< Farawa 25 >

1 Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura.
ויסף אברהם ויקח אשה ושמה קטורה
2 Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.
ותלד לו את זמרן ואת יקשן ואת מדן ואת מדין--ואת ישבק ואת שוח
3 Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin.
ויקשן ילד את שבא ואת דדן ובני דדן היו אשורם ולטושם ולאמים
4 ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.
ובני מדין עיפה ועפר וחנך ואבידע ואלדעה כל אלה בני קטורה
5 Ibrahim ya bar wa Ishaku kome da ya mallaka.
ויתן אברהם את כל אשר לו ליצחק
6 Amma yayinda Ibrahim yake da rai, ya ba wa’ya’yan ƙwarƙwaransa maza kyautai, ya kuma sallame su daga ɗansa Ishaku zuwa ƙasashen gabas.
ולבני הפילגשים אשר לאברהם נתן אברהם מתנת וישלחם מעל יצחק בנו בעודנו חי קדמה אל ארץ קדם
7 Duka-duka, Ibrahim ya yi shekara ɗari da saba’in da biyar.
ואלה ימי שני חיי אברהם--אשר חי מאת שנה ושבעים שנה וחמש שנים
8 Sa’an nan Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu da kyakkyawar tsufa, tsoho da kuma shekaru masu yawa; aka kuma tara shi ga mutanensa.
ויגוע וימת אברהם בשיבה טובה זקן ושבע ויאסף אל עמיו
9 ’Ya’yansa maza kuwa Ishaku da Ishmayel suka binne shi cikin kogon Makfela, kusa da Mamre, a cikin filin Efron ɗan Zohar mutumin Hitti,
ויקברו אתו יצחק וישמעאל בניו אל מערת המכפלה אל שדה עפרן בן צחר החתי אשר על פני ממרא
10 filin da Ibrahim ya saya daga Hittiyawa. A nan aka binne Ibrahim tare da matarsa Saratu.
השדה אשר קנה אברהם מאת בני חת--שמה קבר אברהם ושרה אשתו
11 Bayan rasuwar Ibrahim, Allah ya albarkaci ɗansa Ishaku wanda a lokacin yana zama kusa da Beyer-Lahai-Royi.
ויהי אחרי מות אברהם ויברך אלהים את יצחק בנו וישב יצחק עם באר לחי ראי
12 Waɗannan su ne zuriyar Ishmayel ɗan Ibrahim, wanda Hagar mutuniyar Masar, baranyar Saratu, ta haifa wa Ibrahim.
ואלה תלדת ישמעאל בן אברהם אשר ילדה הגר המצרית שפחת שרה--לאברהם
13 Ga jerin sunayen’ya’yan Ishmayel maza bisa ga haihuwarsu, Nebayiwot ɗan farin Ishmayel, Kedar, Adbeyel, Mibsam,
ואלה שמות בני ישמעאל בשמתם לתולדתם בכר ישמעאל נבית וקדר ואדבאל ומבשם
14 Mishma, Duma, Massa,
ומשמע ודומה ומשא
15 Hadad, Tema, Yetur, Nafish da Kedema.
חדד ותימא יטור נפיש וקדמה
16 Waɗannan su ne’ya’yan Ishmayel maza, waɗanda kuma suke sunayen kabilu goma sha biyu masu mulki bisa ga wuraren zamansu da sansaninsu.
אלה הם בני ישמעאל ואלה שמתם בחצריהם ובטירתם--שנים עשר נשיאם לאמתם
17 Duka-duka Ishmayel ya yi shekara ɗari da talatin da bakwai; sai ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuma mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa.
ואלה שני חיי ישמעאל--מאת שנה ושלשים שנה ושבע שנים ויגוע וימת ויאסף אל עמיו
18 Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran’yan’uwansu.
וישכנו מחוילה עד שור אשר על פני מצרים באכה אשורה על פני כל אחיו נפל
19 Waɗannan su ne zuriyar Ishaku ɗan Ibrahim. Ibrahim ya haifi Ishaku,
ואלה תולדת יצחק בן אברהם אברהם הוליד את יצחק
20 Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram,’yar’uwar Laban mutumin Aram.
ויהי יצחק בן ארבעים שנה בקחתו את רבקה בת בתואל הארמי מפדן ארם--אחות לבן הארמי לו לאשה
21 Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.
ויעתר יצחק ליהוה לנכח אשתו כי עקרה הוא ויעתר לו יהוה ותהר רבקה אשתו
22 Jariran suka kama kokawa da juna a cikinta, sai ta ce, “Me ya sa wannan yake faruwa da ni?” Saboda haka ta tafi don ta nemi nufin Ubangiji.
ויתרצצו הבנים בקרבה ותאמר אם כן למה זה אנכי ותלך לדרש את יהוה
23 Ubangiji ya ce mata, “Al’ummai biyu suna a cikin mahaifarki mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban kuma zai bauta wa ƙaramin.”
ויאמר יהוה לה שני גיים (גוים) בבטנך ושני לאמים ממעיך יפרדו ולאם מלאם יאמץ ורב יעבד צעיר
24 Da lokaci ya yi da za tă haihu, sai ga’yan biyu maza a mahaifarta.
וימלאו ימיה ללדת והנה תומם בבטנה
25 Wanda ya fara fita ja ne, dukan jikinsa kuwa kamar riga mai gashi. Don haka aka sa masa suna Isuwa.
ויצא הראשון אדמוני כלו כאדרת שער ויקראו שמו עשו
26 Bayan wannan, ɗan’uwansa ya fito, da hannunsa yana riƙe da ɗiɗɗigen Isuwa; don haka aka sa masa suna Yaƙub. Ishaku yana da shekara sittin, lokacin da Rebeka ta haife su.
ואחרי כן יצא אחיו וידו אחזת בעקב עשו ויקרא שמו יעקב ויצחק בן ששים שנה בלדת אתם
27 Yaran suka yi girma, Isuwa kuwa ya zama riƙaƙƙen maharbi, mutumin jeji, yayinda Yaƙub, shiru-shiru ne mai son zama a tentuna.
ויגדלו הנערים ויהי עשו איש ידע ציד איש שדה ויעקב איש תם ישב אהלים
28 Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub.
ויאהב יצחק את עשו כי ציד בפיו ורבקה אהבת את יעקב
29 Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai.
ויזד יעקב נזיד ויבא עשו מן השדה והוא עיף
30 Ya ce wa Yaƙub, “Ina roƙonka, ka ɗan ɗiba mini faten nan! Ina fama da yunwa!” (Shi ya sa aka kira shi Edom.)
ויאמר עשו אל יעקב הלעיטני נא מן האדם האדם הזה--כי עיף אנכי על כן קרא שמו אדום
31 Yaƙub ya amsa ya ce, “Ka fara sayar mini da matsayinka na ɗan fari tukuna.”
ויאמר יעקב מכרה כיום את בכרתך לי
32 Isuwa ya ce, “Duba, ina gab da mutuwa, me matsayina na ɗan fari zai yi mini?”
ויאמר עשו הנה אנכי הולך למות ולמה זה לי בכרה
33 Amma Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini tukuna.” Don haka ya rantse masa, ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yaƙub.
ויאמר יעקב השבעה לי כיום וישבע לו וימכר את בכרתו ליעקב
34 Sa’an nan Yaƙub ya ba wa Isuwa burodi da ɗan miyan lansir. Ya ci, ya sha, sa’an nan ya tashi ya tafi. Ta haka Isuwa ya yi banza da matsayinsa na ɗan fari.
ויעקב נתן לעשו לחם ונזיד עדשים ויאכל וישת ויקם וילך ויבז עשו את הבכרה

< Farawa 25 >