< Galatiyawa 2 >

1 Bayan shekara goma sha huɗu sai na sāke haurawa zuwa Urushalima, a wannan lokaci na tafi tare da Barnabas. Na kuma ɗauki Titus muka tafi tare.
Then after fourteen years again I went up to Jerusalem with Barnabas, having also taken Titus with me;
2 Na tafi ne bisa ga wani wahayi. Da na kai can, sai na bayyana musu bisharar da nake wa’azi a cikin Al’ummai. Na yi haka a keɓance a gaban waɗanda suke shugabanni, don tsoro kada gudun da nake yi, ko kuwa na riga na yi, yă zama a banza.
and I went up by revelation, and submitted the good news to them that I preach among the nations, and privately to those esteemed, lest I ran or might run in vain;
3 Amma ko Titus ma da yake tare da ni, ba a ce dole sai ya yi kaciya ba, ko da yake shi mutumin Al’ummai ne.
but not even Titus, who [is] with me, being a Greek, was compelled to be circumcised—
4 Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi.
and [that] because of the false brothers brought in unaware, who came in secretly to spy out our liberty that we have in Christ Jesus, that they might bring us under bondage,
5 Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.
to whom not even for an hour we gave place by subjection, that the truth of the good news might remain to you.
6 Game da waɗanda aka ɗauka a dā a kan su wani abu ne, ko wane ne su, duk ɗaya ne a wurina; gama Allah ba ya nuna bambanci, ina dai gaya muku waɗannan da suke wani abu ne a dā, ba su ƙara mini kome ba.
And from those who were esteemed to be something—whatever they were then, it makes no difference to me. God does not accept the face of man, for to me those esteemed added nothing,
7 A maimakon haka, sun ga cewa an danƙa mini hakkin wa’azin bishara ga Al’ummai, kamar yadda aka danƙa wa Bitrus ga Yahudawa.
but on the contrary, having seen that I have been entrusted with the good news of the uncircumcision, as Peter with [that] of the circumcision,
8 Gama Allah wanda ya yi aiki a cikin hidimar Bitrus a matsayin manzo ga Yahudawa, haka ma ya yi aiki a cikin hidimata a matsayin manzo ga Al’ummai.
for He who worked with Peter to the apostleship of the circumcision, worked also in me in regard to the nations,
9 Yaƙub, Bitrus da Yohanna waɗanda suke fitattun ginshiƙai, sun karɓe ni da Barnabas da hannu biyu biyu sa’ad da suka gane alherin da aka ba ni. Suka kuma yarda cewa ya kamata mu tafi wajen Al’ummai, su kuwa su tafi wajen Yahudawa.
and having known the grace that was given to me, James, and Cephas, and John, who were esteemed to be pillars, they gave to me a right hand of fellowship, and to Barnabas, that we may go to the nations, and they to the circumcision,
10 Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.
only, that we should be mindful of the poor, which I also was diligent—this very thing—to do.
11 Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake.
And when Peter came to Antioch, I stood up against him to the face, because he was blameworthy,
12 Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya.
for before the coming of some from James, he was eating with the nations, and when they came, he was withdrawing and separating himself, fearing those of circumcision,
13 Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe.
and the other Jews acted hypocritically with him, so that Barnabas was also carried away by their hypocrisy.
14 Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?
But when I saw that they are not walking uprightly to the truth of the good news, I said to Peter before all, “If you, being a Jew, live in the manner of the nations, and not in the manner of the Jews, how do you compel the nations to live like Jews?
15 “Mu da muke Yahudawa ta wurin haihuwa ba Al’ummai masu zunubi ba,
We by nature Jews, and not sinners of the nations,
16 mun san cewa mutum ba ya samun kuɓuta ta wurin kiyaye Doka, sai dai ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Saboda haka, mu ma, muka sa bangaskiyarmu cikin Kiristi Yesu don mu sami kuɓuta ta wurin bangaskiya cikin Kiristi ba ta wurin kiyaye Doka ba, domin ba wanda zai kuɓuta ta wurin bin Doka.
having also known that a man is not declared righteous by works of law, but through faith from Jesus Christ, we also believed in Christ Jesus, that we might be declared righteous by faith from Christ, and not by works of law, because no flesh will be declared righteous by works of law.”
17 “In kuwa ya zama muna so mu sami zaman marasa laifi a gaban Allah ta wurin dogara ga Kiristi, sa’an nan an same mu mu kanmu ma masu zunubi ne, ashe, ko wannan zai nuna Kiristi yana ƙarfafa zunubi ke nan? A’a, ko kusa!
And if, seeking to be declared righteous in Christ, we were also ourselves found sinners, [is] Christ then a servant of sin? Let it not be!
18 In na sāke gina abin da na rushe, na zama mai karyar Doka ke nan.
For if the things I threw down, these again I build up, I set myself forth [as] a transgressor;
19 “Gama ta wurin Doka na mutu ga Doka saboda in rayu ga Allah.
for I died through law that I may live to God;
20 An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
I have been crucified with Christ, and I no longer live, but Christ lives in me; and that which I now live in the flesh—I live in the faith of the Son of God, who loved me and gave Himself for me;
21 Ba na ajiyar alherin Allah a gefe, gama da a ce ana samun adalci ta wurin Doka, ai, da Kiristi ya mutu a banza ke nan!”
I do not make the grace of God void, for if righteousness [is] through law—then Christ died in vain.

< Galatiyawa 2 >