu, haka ma garkunan tumaki da awaki, da garkunan shanu da raƙuma.
是によりヤコブ大におそれ且くるしみ己とともにある人衆および羊と牛と駱駝を二隊にわかちて
8 Ya yi tunani, “In Isuwa ya zo ya fāɗa wa ƙungiya ɗaya, sai ƙungiya ɗayan da ta ragu ta tsira.”
言けるはエサウもし一の隊に來りて之をうたば遺れるところの一隊逃るべし
9 Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
ヤコブまた言けるはわが父アブラハムの神わが父イサクの神ヱホバよ汝嘗て我につげて汝の國にかへり汝の親族に到れ我なんぢを善せんといひたまへり
10 Ban cancanci dukan alheri da amincin da ka nuna wa bawanka ba. Da sanda kaɗai nake sa’ad da na ƙetare wannan Urdun, amma ga shi yanzu na zama ƙungiyoyi biyu.
我はなんぢが僕にほどこしたまひし恩恵と眞實を一も受るにたらざるなり我わが杖のみを持てこのヨルダンを濟りしが今は二隊とも成にいたれり
11 Ka cece ni, ina roƙonka daga hannun ɗan’uwana Isuwa, gama ina tsoro zai zo yă fāɗa mini, yă karkashe mu duka,’ya’ya da iyaye.
願くはわが兄の手よりエサウの手より我をすくひいだしたまへ我彼をおそる恐くは彼きたりて我をうち母と子とに及ばん
12 Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’”
汝は嘗て我かならず汝を惠み汝の子孫を濱の沙の多して數ふべからざるが如くなさんといひたまへりと
13 Ya kwana a can, daga cikin abin da yake tare da shi kuwa, ya zaɓi kyauta domin ɗan’uwansa Isuwa,
彼その夜彼處に宿りその手にいりし物の中より兄エサウへの禮物をえらべり
14 awaki ɗari biyu da bunsurai ashirin, tumaki ɗari biyu da raguna ashirin,
即ち牝山羊二百牡山羊二十牝羊二百牡羊二十
15 raƙuma mata talatin tare da ƙananansu, shanu arba’in da bijimai goma, jakuna mata ashirin da kuma jakuna maza goma.
乳駱駝と其子三十牝牛四十牡牛十牝の驢馬二十驢馬の子十
16 Ya sa su a ƙarƙashin kulawar bayinsa, kowane kashin garke ya kasance a ware. Ya ce wa bayinsa, “Ku sha gabana, ku kuma ba da rata tsakanin garke da garke.”
而して其群と群とをわかちて之を僕の手に授し僕にいひけるは吾に先ちて進み群と群との間を隔ておくべし
17 Ya umarci wanda yake jagorar ya ce, “Sa’ad da ɗan’uwana Isuwa ya sadu da ku ya kuma yi tambaya, ‘Ku na wane ne, ina za ku, kuma wane ne mai dukan dabbobin nan da suke gabanku?’
又その前者に命じて言けるはわが兄エサウ汝にあひ汝に問て汝は誰の人にして何處にゆくや是汝のまへなる者は誰の所有なるやといはば
18 Sai ku ce, ‘Na bawanka Yaƙub ne. Kyauta ce wa maigidana Isuwa, yana kuma tafe a bayanmu.’”
汝の僕ヤコブの所有にしてわが主エサウにたてまつる禮物なり視よ彼もわれらの後にをるといふべしと
19 Yaƙub ya kuma umarci na biyu da na uku da kuma dukan waɗansu da suka bi garkunan, “Sai ku faɗa irin abu guda ga Isuwa sa’ad da kuka sadu da shi.
彼かく第二の者第三の者および凡て群々にしたがひゆく者に命じていふ汝等エサウにあふ時はかくの如く之にいふべし
20 Ku kuma tabbata kun ce, ‘Bawanka Yaƙub yana tafe a bayanmu.’” Gama Yaƙub ya yi tunani cewa, “Zan kwantar da ran Isuwa da waɗannan kyautai, kafin mu sadu fuska da fuska, wataƙila yă karɓe shi.”
且汝等いへ視よなんぢの僕ヤコブわれらの後にをるとヤコブおもへらく我わが前におくる禮物をもて彼を和めて然るのち其面を觀ん然ば彼われを接遇ることあらんと
21 Saboda haka kyautai Yaƙub suka sha gabansa, amma shi kansa ya kwana a sansani.
是によりて禮物かれに先ちて行く彼は其夜陣營の中に宿りしが
22 A wannan dare Yaƙub ya tashi ya ɗauki matansa biyu, da matan nan biyu masu hidima da’ya’yansa goma sha ɗaya ya haye rafin Yabbok.
其夜おきいでて二人の妻と二人の仕女および十一人の子を導きてヤボクの渡をわたれり
23 Bayan ya sa suka haye rafin, haka ma ya tura dukan mallakarsa zuwa hayen.
即ち彼等をみちびきて川を渉らしめ又その有る物を渡せり
24 Saboda haka sai aka bar Yaƙub shi kaɗai. Sai ga wani mutum ya zo ya yi kokawa da shi har wayewar gari.
而してヤコブ一人遺りしが人ありて夜の明るまで之と角力す
25 Da mutumin ya ga cewa bai fi ƙarfin Yaƙub ba, sai ya bugi kwarin ƙashin cinyar Yaƙub, sai gaɓar ƙashin cinyarsa ya goce, a sa’ad da yake kokawa da mutumin.
其人己のヤコブに勝ざるを見てヤコブの髀の樞骨に觸しかばヤコブの髀の樞骨其人と角力する時挫離たり
26 Sa’an nan mutumin ya ce, “Bar ni in tafi, gama gari ya waye.” Amma Yaƙub ya amsa ya ce, “Ba zan bar ka ka tafi ba, sai ka sa mini albarka.”
其人夜明んとすれば我をさらしめよといひければヤコブいふ汝われを祝せずばさらしめずと
27 Mutumin ya tambaye shi ya ce, “Mene ne sunanka?” Yaƙub ya amsa ya ce, “Yaƙub.”
是に於て其人かれにいふ汝の名は何なるや彼いふヤコブなり
28 Sai mutumin ya ce, “Sunanka ba zai ƙara zama Yaƙub ba, amma Isra’ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”
其人いひけるは汝の名は重てヤコブととなふべからずイスラエルととなふべし其は汝神と人とに力をあらそひて勝たればなりと
29 Yaƙub ya ce, “Ina roƙonka, faɗa mini sunanka.” Amma mutumin ya amsa ya ce, “Me ya sa kake tambayata sunana?” Sa’an nan ya albarkace shi.
ヤコブ問て請ふ汝の名を告よといひければ其人何故にわが名をとふやといひて乃ち其處にて之を祝せり
30 Saboda haka Yaƙub ya kira wurin Feniyel, yana cewa, “Domin na ga Allah fuska da fuska, duk da haka aka bar ni da rai.”
是を以てヤコブその處の名をベニエル(神の面)となづけて曰ふ我面と面をあはせて神とあひ見てわが生命なほ存るなりと
31 Rana ta yi sama a sa’ad da ya wuce Fenuwel yana kuma ɗingishi saboda ƙashin cinyarsa.
斯て彼日のいづる時にベニエルを過たりしが其髀のために歩行はかどらざりき
32 Wannan ya sa har wa yau Isra’ilawa ba sa cin jijiyar ƙashin cinya wadda take a kwarin ƙashin cinya, domin an taɓa kwarin ƙashin cinyar Yaƙub kusa da jijiyar.
是故にイスラエルの子孫は今日にいたるまで髀の樞の巨筋を食はず是彼人がヤコブの髀の巨筋に觸たるによりてなり