< Farawa 21 >

1 Ana nan sai Ubangiji ya nuna wa Saratu alheri kamar yadda ya ce, Ubangiji kuma ya yi wa Saratu abin da ya yi alkawari.
ויהוה פקד את שרה כאשר אמר ויעש יהוה לשרה כאשר דבר
2 Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.
ותהר ותלד שרה לאברהם בן לזקניו למועד אשר דבר אתו אלהים
3 Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.
ויקרא אברהם את שם בנו הנולד לו אשר ילדה לו שרה--יצחק
4 Sa’ad da ɗansa Ishaku ya kai kwana takwas da haihuwa, sai Ibrahim ya yi masa kaciya, kamar yadda Allah ya umarce shi.
וימל אברהם את יצחק בנו בן שמנת ימים כאשר צוה אתו אלהים
5 Ibrahim yana da shekara ɗari, sa’ad da aka haifa masa ɗansa Ishaku.
ואברהם בן מאת שנה בהולד לו את יצחק בנו
6 Saratu ta ce, “Allah ya sa na yi dariya, kuma duk wanda ya ji game da wannan, zai yi dariya tare da ni.”
ותאמר שרה--צחק עשה לי אלהים כל השמע יצחק לי
7 Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”
ותאמר מי מלל לאברהם היניקה בנים שרה כי ילדתי בן לזקניו
8 Yaron ya yi girma, aka kuma yaye shi, a ranar da aka yaye shi kuwa, Ibrahim ya yi babban biki.
ויגדל הילד ויגמל ויעש אברהם משתה גדול ביום הגמל את יצחק
9 Amma Saratu ta ga cewa yaron da Hagar, mutuniyar Masar ta haifa wa Ibrahim yana wa ɗanta Ishaku gori,
ותרא שרה את בן הגר המצרית אשר ילדה לאברהם--מצחק
10 sai ta ce wa Ibrahim, “Ka kori baiwan nan tare da ɗanta, saboda ɗan baiwan nan ba zai taɓa raba gādo da ɗana Ishaku ba.”
ותאמר לאברהם גרש האמה הזאת ואת בנה כי לא יירש בן האמה הזאת עם בני עם יצחק
11 Al’amarin ya ɓata wa Ibrahim rai sosai domin zancen ya shafi ɗansa.
וירע הדבר מאד בעיני אברהם על אודת בנו
12 Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada hankalinka yă tashi game da yaron nan da kuma baiwarka. Ka saurari duk abin da Saratu ta faɗa maka, saboda ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.
ויאמר אלהים אל אברהם אל ירע בעיניך על הנער ועל אמתך--כל אשר תאמר אליך שרה שמע בקלה כי ביצחק יקרא לך זרע
13 Zan ba ɗan baiwan nan al’umma shi ma, domin shi zuriyarka ne.”
וגם את בן האמה לגוי אשימנו כי זרעך הוא
14 Kashegari da sassafe sai Ibrahim ya ɗauki abinci da salkar ruwa, ya ba wa Hagar. Ya ɗora su a kafaɗunta, sa’an nan ya sallame ta da yaron. Ta kama hanyarta ta kuma yi ta yawo a cikin jejin Beyersheba.
וישכם אברהם בבקר ויקח לחם וחמת מים ויתן אל הגר שם על שכמה ואת הילד--וישלחה ותלך ותתע במדבר באר שבע
15 Sa’ad da ruwan da yake cikin salkan ya ƙare, sai ta ajiye yaron a ƙarƙashin wani ƙaramin itace.
ויכלו המים מן החמת ותשלך את הילד תחת אחד השיחם
16 Sai ta tafi, ta zauna ɗan nesa da yaron, misalin nisan harbin baka, gama ta yi tunani ta ce, “Ba zan iya kallon yaron yana mutuwa ba.” Da ta zauna nesa da yaron, sai ta fara kuka.
ותלך ותשב לה מנגד הרחק כמטחוי קשת כי אמרה אל אראה במות הילד ותשב מנגד ותשא את קלה ותבך
17 Allah kuwa ya ji yaron yana kuka, sai mala’ikan Allah ya kira Hagar daga sama ya ce mata, “Mene ne damuwarki, Hagar? Kada ki ji tsoro, Allah ya ji yaron yana kuka yayinda yake kwance a can.
וישמע אלהים את קול הנער ויקרא מלאך אלהים אל הגר מן השמים ויאמר לה מה לך הגר אל תיראי כי שמע אלהים אל קול הנער באשר הוא שם
18 Ki ɗaga yaron ki riƙe shi a hannu, gama zan mai da shi al’umma mai girma.”
קומי שאי את הנער והחזיקי את ידך בו כי לגוי גדול אשימנו
19 Sa’an nan Allah ya buɗe idanunta ta ga wata rijiyar ruwa. Don haka sai ta tafi ta cika salkan da ruwa, ta kuma ba wa yaron ruwa ya sha.
ויפקח אלהים את עיניה ותרא באר מים ותלך ותמלא את החמת מים ותשק את הנער
20 Allah ya kasance da yaron, yayinda yake girma. Ya yi zama a jeji, ya kuma zama maharbi.
ויהי אלהים את הנער ויגדל וישב במדבר ויהי רבה קשת
21 Yayinda yake zama a Jejin Faran, sai mahaifiyarsa ta samo masa mata daga Masar.
וישב במדבר פארן ותקח לו אמו אשה מארץ מצרים
22 A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi.
ויהי בעת ההוא ויאמר אבימלך ופיכל שר צבאו אל אברהם לאמר אלהים עמך בכל אשר אתה עשה
23 Yanzu ka rantse mini a nan a gaban Allah cewa, ba za ka yaudare ni ko’ya’yana ko kuma zuriyata ba. Ka nuna mini alheri, kai da ƙasar da kake zama baƙunci kamar yadda na nuna maka.”
ועתה השבעה לי באלהים הנה אם תשקר לי ולניני ולנכדי כחסד אשר עשיתי עמך תעשה עמדי ועם הארץ אשר גרתה בה
24 Ibrahim ya ce, “Na rantse.”
ויאמר אברהם אנכי אשבע
25 Sa’an nan Ibrahim ya kawo kuka ga Abimelek game da rijiyar ruwan da bayin Abimelek suka ƙwace.
והוכח אברהם את אבימלך על אדות באר המים אשר גזלו עבדי אבימלך
26 Sai Abimelek ya ce, “Ban san wanda ya yi wannan ba. Ba ka faɗa mini ba, ban kuwa taɓa ji ba, sai yau.”
ויאמר אבימלך--לא ידעתי מי עשה את הדבר הזה וגם אתה לא הגדת לי וגם אנכי לא שמעתי--בלתי היום
27 Sai Ibrahim ya kawo tumaki da shanu ya ba wa Abimelek, sai su biyun suka yi yarjejjeniya.
ויקח אברהם צאן ובקר ויתן לאבימלך ויכרתו שניהם ברית
28 Ibrahim ya ware’yan raguna bakwai daga cikin garke,
ויצב אברהם את שבע כבשת הצאן--לבדהן
29 sai Abimelek ya ce wa Ibrahim, “Mene ne ma’anar’yan raguna bakwai da ka keɓe?”
ויאמר אבימלך אל אברהם מה הנה שבע כבשת האלה אשר הצבת לבדנה
30 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ka karɓi waɗannan’yan tumaki bakwai daga hannuna a matsayin shaida cewa ni ne na haƙa wannan rijiya.”
ויאמר--כי את שבע כבשת תקח מידי בעבור תהיה לי לעדה כי חפרתי את הבאר הזאת
31 Saboda haka aka kira wurin Beyersheba, domin a nan ne su biyun suka yi rantsuwa.
על כן קרא למקום ההוא--באר שבע כי שם נשבעו שניהם
32 Bayan da aka yi yarjejjeniya a Beyersheba, sai Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka koma ƙasar Filistiyawa.
ויכרתו ברית בבאר שבע ויקם אבימלך ופיכל שר צבאו וישבו אל ארץ פלשתים
33 Sai Ibrahim ya shuka itacen tsamiya a Beyersheba, a can kuma ya kira bisa sunan Ubangiji, Allah Madawwami.
ויטע אשל בבאר שבע ויקרא שם--בשם יהוה אל עולם
34 Ibrahim kuwa ya zauna a ƙasar Filistiyawa na dogon lokaci.
ויגר אברהם בארץ פלשתים ימים רבים

< Farawa 21 >