< Ezra 8 >

1 Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.
在阿塔薛西斯在位期間,與我從巴比倫一同起程的族長,笸他們的祖譜,記載如下:
2 Daga zuriyar Finehas, Gershom ne shugaba; daga zuriyar Itamar, Daniyel ne shugaba; daga zuriyar Dawuda, Hattush
丕乃哈斯的子孫,有革爾雄;依塔瑪爾的子孫,有達尼爾;達味的子孫,有舍加尼雅的兒子哈突士,
3 ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba, daga zuriyar Farosh, Zakariya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 150;
帕洛士的子孫,有則加黎雅,同他登記的,有男子一百五十名;
4 daga Fahat-Mowab, Eliyehoyenai ɗan Zerahiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 200;
哈特摩阿布的子孫,有則辣希雅的兒子厄里約乃,同他一起的,有男子二百名;
5 daga zuriyar Zattu, Shekaniya ɗan Yahaziyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 300;
匝突的子孫,有雅哈齊耳的兒子舍加尼雅,同他一起的,有男子三百名;
6 daga zuriyar Adin, Ebed ɗan Yonatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 50;
阿丁的子孫,有約納堂的兒子厄貝得,同他一起的,有男子五十名;
7 daga zuriyar Elam, Yeshahiya ɗan Ataliya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 70;
厄藍的子孫,有阿塔里雅的所以耶沙雅,同他一起的,有男子七十名;
8 daga zuriyar Shefatiya, Zebadiya ɗan Mika’ilu ne shugaba, tare da shi akwai mutum 80;
舍法提雅的子孫,有米加耳的兒子則把狄雅,同他一起的,有男子八十名;
9 daga iyalin Yowab, Obadiya ɗan Yehiyel ne shugaba, tare da shi akwai mutum 218;
約阿布的子孫,有耶希耳的兒子敖巴狄雅,同他一起的,有男子二百一十八名;
10 daga Bani, Shelomit ɗan Yosifiya ne shugaba, tare da shi akwai mutum 160;
巴尼的子孫,有約息非雅的兒子舍羅米特,同他一起的,有男子一百六十名;
11 daga Bebai, Zakariya ɗan Bebai ne shugaba, tare da shi akwai mutum 28;
貝拜的子孫,有貝拜的兒子則加黎雅,同他一起的,有男子二十八名;
12 daga iyalin Azgad, Yohanan ɗan Hakkatan ne shugaba, tare da shi akwai mutum 110;
阿次加得的子孫,有哈卡堂的兒子約哈南,同他一起的,有男子一百一十名;
13 zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe, sunayensu kuwa su ne Elifelet, Yehiyel da Shemahiya, tare da su akwai mutum 60;
阿多尼干的子孫,是最後來的,他們的名字是厄里培肋特、耶依耳和舍雅,同他們一起的,有男子六十名。
14 daga zuriyar Bigwai, Uttai da Zakkur ne shugabanni, tare da su akwai mutum 70.
彼革外的子孫,鍵盤匝雇爾的兒子烏泰,同他一起的,有男子七十名。
15 Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa.
我將眾人召集在流往阿哈瓦的河邊,在那裏住了三天;當我視察眾人和司祭時,其中沒有發現一個肋未人。
16 Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.
我遂派首領厄里厄則爾、阿黎爾、舍瑪雅、厄耳納堂、雅黎布、厄耳納堂、納堂、則加黎雅和默叔藍通士約雅黎布和厄耳納堂,
17 Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.
命他們到加息非雅地方的首領依多那裏去,我並把他們應向那定居在加息非雅的依多和兄弟們,要說的話告訴了他們,好為我們天主的殿,給我們帶來侍役。
18 Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da’ya’yansa da kuma’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.
賴我們天主慈悲的手對我們的扶助,他們由以色列的兒子肋未的後裔瑪赫里的子孫中,給我們帶來了一位明智人,就是舍勒彼雅,和兒子及兄弟,一共十八人;
19 Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da’yan’uwansu da kuma’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne.
還有哈沙彼雅,同他一起的,有默辣黎的子孫耶沙和雅及兒子,一共二 十人;
20 Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.
還有達味和諸首長服事肋未人所立 獻身者,一共二百二十人;這些人全部都是登記了的。
21 A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da’ya’yanmu da kayanmu duka.
我遂在阿哈瓦河那裏禁食,在我們的天主前自謙自卑,祈求衪使我們和我們的子孫,並我們的一切財物,一路平安;
22 Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.”
因為我羞於請求君王派遺步隊和騎兵,協助我們防禦路上的仇敵,因為我們曾向君王說萵:「凡尋求天主的人,衪的手常加助佑;凡離棄衪的人,衪便施行強力和義怒」。
23 Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.
我們為此禁食,祈求我們的天主,衪便俯聽了我們。
24 Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma’yan’uwansu guda goma.
我由司祭的首領選了十二人,又選了舍勒彼雅和哈沙彼雅,以及同他們在一起的十個兄弟,
25 Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu.
把金銀和器皿,即君王和他的謀、首長,以及在那裏所有的以色列人,奉獻給我們天主殿的禮品,一一衡量了交給了他們。
26 Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya,
我衡量了交在他們手中的,有銀子六百五十「塔冷通」,銀器一百「塔冷通」,金子一百「塔冷通」;
27 kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.
還有金碗二十個,值一千「達理克」;發亮的銅器二個,貴如黃金。
28 Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku.
我向他們說:「你們在上主前是聖的,器皿也是聖的,金銀是自願獻於上主你們祖先的天主,作禮品的。
29 Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.”
你們要謹慎護守,直到在耶路撒冷,在上主殿宇的庫房內,當著司祭和肋未人的首領,以及以色列眾族長的面,衡量交清為止」。
30 Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima.
司祭自己和肋未人,就把數點過的金銀和器皿收下,帶到耶路撒冷我們天主的殿內。
31 A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da’yan fashi.
一月十二日,我們從阿哈瓦河起程赴耶路撒冷,賴我們天主的手扶助,我們一路脫免了仇人和暗害者的手,
32 Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.
平安到了耶路撒冷,在那裏休息了三天o
33 A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.
第四日,在我們天主是殿內,衡量了金銀和器皿,交給了烏利雅的兒子默勒摩特司祭,同他在一起的,還有丕乃哈斯的兒子厄肋阿匝爾,以及肋未人耶叔亞的兒子約匝巴得,和彼奴依的兒子諾阿狄雅,
34 Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin.
每件點過稱過,即將總數記錄下來。
35 Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida,’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.
當時被擄充軍回來的子民,向以色列的天主奉獻了全燔祭,為全以色列奉獻了牛犢十二頭,公綿羊九十六隻,羔羊七十二隻,作贖罪祭的公山羊十二隻:這一切都獻給上主作全燔祭。
36 Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah.
以後,他們向君王的州長和河西諸省長,呈上君王的諭令;他們便協助民眾,資助天主的殿宇。

< Ezra 8 >