+ Farawa 1 >
1 A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.
In principio Dio creò il cielo e la terra.
2 To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
Ora la terra era informe e deserta e le tenebre ricoprivano l'abisso e lo spirito di Dio aleggiava sulle acque.
3 Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske.
Dio disse: «Sia la luce!». E la luce fu.
4 Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu.
Dio vide che la luce era cosa buona e separò la luce dalle tenebre
5 Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
e chiamò la luce giorno e le tenebre notte. E fu sera e fu mattina: primo giorno.
6 Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.”
Dio disse: «Sia il firmamento in mezzo alle acque per separare le acque dalle acque».
7 Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance.
Dio fece il firmamento e separò le acque, che sono sotto il firmamento, dalle acque, che son sopra il firmamento. E così avvenne.
8 Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
Dio chiamò il firmamento cielo. E fu sera e fu mattina: secondo giorno.
9 Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance.
Dio disse: «Le acque che sono sotto il cielo, si raccolgano in un solo luogo e appaia l'asciutto». E così avvenne.
10 Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.
Dio chiamò l'asciutto terra e la massa delle acque mare. E Dio vide che era cosa buona.
11 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
E Dio disse: «La terra produca germogli, erbe che producono seme e alberi da frutto, che facciano sulla terra frutto con il seme, ciascuno secondo la sua specie». E così avvenne:
12 Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.
la terra produsse germogli, erbe che producono seme, ciascuna secondo la propria specie e alberi che fanno ciascuno frutto con il seme, secondo la propria specie. Dio vide che era cosa buona.
13 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
E fu sera e fu mattina: terzo giorno.
14 Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru,
Dio disse: «Ci siano luci nel firmamento del cielo, per distinguere il giorno dalla notte; servano da segni per le stagioni, per i giorni e per gli anni
15 bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance.
e servano da luci nel firmamento del cielo per illuminare la terra». E così avvenne:
16 Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari.
Dio fece le due luci grandi, la luce maggiore per regolare il giorno e la luce minore per regolare la notte, e le stelle.
17 Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya,
Dio le pose nel firmamento del cielo per illuminare la terra
18 su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
e per regolare giorno e notte e per separare la luce dalle tenebre. E Dio vide che era cosa buona.
19 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
E fu sera e fu mattina: quarto giorno.
20 Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.”
Dio disse: «Le acque brulichino di esseri viventi e uccelli volino sopra la terra, davanti al firmamento del cielo».
21 Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Dio creò i grandi mostri marini e tutti gli esseri viventi che guizzano e brulicano nelle acque, secondo la loro specie, e tutti gli uccelli alati secondo la loro specie. E Dio vide che era cosa buona.
22 Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.”
Dio li benedisse: «Siate fecondi e moltiplicatevi e riempite le acque dei mari; gli uccelli si moltiplichino sulla terra».
23 Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
E fu sera e fu mattina: quinto giorno.
24 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.
Dio disse: «La terra produca esseri viventi secondo la loro specie: bestiame, rettili e bestie selvatiche secondo la loro specie». E così avvenne:
25 Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
Dio fece le bestie selvatiche secondo la loro specie e il bestiame secondo la propria specie e tutti i rettili del suolo secondo la loro specie. E Dio vide che era cosa buona.
26 Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”
E Dio disse: «Facciamo l'uomo a nostra immagine, a nostra somiglianza, e domini sui pesci del mare e sugli uccelli del cielo, sul bestiame, su tutte le bestie selvatiche e su tutti i rettili che strisciano sulla terra».
27 Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
Dio creò l'uomo a sua immagine; a immagine di Dio lo creò; maschio e femmina li creò.
28 Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.”
Dio li benedisse e disse loro: «Siate fecondi e moltiplicatevi, riempite la terra; soggiogatela e dominate sui pesci del mare e sugli uccelli del cielo e su ogni essere vivente, che striscia sulla terra».
29 Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.
Poi Dio disse: «Ecco, io vi do ogni erba che produce seme e che è su tutta la terra e ogni albero in cui è il frutto, che produce seme: saranno il vostro cibo.
30 Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance.
A tutte le bestie selvatiche, a tutti gli uccelli del cielo e a tutti gli esseri che strisciano sulla terra e nei quali è alito di vita, io do in cibo ogni erba verde». E così avvenne.
31 Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
Dio vide quanto aveva fatto, ed ecco, era cosa molto buona. E fu sera e fu mattina: sesto giorno.