< Farawa 17 >

1 Sa’ad da Abram ya yi shekaru 99, sai Ubangiji ya bayyana a gare shi ya ce, ni “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi tafiya a gabana ka kuma zama marar abin zargi.
Abram tenía 99 años cuando Yavé se le apareció, y le dijo: Yo soy ʼEL-Shadday. Anda delante de Mí y sé perfecto.
2 Zan tabbatar da alkawarina tsakanina da kai, zan kuma ƙara zuriyarka ta yi yawa.”
Estableceré mi Pacto entre Yo y tú, y te multiplicaré muchísimo.
3 Abram ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, Allah kuma ya ce masa,
Entonces Abram se postró sobre su rostro. ʼElohim le habló:
4 “Gare ni kam, wannan shi ne alkawarina da kai, za ka zama mahaifin al’ummai masu yawa.
Mira, establezco mi Pacto contigo: Serás padre de una multitud de pueblos.
5 Ba za a ƙara kiranka Abram ba; sunanka zai zama Ibrahim, gama na mai da kai uban al’ummai masu yawa.
Tu nombre ya no será Abram, sino Abraham, porque te constituí padre de una multitud de pueblos.
6 Zan sa ka azurta sosai, zan yi al’ummai daga cikinka, sarakuna kuma za su fito daga cikinka,
Te haré muy fecundo. Haré naciones de ti, y de ti saldrán reyes.
7 zan kafa alkawarina kamar madawwamin alkawari tsakanina da kai da kuma zuriyarka bayanka har tsararraki masu zuwa, in zama Allahnka da kuma Allahn zuriyarka a bayanka.
Yo establezco mi Pacto entre Yo y tú, y después de ti con tu descendencia en sus generaciones como alianza perpetua, para ser el ʼElohim tuyo y a tu descendencia.
8 Dukan ƙasar Kan’ana inda kake baƙo a yanzu, zan ba da ita a matsayin madawwamiyar mallaka gare ka da kuma zuriyarka a bayanka, zan kuma zama Allahnsu.”
Te daré por posesión perpetua la tierra de tus peregrinaciones, toda la tierra de Canaán, y a tu descendencia. Y seré su ʼElohim.
9 Sa’an nan Allah ya ce wa Ibrahim. “Kai fa, sai ka kiyaye alkawarina, kai da zuriyarka bayanka, har tsararraki masu zuwa.
Además ʼElohim dijo a Abraham: Tú guardarás mi Pacto, tú y tu descendencia en sus generaciones.
10 Wannan shi ne alkawarina da kai da kuma zuriyarka a bayanka, alkawarin da za ka kiyaye ke nan. Kowane namiji a cikinku kuwa za a yi masa kaciya.
Éste es mi Pacto entre Yo y ustedes, el cual guardarán tú y tu descendencia: Que todo varón entre ustedes sea circuncidado.
11 Za ku yi kaciya, za tă kuma zama alamar alkawari tsakanina da kai.
Circuncidarán sus prepucios, y esta será la señal del Pacto entre Yo y ustedes.
12 Daga yanzu duk namijin da aka haifa a cikinku za a yi masa kaciya a rana ta takwas har dukan zamananku, ko haifaffen gida ne, ko sayayye da kuɗi daga kowane baƙo wanda ba na zuriyarku ba.
Todo varón entre ustedes en todas sus generaciones será circuncidado a los ocho días de nacido, tanto el nacido en casa, como el comprado con dinero a cualquier extranjero que no sea de tu descendencia.
13 Ko haifaffe a gidanka ko an sayo da kuɗi, dole a yi musu kaciya. Alkawarina cikin jikinku zai kasance madawwamin alkawari.
Ciertamente será circuncidado el nacido en tu casa y el comprado con tu dinero. Mi Pacto estará en su cuerpo como Pacto eterno.
14 Kowane namijin da ba a yi masa kaciya a jiki ba, za a fid da shi daga cikin mutanensa; domin ya karya alkawarina.”
Pero el varón incircunciso, que no haya circuncidado su prepucio, será cortado de su pueblo. Quebrantó mi Pacto.
15 Allah ya kuma ce wa Ibrahim, “Game da Saira matarka kuwa, ba za ka ƙara kiranta Saira ba, sunanta zai zama Saratu.
También ʼElohim dijo a Abraham: A tu esposa Saray no la llamarás Saray, sino su nombre será Sara.
16 Zan sa mata albarka, ban da haka ma, zan ba ka ɗa ta wurinta, zan sa mata albarka, za tă kuwa zama mahaifiyar al’ummai; sarakunan mutane za su fito daga gare ta.”
La bendeciré y también te daré un hijo por medio de ella. Sí, la bendeciré. Ella [será madre de] naciones. Reyes de pueblos procederán de ella.
17 Ibrahim ya rusuna da fuskarsa har ƙasa, ya yi dariya, ya ce wa kansa, “Za a haifi ɗa wa mutum mai shekaru ɗari? Saratu za tă haifi ɗa tana da shekaru tasa’in?”
Abraham se postró sobre su rostro. Pero se rió y dijo en su corazón: ¿A un hombre de 100 años le nacerá un hijo? Y Sara, ¿dará a luz a los 90 años?
18 Ibrahim ya kuma ce wa Allah, “Me zai hana a dai bar Ishmayel kawai yă gāji alkawarin nan da ka yi mini.”
Abraham dijo a ʼElohim: ¡Ojalá Ismael viva delante de Ti!
19 Sai Allah ya ce, “Duk da haka dai, matarka Saratu za tă haifi maka ɗa; za ka kuma kira shi Ishaku. A kansa zan tabbatar da madawwamin alkawarina, da kuma ga zuriyarsa da za su zo bayansa.
Pero ʼElohim le dijo: Ciertamente tu esposa Sara te dará a luz un hijo. Tú lo llamarás Isaac, y estableceré mi Pacto con él como Pacto perpetuo para su descendencia después de él.
20 Game da Ishmayel kuwa, na ji ka. Tabbatacce zan albarkace shi, zan sa yă azurta, zai kuma ƙaru ƙwarai. Zai zama mahaifin masu mulki goma sha biyu, zan kuma maishe shi babban al’umma!
En cuanto a Ismael, te escuché: Ciertamente lo bendeciré, lo haré fecundo y lo multiplicaré muchísimo. Engendrará 12 príncipes y haré de él una gran nación.
21 Amma dai zan kafa alkawarina da Ishaku wanda Saratu za tă haifa maka war haka shekara mai zuwa.”
Pero mi Pacto lo confirmaré con Isaac, a quien Sara te dará a luz por este tiempo, el año próximo.
22 Da ya gama magana da Ibrahim, sai Allah ya tashi daga gare shi.
Cuando terminó de hablarle, ʼElohim ascendió de [la presencia] de Abraham.
23 A wannan rana, Ibrahim ya ɗauki ɗansa Ishmayel da dukan waɗanda aka haifa cikin gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗinsa, ya kuwa yi wa kowane namiji a cikin gidansa kaciya kamar yadda Allah ya faɗa masa.
Entonces ese mismo día Abraham tomó a Ismael su hijo, a todos los nacidos en su casa, a todos los comprados con su dinero, y a todo varón entre las gentes de la casa de Abraham, y circuncidó su prepucio, como ʼElohim le dijo.
24 Ibrahim yana da shekara tasa’in da tara sa’ad da aka yi masa kaciya,
Abraham tenía 99 años cuando circuncidó su prepucio,
25 Ishmayel ɗansa kuma yana da shekara goma sha uku.
y su hijo Ismael tenía 13 años cuando su prepucio fue circuncidado.
26 Aka yi wa Ibrahim da ɗansa Ishmayel kaciya a rana ɗaya.
Aquel mismo día Abraham se circuncidó, y también su hijo Ismael.
27 Aka yi wa kowane namiji a gidan Ibrahim kaciya, da waɗanda aka haifa a gidansa, da waɗanda aka sayo da kuɗi daga baƙo.
Todos los hombres de su casa, nacidos en casa o comprados con dinero a un extranjero, fueron circuncidados con él.

< Farawa 17 >