< Farawa 16 >

1 To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,
ושרי אשת אברם לא ילדה לו ולה שפחה מצרית ושמה הגר
2 saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.” Abram kuwa ya yarda da abin da Saira ta faɗa.
ותאמר שרי אל אברם הנה נא עצרני יהוה מלדת--בא נא אל שפחתי אולי אבנה ממנה וישמע אברם לקול שרי
3 Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.
ותקח שרי אשת אברם את הגר המצרית שפחתה מקץ עשר שנים לשבת אברם בארץ כנען ותתן אתה לאברם אישה לו לאשה
4 Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki. Sa’ad da Hagar ta gane tana da ciki, sai ta fara rena uwargijiyarta.
ויבא אל הגר ותהר ותרא כי הרתה ותקל גברתה בעיניה
5 Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”
ותאמר שרי אל אברם חמסי עליך--אנכי נתתי שפחתי בחיקך ותרא כי הרתה ואקל בעיניה ישפט יהוה ביני וביניך
6 Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.
ויאמר אברם אל שרי הנה שפחתך בידך--עשי לה הטוב בעיניך ותענה שרי ותברח מפניה
7 Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur.
וימצאה מלאך יהוה על עין המים--במדבר על העין בדרך שור
8 Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?” Ta amsa ta ce, “Ina gudu ne daga wurin uwargijiyata Saira.”
ויאמר הגר שפחת שרי אי מזה באת--ואנה תלכי ותאמר--מפני שרי גברתי אנכי ברחת
9 Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.”
ויאמר לה מלאך יהוה שובי אל גברתך והתעני תחת ידיה
10 Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”
ויאמר לה מלאך יהוה הרבה ארבה את זרעך ולא יספר מרב
11 Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata, “Ga shi kina da ciki za ki kuwa haifi ɗa. Za ki ba shi suna Ishmayel, gama Ubangiji ya ga wahalarki.
ויאמר לה מלאך יהוה הנך הרה וילדת בן וקראת שמו ישמעאל כי שמע יהוה אל עניך
12 Zai zama mutum mai halin jakin jeji. Hannunsa zai yi gāba da kowa, hannun kowa kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zama gāba ga dukan’yan’uwansa.”
והוא יהיה פרא אדם--ידו בכל ויד כל בו ועל פני כל אחיו ישכן
13 Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.”
ותקרא שם יהוה הדבר אליה אתה אל ראי כי אמרה הגם הלם ראיתי--אחרי ראי
14 Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.
על כן קרא לבאר באר לחי ראי--הנה בין קדש ובין ברד
15 Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.
ותלד הגר לאברם בן ויקרא אברם שם בנו אשר ילדה הגר ישמעאל
16 Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.
ואברם בן שמנים שנה ושש שנים בלדת הגר את ישמעאל לאברם

< Farawa 16 >