< Farawa 29 >

1 Sa’an nan Yaƙub ya ci gaba da tafiyarsa har ya kai ƙasar mutanen gabashi.
וישא יעקב רגליו וילך ארצה בני קדם
2 A can ya ga rijiya a jeji da garkuna uku na tumaki kwance kusa da ita, gama a wannan rijiya ce ake shayar da garkuna. Dutsen da ake rufe bakin rijiyar mai girma ne.
וירא והנה באר בשדה והנה שם שלשה עדרי צאן רבצים עליה--כי מן הבאר ההוא ישקו העדרים והאבן גדלה על פי הבאר
3 Sa’ad da dukan garkuna suka taru a can, sai makiyayan su gungurar da dutsen daga bakin rijiyar su shayar da tumaki. Sa’an nan su mai da dutsen a wurinsa a bakin rijiya.
ונאספו שמה כל העדרים וגללו את האבן מעל פי הבאר והשקו את הצאן והשיבו את האבן על פי הבאר למקמה
4 Yaƙub ya tambayi makiyayan ya ce, “’Yan’uwa, ina kuka fito?” Suka amsa, “Mu daga Haran ne.”
ויאמר להם יעקב אחי מאין אתם ויאמרו מחרן אנחנו
5 Sai ya ce musu, “Kun san Laban, jikan Nahor?” Suka amsa, “I, mun san shi.”
ויאמר להם הידעתם את לבן בן נחור ויאמרו ידענו
6 Sa’an nan Yaƙub ya tambaye su, “Yana nan lafiya?” Suka ce, “I, yana lafiya, ga ma’yarsa Rahila tafe da tumaki.”
ויאמר להם השלום לו ויאמרו שלום--והנה רחל בתו באה עם הצאן
7 Ya ce, “Duba har yanzu da sauran rana da yawa, lokaci bai kai na tara garkuna ba. Ku shayar da tumaki ku mai da su wurin kiwo.”
ויאמר הן עוד היום גדול--לא עת האסף המקנה השקו הצאן ולכו רעו
8 Suka amsa suka ce, “Ba za mu iya ba, sai dukan garkunan sun taru, aka kuma gungurar da dutsen daga bakin rijiyar. Sa’an nan za mu shayar da tumakin.”
ויאמרו לא נוכל עד אשר יאספו כל העדרים וגללו את האבן מעל פי הבאר והשקינו הצאן
9 Tun yana cikin magana da su, sai ga Rahila ta zo da tumakin mahaifinta, gama ita makiyayyiya ce.
עודנו מדבר עמם ורחל באה עם הצאן אשר לאביה--כי רעה הוא
10 Sa’ad da Yaƙub ya ga Rahila’yar Laban, ɗan’uwan mahaifiyarsa, da tumakin Laban, sai ya tafi ya gungurar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma shayar da tumakin kawunsa.
ויהי כאשר ראה יעקב את רחל בת לבן אחי אמו ואת צאן לבן אחי אמו ויגש יעקב ויגל את האבן מעל פי הבאר וישק את צאן לבן אחי אמו
11 Sa’an nan Yaƙub ya sumbaci Rahila, ya kuma ɗaga murya ya yi kuka.
וישק יעקב לרחל וישא את קלו ויבך
12 Ya riga ya faɗa wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne kuma ɗan Rebeka. Saboda haka ta ruga da gudu ta faɗa wa mahaifinta.
ויגד יעקב לרחל כי אחי אביה הוא וכי בן רבקה הוא ותרץ ותגד לאביה
13 Nan da nan, da Laban ya sami labari game da Yaƙub, ɗan’yar’uwarsa, ya gaggauta yă sadu da shi. Sai ya rungume shi ya sumbace shi, ya kuma kawo shi gidansa, a can kuwa Yaƙub ya faɗa masa dukan waɗannan abubuwa.
ויהי כשמע לבן את שמע יעקב בן אחתו וירץ לקראתו ויחבק לו וינשק לו ויביאהו אל ביתו ויספר ללבן את כל הדברים האלה
14 Sa’an nan Laban ya ce masa, “Kai nama da jinina ne.” Bayan Yaƙub ya zauna da shi na wata guda cif,
ויאמר לו לבן אך עצמי ובשרי אתה וישב עמו חדש ימים
15 sai Laban ya ce masa, “Don kawai kai dangina ne na kusa, sai kawai ka yi mini aiki a banza? Faɗa mini abin da albashinka zai zama.”
ויאמר לבן ליעקב הכי אחי אתה ועבדתני חנם הגידה לי מה משכרתך
16 Laban dai yana da’ya’ya mata biyu; sunan babbar Liyatu, sunan ƙaramar kuwa Rahila.
וללבן שתי בנות שם הגדלה לאה ושם הקטנה רחל
17 Liyatu tana da raunannun idanu, amma Rahila dai tsarinta yana da kyau kuma kyakkyawa ce.
ועיני לאה רכות ורחל היתה יפת תאר ויפת מראה
18 Yaƙub ya ƙaunaci Rahila, sai ya ce, “Zan yi maka aiki na shekaru bakwai domin ƙaramar’yarka Rahila.”
ויאהב יעקב את רחל ויאמר אעבדך שבע שנים ברחל בתך הקטנה
19 Laban ya ce, “Ya fi kyau in ba ka ita, da in ba wani mutum dabam. Zauna tare da ni.”
ויאמר לבן טוב תתי אתה לך מתתי אתה לאיש אחר שבה עמדי
20 Saboda haka Yaƙub ya yi bauta shekaru bakwai domin a ba shi Rahila, amma shekarun suka zama kamar’yan kwanaki ne kawai gare shi saboda ƙaunar da yake mata.
ויעבד יעקב ברחל שבע שנים ויהיו בעיניו כימים אחדים באהבתו אתה
21 Sa’an nan Yaƙub ya ce wa Laban, “Ba ni matata. Lokacina ya cika, ina kuma so in kwana da ita.”
ויאמר יעקב אל לבן הבה את אשתי כי מלאו ימי ואבואה אליה
22 Saboda haka Laban ya tara dukan mutanen wurin, ya yi biki.
ויאסף לבן את כל אנשי המקום ויעש משתה
23 Amma da yamma ta yi, sai ya ɗauki’yarsa Liyatu ya ba da ita ga Yaƙub, sai Yaƙub ya kwana da ita.
ויהי בערב--ויקח את לאה בתו ויבא אתה אליו ויבא אליה
24 Laban kuma ya ba da baranyarsa Zilfa wa’yarsa tă zama mai hidimarta.
ויתן לבן לה את זלפה שפחתו--ללאה בתו שפחה
25 Sa’ad da safiya ta yi, sai ga Liyatu! Saboda haka Yaƙub ya ce wa Laban, “Mene ne ke nan ka yi mini? Na yi maka bauta domin Rahila, ba haka na yi ba? Don me ka ruɗe ni?”
ויהי בבקר והנה הוא לאה ויאמר אל לבן מה זאת עשית לי--הלא ברחל עבדתי עמך ולמה רמיתני
26 Laban ya amsa, “Ba al’adarmu ba ce a nan a ba da’ya ƙarama aure kafin’yar fari.
ויאמר לבן לא יעשה כן במקומנו--לתת הצעירה לפני הבכירה
27 Ka gama makon amaryanci na’yar nan; sa’an nan za mu ba ka ƙaramar ita ma, don ƙarin waɗansu shekaru bakwai na aiki.”
מלא שבע זאת ונתנה לך גם את זאת בעבדה אשר תעבד עמדי עוד שבע שנים אחרות
28 Haka kuwa Yaƙub ya yi. Ya gama mako guda da Liyatu, sa’an nan Laban ya ba shi’yarsa Rahila tă zama matarsa.
ויעש יעקב כן וימלא שבע זאת ויתן לו את רחל בתו לו לאשה
29 Laban ya ba da baranyarsa Bilha wa’yarsa Rahila ta zama mai hidimarta.
ויתן לבן לרחל בתו את בלהה שפחתו--לה לשפחה
30 Yaƙub ya kwana da Rahila ita ma, ya kuwa ƙaunaci Rahila fiye da Liyatu. Ya kuma yi wa Laban aiki na ƙarin waɗansu shekaru bakwai.
ויבא גם אל רחל ויאהב גם את רחל מלאה ויעבד עמו עוד שבע שנים אחרות
31 Sa’ad da Ubangiji ya ga ba a ƙaunar Liyatu, sai ya buɗe mahaifarta, amma Rahila ta zama bakararriya.
וירא יהוה כי שנואה לאה ויפתח את רחמה ורחל עקרה
32 Sai Liyatu ta yi ciki ta haifi ɗa. Ta sa masa suna Ruben, gama ta ce, “Domin Ubangiji ya ga wahalata. Tabbatacce mijina zai ƙaunace ni yanzu.”
ותהר לאה ותלד בן ותקרא שמו ראובן כי אמרה כי ראה יהוה בעניי--כי עתה יאהבני אישי
33 Ta sāke yin ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Gama Ubangiji ya ji cewa ba a ƙaunata, ya ba ni wannan shi ma.” Saboda haka ta ba shi suna Simeyon.
ותהר עוד ותלד בן ותאמר כי שמע יהוה כי שנואה אנכי ויתן לי גם את זה ותקרא שמו שמעון
34 Har yanzu ta yi ciki, sa’ad da kuma ta haifi ɗa sai ta ce, “Yanzu, a ƙarshe mijina zai manne mini, gama na haifa masa’ya’ya maza uku.” Saboda haka ta ba shi suna Lawi.
ותהר עוד ותלד בן ותאמר עתה הפעם ילוה אישי אלי כי ילדתי לו שלשה בנים על כן קרא שמו לוי
35 Ta sāke yin ciki, sa’ad da ta haifi ɗa sai ta ce, “A wannan lokaci zan yabi Ubangiji.” Saboda haka ta ba shi suna Yahuda. Sa’an nan ta daina haihuwa.
ותהר עוד ותלד בן ותאמר הפעם אודה את יהוה--על כן קראה שמו יהודה ותעמד מלדת

< Farawa 29 >