< Farawa 24 >

1 Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya.
아브라함이 나이 많아 늙었고 여호와께서 그의 범사에 복을 주셨더라
2 Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata.
아브라함이 자기 집 모든 소유를 맡은 늙은 종에게 이르되 청컨대 네 손을 내 환도뼈 밑에 넣으라
3 Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba.
내가 너로 하늘의 하나님, 땅의 하나님이신 여호와를 가리켜 맹세하게 하노니 너는 나의 거하는 이 지방 가나안 족속의 딸 중에서 내 아들을 위하여 아내를 택하지 말고
4 Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
내 고향 내 족속에게로 가서 내 아들 이삭을 위하여 아내를 택하라
5 Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?”
종이 가로되 여자가 나를 좇아 이 땅으로 오고자 아니하거든 내가 주인의 아들을 주인의 나오신 땅으로 인도하여 돌아가리이까
6 Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.”
아브라함이 그에게 이르되 삼가 내 아들을 그리로 데리고 돌아가지 말라
7 Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can.
하늘의 하나님 여호와께서 나를 내 아버지의 집과 내 본토에서 떠나게 하시고 내게 말씀하시며 내게 맹세하여 이르시기를 이 땅을 네 씨에게 주리라 하셨으니 그가 그 사자를 네 앞서 보내실지라 네가 거기서 내 아들을 위하여 아내를 택할지니라
8 In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.”
만일 여자가 너를 좇아 오고자 아니하면 나의 이 맹세가 너와 상관이 없나니 오직 내 아들을 데리고 그리로 가지 말지니라
9 Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari.
종이 이에 주인 아브라함의 환도뼈 아래 손을 넣고 이 일에 대하여 그에게 맹세하였더라
10 Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.
이에 종이 그 주인의 약대 중 열 필을 취하고 떠났는데 곧 그 주인의 모든 좋은 것을 가지고 떠나 메소보다미아로 가서 나홀의 성에 이르러
11 Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
그 약대를 성 밖 우물 곁에 꿇렸으니 저녁때라 여인들이 물을 길러 나올 때이었더라
12 Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim.
그가 가로되 우리 주인 아브라함의 하나님 여호와여 원컨대 오늘날 나로 순적히 만나게 하사 나의 주인 아브라함에게 은혜를 베푸시옵소서
13 Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa,’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa.
성 중 사람의 딸들이 물 길러 나오겠사오니 내가 우물 곁에 섰다가
14 Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
한 소녀에게 이르기를 청컨대 너는 물 항아리를 기울여 나로 마시게 하라 하리니 그의 대답이 마시라 내가 당신의 약대에게도 마시우리라 하면 그는 주께서 주의 종 이삭을 위하여 정하신 자라 이로 인하여 주께서 나의 주인에게 은혜 베푸심을 내가 알겠나이다
15 Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.
말을 마치지 못하여서 리브가가 물 항아리를 어깨에 메고 나오니 그는 아브라함의 동생 나홀의 아내 밀가의 아들 브두엘의 소생이라
16 Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
그 소녀는 보기에 심히 아리땁고 지금까지 남자가 가까이 하지아니한 처녀더라 그가 우물에 내려가서 물을 그 물 항아리에 채워 가지고 올라오는지라
17 Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.”
종이 마주 달려가서 가로되 청컨대 네 물 항아리의 물을 내게 조금 마시우라
18 Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.
그가 가로되 주여 마시소서 하며 급히 그 물 항아리를 손에 내려 마시게 하고
19 Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.”
마시우기를 다하고 가로되 당신의 약대도 위하여 물을 길어 그것들로 배불리 마시게 하리이다 하고
20 Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa.
급히 물 항아리의 물을 구유에 붓고 다시 길으려고 우물로 달려가서 모든 약대를 위하여 긷는지라
21 Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu.
그 사람이 그를 묵묵히 주목하며 여호와께서 과연 평탄한 길을 주신 여부를 알고자 하더니
22 Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta.
약대가 마시기를 다하매 그가 반 세겔중 금고리 한개와 열 세겔 중 금 손목고리 한 쌍을 그에게 주며
23 Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?”
가로되 네가 뉘 딸이냐 청컨대 내게 고하라 네 부친의 집에 우리 유숙할 곳이 있느냐
24 Sai ta ce masa, “Ni’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.”
그 여자가 그에게 이르되 나는 밀가가 나홀에게 낳은 아들 브두엘의 딸이니이다
25 Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”
또 가로되 우리에게 짚과 보리가 족하며 유숙할 곳도 있나이다
26 Sa’an nan mutumin ya rusuna ya yi wa Ubangiji sujada,
이에 그 사람이 머리를 숙여 여호와께 경배하고
27 yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan’yan’uwan maigidana.”
가로되 나의 주인 아브라함의 하나님 여호와를 찬송하나이다 나의 주인에게 주의 인자와 성실을 끊이지 아니하셨사오며 여호와께서 길에서 나를 인도하사 내 주인의 동생집에 이르게 하셨나이다 하니라
28 Yariyan ta gudu ta faɗa wa mutanen gidan mahaifiyarta game da abubuwan nan.
소녀가 달려가서 이 일을 어미 집에 고하였더니
29 Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar.
리브가에게 오라비가 있어 이름은 라반이라 그가 우물로 달려가 그 사람에게 이르니
30 Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.
그가 그 누이의 고리와 그 손의 손목고리를 보고 또 그 누이 리브가가 그 사람이 자기에게 이같이 말하더라 함을 듣고 그 사람에게로 나아감이라 때에 그가 우물가 약대 곁에 섰더라
31 Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”
라반이 가로되 여호와께 복을 받은 자여 들어오소서 어찌 밖에 섰나이까 내가 방과 약대의 처소를 예비하였나이다
32 Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.
그 사람이 집으로 들어가매 라반이 약대의 짐을 부리고 짚과 보리를 약대에게 주고 그 사람의 발과 그 종자의 발 씻을 물을 주고
33 Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.”
그 앞에 식물을 베푸니 그 사람이 가로되 내가 내 일을 진술하기 전에는 먹지 아니하겠나이다 라반이 가로되 말하소서
34 Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne.
그가 가로되 나는 아브라함의 종이니이다
35 Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna.
여호와께서 나의 주인에게 크게 복을 주어 창성케 하시되 우양과 은금과 노비와 약대와 나귀를 그에게 주셨고
36 Saratu matar maigidana ta haifa masa ɗa a tsufanta, ya kuma ba shi duk mallakarsa.
나의 주인의 부인 사라가 노년에 나의 주인에게 아들을 낳으매 주인이 그 모든 소유를 그 아들에게 주었나이다
37 Maigidana ya sa na yi rantsuwa, ya kuma ce, ‘Kada ka ɗauko wa ɗana mata daga’ya’ya matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama a ƙasarsu,
나의 주인이 나로 맹세하게 하여 가로되 너는 내 아들을 위하여 나사는 땅 가나안 족속의 딸 중에서 아내를 택하지 말고
38 amma ka tafi wajen gidan mahaifina da kuma dangina, ka ɗauko wa ɗana mata.’
내 아비 집 내 족속에게로 가서 내 아들을 위하여 아내를 택하라 하시기로
39 “Sai na ce wa maigidana, ‘A ce matar ba tă yarda tă zo tare da ni ba fa?’
내가 내 주인에게 말씀하되 혹 여자가 나를 좇지 아니하면 어찌하리이까 한즉
40 “Maigidana ya ce, ‘Ubangiji wanda yake tare da ni zai aiki mala’ikansa tare da kai, yă kuma sa tafiyarka tă yi nasara, don ka samo wa ɗana mata daga dangina, daga kuma gidan mahaifina.
주인이 내게 이르되 나의 섬기는 여호와께서 그 사자를 너와 함께 보내어 네게 평탄한 길을 주시리니 너는 내 족속 중 내 아비 집에서 내 아들을 위하여 아내를 택할 것이니라
41 Ta haka za ka kuɓuta daga rantsuwata sa’ad da ka tafi wurin dangina, ko ma sun ƙi su ba ka ita, za ka kuɓuta daga rantsuwata.’
네가 내 족속에게 이를 때에는 네가 내 맹세와 상관이 없으리라 설혹 그들이 네게 주지 아니할지라도 네가 내 맹세와 상관이 없으리라 하시기로
42 “Sa’ad da na zo rijiya a yau, na ce, ‘Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ina roƙonka ka ba ni nasara a tafiyar da na yi.
내가 오늘 우물에 이르러 말씀하기를 나의 주인 아브라함의 하나님 여호와여 만일 나의 행하는 길에 형통함을 주실진대
43 Duba, ina tsaye kusa da wannan rijiya; in wata yarinya ta fito domin tă ɗiba ruwa, wadda in na ce mata, “Ina roƙonki bari in ɗan sha ruwa daga tulunki,”
내가 이 우물 곁에 섰다가 청년 여자가 물을 길러 오거든 내가 그에게 청하기를 너는 물 항아리의 물을 내게 조금 마시우라 하여
44 in ta ce, “Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma,” bari tă zama wadda Ubangiji ya zaɓar wa ɗan maigidana.’
그의 대답이 당신은 마시라 내가 또 당신의 약대를 위하여도 길으리라 하면 그 여자는 여호와께서 나의 주인의 아들을 위하여 정하여 주신 자가 되리이다 하며
45 “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’
내가 묵도하기를 마치지 못하여 리브가가 물 항아리를 어깨에 메고 나와서 우물로 내려와 긷기로 내가 그에게 이르기를 청컨대 내게 마시우라 한즉
46 “Ta yi sauri ta saukar da tulun daga kafaɗarta ta ce, ‘Sha, zan kuma ba wa raƙumanka su ma.’ Sai na sha, ta kuma shayar da raƙumana su ma.
그가 급히 물 항아리를 어깨에서 내리며 가로되 마시라 내가 당신의 약대에게도 마시우리라 하기로 내가 마시매 그가 또 약대에게도 마시운지라
47 “Na tambaye ta, ‘Ke’yar wane ne?’ “Ta ce, ‘’Yar Betuwel ɗan Nahor, wanda Milka ta haifa masa.’ “Sai na sa mata zobe a hancinta, woroworo kuma a hannuwata,
내가 그에게 묻기를 네가 뉘 딸이뇨 한즉 가로되 밀가가 나홀에게 낳은 브두엘의 딸이라 하기로 내가 고리를 그 코에 꿰고 손목고리를 그 손에 끼우고
48 na kuma sunkuya na yi wa Ubangiji sujada. Na yabi Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim wanda ya bi da ni a hanyar da take daidai, don in samo wa ɗan maigidana jikanyar ɗan’uwansa.
나의 주인 아브라함의 하나님 여호와께서 나를 바른 길로 인도하사 나의 주인의 동생의 딸을 그 아들을 위하여 택하게 하셨으므로 내가 머리를 숙여 그에게 경배하고 찬송하였나이다
49 Yanzu fa in za ku nuna wa maigidana alheri da aminci, ku faɗa mini, in kuma ba haka ba, ku faɗa mini, don in san hanyar da zan juya.”
이제 당신들이 인자와 진실로 나의 주인을 대접하려거든 내게 고하시고 그렇지 않을지라도 내게 고하여 나로 좌우간 행하게 하소서
50 Laban da Betuwel suka ce, “Wannan daga wurin Ubangiji ne, ba abin da za mu ce I, ko a’a ba.
라반과 브두엘이 대답하여 가로되 이 일이 여호와께로 말미암았으니 우리는 가부를 말할 수 없노라
51 Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
리브가가 그대 앞에 있으니 데리고 가서 여호와의 명대로 그로 그대의 주인의 아들의 아내가 되게 하라
52 Sa’ad da bawan Ibrahim ya ji abin da suka ce, sai ya rusuna har ƙasa a gaban Ubangiji.
아브라함의 종이 그들의 말을 듣고 땅에 엎드리어 여호와께 절하고
53 Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada.
은금 패물과 의복을 꺼내어 리브가에게 주고 그 오라비와 어미에게도 보물을 주니라
54 Sa’an nan shi da mutanen da suke tare da shi suka ci, suka sha, suka kuma kwana a can. Kashegari da safe da suka tashi sai ya ce, “A sallame ni in koma wurin maigidana.”
이에 그들 곧 종과 종자들이 먹고 마시고 유숙하고 아침에 일어나서 그가 가로되 나를 보내어 내 주인에게로 돌아가게 하소서
55 Amma ɗan’uwanta da mahaifiyarta suka ce, “Bari yarinyar ta ɗan zauna tare da mu kwana goma ko fiye, sa’an nan ka ta fi.”
리브가의 오라비와 그 어미가 가로되 소녀로 며칠을 적어도 열흘을 우리와 함께 있게 하라 그 후에 그가 갈 것이니라
56 Amma ya ce musu, “Kada ku tsai da ni, tun da Ubangiji ya ba ni nasara a tafiyata. Ku sallame ni domin in tafi wurin maigidana.”
그 사람이 그들에게 이르되 나를 만류치 마소서 여호와께서 내게 형통한 길을 주셨으니 나를 보내어 내 주인에게로 돌아가게 하소서
57 Sa’an nan suka ce, “Bari mu kira yarinyar mu tambaye ta game da zancen.”
그들이 가로되 우리가 소녀를 불러 그에게 물으리라 하고
58 Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.”
리브가를 불러 그에게 이르되 네가 이 사람과 함께 가려느냐 그가 대답하되 가겠나이다
59 Saboda haka suka sallame Rebeka,’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa.
그들이 그 누이 리브가와 그의 유모와 아브라함의 종과 종자들을 보내며
60 Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata, “’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar dubu dubbai, bari zuriyarki su mallaki ƙofofin abokan gābansu.”
리브가에게 축복하여 가로되 우리 누이여 너는 천만인의 어미가 될지어다 네 씨로 그 원수의 성문을 얻게 할지어다
61 Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.
리브가가 일어나 비자와 함께 약대를 타고 그 사람을 따라가니 종이 리브가를 데리고 가니라
62 Ishaku kuwa ya zo daga Beyer-Lahai-Royi, gama yana zama a Negeb.
때에 이삭이 브엘라해로이에서 왔으니 그가 남방에 거하였었음이라
63 Wata rana da yamma ya fita zuwa fili domin yă yi tunani, sa’ad da ya ɗaga ido, sai ya ga raƙuma suna zuwa.
이삭이 저물 때에 들에 나가 묵상하다가 눈을 들어 보매 약대들이 오더라
64 Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,
리브가가 눈을 들어 이삭을 바라보고 약대에서 내려
65 ta ce wa bawan, “Wane ne mutumin can a fili, da yake zuwa yă tarye mu?” Bawan ya ce, “Maigidana ne.” Saboda haka ta ɗauki mayafinta to rufe kanta.
종에게 말하되 들에서 배회하다가 우리에게로 마주 오는 자가 누구뇨 종이 가로되 이는 내 주인이니이다 리브가가 면박을 취하여 스스로 가리우더라
66 Sai bawan ya faɗa wa Ishaku duk abin da ya yi.
종이 그 행한 일을 다 이삭에게 고하매
67 Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.
이삭이 리브가를 인도하여 모친 사라의 장막으로 들이고 그를 취하여 아내를 삼고 사랑하였으니 이삭이 모친 상사 후에 위로를 얻었더라

< Farawa 24 >