< Farawa 13 >

1 Saboda haka Abram ya haura daga Masar zuwa Negeb tare da matarsa, da dukan abin da yake da shi tare da Lot.
ויעל אברם ממצרים הוא ואשתו וכל אשר לו ולוט עמו--הנגבה
2 Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya.
ואברם כבד מאד במקנה בכסף ובזהב
3 Daga Negeb, ya ci gaba da tafiyarsa a wurare dabam-dabam har ya kai tsakanin Betel da Ai, a inda dā ya kafa tentinsa na fari
וילך למסעיו מנגב ועד בית אל--עד המקום אשר היה שם אהלה בתחלה בין בית אל ובין העי
4 da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
אל מקום המזבח אשר עשה שם בראשנה ויקרא שם אברם בשם יהוה
5 Lot wanda yake tafiya tare da Abram, shi ma yana da garken shanu da tumaki da kuma tentuna.
וגם ללוט--ההלך את אברם היה צאן ובקר ואהלים
6 Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba.
ולא נשא אתם הארץ לשבת יחדו כי היה רכושם רב ולא יכלו לשבת יחדו
7 Rikici kuma ya tashi tsakanin masu kiwon dabbobin Abram da na Lot. Mazaunan ƙasar, a lokacin kuwa Kan’aniyawa da Ferizziyawa ne.
ויהי ריב בין רעי מקנה אברם ובין רעי מקנה לוט והכנעני והפרזי אז ישב בארץ
8 Saboda haka Abram ya ce wa Lot, “Kada mu bar rikici yă shiga tsakaninmu, ko kuma tsakanin masu kiwon dabbobinka da nawa, gama mu’yan’uwa ne.
ויאמר אברם אל לוט אל נא תהי מריבה ביני ובינך ובין רעי ובין רעיך כי אנשים אחים אנחנו
9 Ba ga dukan ƙasar tana gabanka ba? Bari mu rabu. In ka yi hagu sai ni in yi dama. In ka yi dama, sai ni in yi hagu.”
הלא כל הארץ לפניך הפרד נא מעלי אם השמאל ואימנה ואם הימין ואשמאילה
10 Lot ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, sai ya ga kwarin yana da ciyawa mai kyau ƙwarai sai ka ce lambun Ubangiji, kamar ƙasar Masar, wajajen Zowar. (Wannan fa kafin Ubangiji yă hallaka Sodom da Gomorra.)
וישא לוט את עיניו וירא את כל ככר הירדן כי כלה משקה--לפני שחת יהוה את סדם ואת עמרה כגן יהוה כארץ מצרים באכה צער
11 Saboda haka sai Lot ya zaɓar wa kansa dukan kwarin Urdun, ya tashi ya nufi wajen gabas. Haka fa suka rabu da juna.
ויבחר לו לוט את כל ככר הירדן ויסע לוט מקדם ויפרדו איש מעל אחיו
12 Abram ya zauna a ƙasar Kan’ana, yayinda Lot ya zauna cikin biranen kwari, ya kafa tentunansa kusa da Sodom.
אברם ישב בארץ כנען ולוט ישב בערי הככר ויאהל עד סדם
13 Mutanen Sodom kuwa mugaye ne, sun aikata zunubi ƙwarai ga Ubangiji.
ואנשי סדם רעים וחטאים ליהוה מאד
14 Bayan Lot ya rabu da Abram, sai Ubangiji ya ce wa Abram, “Ɗaga idanunka daga inda kake, ka dubi arewa da kudu, gabas da yamma.
ויהוה אמר אל אברם אחרי הפרד לוט מעמו שא נא עיניך וראה מן המקום אשר אתה שם--צפנה ונגבה וקדמה וימה
15 Dukan ƙasar da kake gani zan ba ka, kai da zuriyarka har abada.
כי את כל הארץ אשר אתה ראה לך אתננה ולזרעך עד עולם
16 Zan sa zuriyarka tă yi yawa kamar ƙurar ƙasa, har in wani yana iya ƙidaya ƙurar, to, za a iya ƙidaya zuriyarka.
ושמתי את זרעך כעפר הארץ אשר אם יוכל איש למנות את עפר הארץ--גם זרעך ימנה
17 Tafi, ka ratsa tsawo da fāɗin ƙasar, gama zan ba ka ita.”
קום התהלך בארץ לארכה ולרחבה כי לך אתננה
18 Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.
ויאהל אברם ויבא וישב באלני ממרא--אשר בחברון ויבן שם מזבח ליהוה

< Farawa 13 >