< Galatiyawa 4 >
1 Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.
2 Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.
3 Haka yake, sa’ad da muke’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.
4 Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,
5 domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman’ya’ya.
6 Da yake ku’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”
7 Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
8 Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne.
9 Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?
10 Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman!
11 Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!
12 Ina roƙonku’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
13 Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko.
14 Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
15 Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.
16 Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
17 Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su.
18 Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba.
19 Ya ku’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.
20 Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!
21 Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne?
22 Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa.
23 Ɗansa na wajen mace’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.
24 Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.
25 Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da’ya’yanta.
26 Amma Urushalimar da take sama’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.
27 Gama a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne’ya’yan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.”
28 To, ku’yan’uwa, ku’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.
29 A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.
30 Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”
31 Saboda haka,’yan’uwa, mu ba’ya’yan mace’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.