< Farawa 22 >

1 Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
ויהי אחר הדברים האלה והאלהים נסה את אברהם ויאמר אליו אברהם ויאמר הנני
2 Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.”
ויאמר קח נא את בנך את יחידך אשר אהבת את יצחק ולך לך אל ארץ המריה והעלהו שם לעלה על אחד ההרים אשר אמר אליך
3 Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa.
וישכם אברהם בבקר ויחבש את חמרו ויקח את שני נעריו אתו ואת יצחק בנו ויבקע עצי עלה ויקם וילך אל המקום אשר אמר לו האלהים
4 A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa.
ביום השלישי וישא אברהם את עיניו וירא את המקום--מרחק
5 Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.”
ויאמר אברהם אל נעריו שבו לכם פה עם החמור ואני והנער נלכה עד כה ונשתחוה ונשובה אליכם
6 Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya,
ויקח אברהם את עצי העלה וישם על יצחק בנו ויקח בידו את האש ואת המאכלת וילכו שניהם יחדו
7 sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?”
ויאמר יצחק אל אברהם אביו ויאמר אבי ויאמר הנני בני ויאמר הנה האש והעצים ואיה השה לעלה
8 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.
ויאמר אברהם אלהים יראה לו השה לעלה בני וילכו שניהם יחדו
9 Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden.
ויבאו אל המקום אשר אמר לו האלהים ויבן שם אברהם את המזבח ויערך את העצים ויעקד את יצחק בנו וישם אתו על המזבח ממעל לעצים
10 Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa.
וישלח אברהם את ידו ויקח את המאכלת לשחט את בנו
11 Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.”
ויקרא אליו מלאך יהוה מן השמים ויאמר אברהם אברהם ויאמר הנני
12 Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.”
ויאמר אל תשלח ידך אל הנער ואל תעש לו מאומה כי עתה ידעתי כי ירא אלהים אתה ולא חשכת את בנך את יחידך ממני
13 Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.
וישא אברהם את עיניו וירא והנה איל אחר נאחז בסבך בקרניו וילך אברהם ויקח את האיל ויעלהו לעלה תחת בנו
14 Ibrahim kuwa ya ba wa wurin suna, Ubangiji Zai Tanada. Gama kamar yadda ake ce har yă zuwa yau, “A bisan dutsen Ubangiji, za a tanada.”
ויקרא אברהם שם המקום ההוא יהוה יראה אשר יאמר היום בהר יהוה יראה
15 Mala’ikan Ubangiji ya kira Ibrahim daga sama sau na biyu
ויקרא מלאך יהוה אל אברהם שנית מן השמים
16 ya ce, “Na rantse da kaina, in ji Ubangiji, domin ka yi wannan, ba ka kuwa hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba,
ויאמר בי נשבעתי נאם יהוה כי יען אשר עשית את הדבר הזה ולא חשכת את בנך את יחידך
17 tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,
כי ברך אברכך והרבה ארבה את זרעך ככוכבי השמים וכחול אשר על שפת הים וירש זרעך את שער איביו
18 ta wurin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka, domin ka yi mini biyayya.”
והתברכו בזרעך כל גויי הארץ עקב אשר שמעת בקלי
19 Sa’an nan Ibrahim ya koma wurin bayinsa, suka kuma kama hanya tare zuwa Beyersheba. Ibrahim kuwa ya yi zamansa a Beyersheba.
וישב אברהם אל נעריו ויקמו וילכו יחדו אל באר שבע וישב אברהם בבאר שבע
20 Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka,’ya’ya maza;
ויהי אחרי הדברים האלה ויגד לאברהם לאמר הנה ילדה מלכה גם הוא בנים--לנחור אחיך
21 ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram),
את עוץ בכרו ואת בוז אחיו ואת קמואל אבי ארם
22 Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”
ואת כשד ואת חזו ואת פלדש ואת ידלף ואת בתואל
23 Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan’ya’ya maza takwas.
ובתואל ילד את רבקה שמנה אלה ילדה מלכה לנחור אחי אברהם
24 Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.
ופילגשו ושמה ראומה ותלד גם הוא את טבח ואת גחם ואת תחש ואת מעכה

< Farawa 22 >