< Farawa 11 >

1 To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce.
ויהי כל הארץ שפה אחת ודברים אחדים
2 Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can.
ויהי בנסעם מקדם וימצאו בקעה בארץ שנער וישבו שם
3 Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka.
ויאמרו איש אל רעהו הבה נלבנה לבנים ונשרפה לשרפה ותהי להם הלבנה לאבן והחמר היה להם לחמר
4 Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.”
ויאמרו הבה נבנה לנו עיר ומגדל וראשו בשמים ונעשה לנו שם פן נפוץ על פני כל הארץ
5 Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini.
וירד יהוה לראת את העיר ואת המגדל אשר בנו בני האדם
6 Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba.
ויאמר יהוה הן עם אחד ושפה אחת לכלם וזה החלם לעשות ועתה לא יבצר מהם כל אשר יזמו לעשות
7 Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.”
הבה נרדה ונבלה שם שפתם--אשר לא ישמעו איש שפת רעהו
8 Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin.
ויפץ יהוה אתם משם על פני כל הארץ ויחדלו לבנת העיר
9 Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.
על כן קרא שמה בבל כי שם בלל יהוה שפת כל הארץ ומשם הפיצם יהוה על פני כל הארץ
10 Wannan shi ne labarin Shem. Shekara biyu bayan ambaliya, sa’ad da Shem ya yi shekara 100, sai ya haifi Arfakshad.
אלה תולדת שם--שם בן מאת שנה ויולד את ארפכשד שנתים אחר המבול
11 Bayan ya haifi Arfakshad, Shem ya yi shekara 500, ya haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי שם אחרי הולידו את ארפכשד חמש מאות שנה ויולד בנים ובנות
12 Sa’ad da Arfakshad ya yi shekara 35, sai ya haifi Shela.
וארפכשד חי חמש ושלשים שנה ויולד את שלח
13 Bayan ya haifi Shela kuwa, Arfakshad ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי ארפכשד אחרי הולידו את שלח שלש שנים וארבע מאות שנה ויולד בנים ובנות
14 Sa’ad da Shela ya yi shekaru 30, sai ya haifi Eber.
ושלח חי שלשים שנה ויולד את עבר
15 Bayan ya haifi Eber, Shela ya yi shekara 403, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי שלח אחרי הולידו את עבר שלש שנים וארבע מאות שנה ויולד בנים ובנות
16 Sa’ad da Eber ya yi shekaru 34, sai ya haifi Feleg.
ויחי עבר ארבע ושלשים שנה ויולד את פלג
17 Bayan ya haifi Feleg, Eber ya yi shekara 430, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי עבר אחרי הולידו את פלג שלשים שנה וארבע מאות שנה ויולד בנים ובנות
18 Sa’ad da Feleg ya yi shekaru 30, sai ya haifi Reyu.
ויחי פלג שלשים שנה ויולד את רעו
19 Bayan ya haifi Reyu, Feleg ya yi shekara 209, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי פלג אחרי הולידו את רעו תשע שנים ומאתים שנה ויולד בנים ובנות
20 Sa’ad da Reyu ya yi shekaru 32, sai ya haifi Serug.
ויחי רעו שתים ושלשים שנה ויולד את שרוג
21 Bayan ya haifi Serug, Reyu ya yi shekara 207, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי רעו אחרי הולידו את שרוג שבע שנים ומאתים שנה ויולד בנים ובנות
22 Sa’ad da Serug ya yi shekaru 30, sai ya haifi Nahor.
ויחי שרוג שלשים שנה ויולד את נחור
23 Bayan ya haifi Nahor, Serug ya yi shekara 200, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי שרוג אחרי הולידו את נחור--מאתים שנה ויולד בנים ובנות
24 Sa’ad da Nahor ya yi shekaru 29, sai ya haifi Tera.
ויחי נחור תשע ועשרים שנה ויולד את תרח
25 Bayan ya haifi Tera, Nahor ya yi shekara 119, ya kuma haifi waɗansu’ya’ya maza da mata.
ויחי נחור אחרי הולידו את תרח תשע עשרה שנה ומאת שנה ויולד בנים ובנות
26 Bayan Tera ya yi shekaru 70, sai ya haifi Abram, Nahor da Haran.
ויחי תרח שבעים שנה ויולד את אברם את נחור ואת הרן
27 Wannan ita ce zuriyar Tera. Tera ya haifi Abram, Nahor da Haran. Haran kuma ya haifi Lot.
ואלה תולדת תרח--תרח הוליד את אברם את נחור ואת הרן והרן הוליד את לוט
28 Yayinda mahaifinsa Tera yana da rai, Haran ya rasu a Ur ta Kaldiyawa, a ƙasar haihuwarsa.
וימת הרן על פני תרח אביו בארץ מולדתו באור כשדים
29 Abram da Nahor suka yi aure. Sunan matar Abram, Saira ne, sunan matar Nahor kuwa Milka; ita’yar Haran ce, mahaifin Milka da Iska.
ויקח אברם ונחור להם נשים שם אשת אברם שרי ושם אשת נחור מלכה בת הרן אבי מלכה ואבי יסכה
30 Saira kuwa bakararriya ce, ba ta da yara.
ותהי שרי עקרה אין לה ולד
31 Tera ya ɗauki ɗansa Abraham, jikansa Lot ɗan Haran, da surukarsa Saira, matar Abram, tare kuwa suka bar Ur ta Kaldiyawa, don su tafi Kan’ana. Amma sa’ad da suka zo Haran sai suka zauna a can.
ויקח תרח את אברם בנו ואת לוט בן הרן בן בנו ואת שרי כלתו אשת אברם בנו ויצאו אתם מאור כשדים ללכת ארצה כנען ויבאו עד חרן וישבו שם
32 Tera yi shekaru 205, ya kuma mutu a Haran.
ויהיו ימי תרח חמש שנים ומאתים שנה וימת תרח בחרן

< Farawa 11 >