< Ezra 5 >

1 Sai annabi Haggai, da annabi Zakariya zuriyar Iddo, suka yi wa Yahudawa a Yahuda da Urushalima annabci a cikin sunan Allah na Isra’ila wanda yake da mulki a kansu.
At that time two prophets gave messages from God to the Jews in Jerusalem and [other cities in] Judah. The prophets were Haggai and Zechariah, who was a descendant of Iddo. They spoke those messages representing God, whom the Israelis [worshiped/belonged to], the one who was their true king.
2 Sa’an nan Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel da Yeshuwa ɗan Yozadak suka yi shiri suka kama aikin sāke gina gidan Allah a Urushalima. Annabawan Allah kuwa suna tare da su, suna taimakonsu.
Then Zerubbabel and Shealtiel [led many other people] as they started [again] to rebuild the temple of God in Jerusalem. And God’s prophets [Haggai and Zechariah] were with them and helped them.
3 A wannan lokaci, Tattenai gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu suka je wurinsu suka tambaye su cewa, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali har ku gyara katangar?”
Then Tattenai the governor of the province west of the [Euphrates] River and Shethar-Bozenai his assistant and [some of] their officials went to Jerusalem and said to the people, “Who has permitted you to rebuild this temple and put furnishings in it?”
4 Suka kuma tambaye su “Ina sunayen waɗanda suke wannan gini?”
They also requested the people to tell them the names of the men who were working [at the temple]. [But the people refused].
5 Amma Allah yana tsaron dattawan Yahudawa, saboda haka ba a hana su aikin ba har sai rahoto ya kai wurin Dariyus aka kuma sami amsarsa a rubuce tukuna.
However, God was taking care of the Jewish leaders, so their enemies were not able to prevent the people from continuing [to rebuild the temple]. [They continued to work while their enemies] sent a report to King Darius, and asked him [what he wanted them to do] about it.
6 Ga wasiƙar da Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai da abokansu masu riƙe da muƙamai a Kewayen Kogin Yuferites suka aika wa Sarki Dariyus.
So Tattenai and Shethar-Bozenai and their officials sent a report to King Darius.
7 Ga rahoton da suka aika masa. Zuwa ga Sarki Dariyus. Gaisuwa da fatan alheri.
This is what they wrote: “King Darius, we hope that things are going well for you!
8 Ya kamata sarki yă sani cewa mun je yankin Yahuda, zuwa gidan Allah mai girma. Muka ga mutanen suna ginin haikalin da manyan duwatsu, suna sa katakai a bangon. Ana aikin da ƙwazo, aikin kuma yana cin gaba sosai, suna kuma lura da shi.
[“We want you to know that] we went to Judah Province, where the temple of the great God is being rebuilt. The people are building it with huge stones, and they are putting wooden beams in the walls. The work is being done very carefully, and they are progressing well.
9 Mun tambayi dattawan muka ce musu, “Wa ya ba ku iko ku sāke gina wannan haikali, ku kuma sāke gyara katangarsa?”
“We asked the Jewish leaders, ‘Who has permitted you to rebuild this temple and put furnishings in it?’
10 Muka kuma tambaye su sunayensu don mu rubuta mu sanar da kai waɗanda suke shugabanninsu.
And we requested them to tell us the names of their leaders, in order that we could tell you who they were.
11 Wannan ita ce amsar da suka ba mu. “Mu bayin Allah na sama da ƙasa ne, muna sāke gina haikalin da aka gina tun shekaru da yawa da suka wuce, da wani babban sarkin Isra’ila ya gina ya kuma gama.
“But [instead of telling us their leaders’ names, ] what they said was, ‘We serve the God [who created] the heaven and the earth. Many years ago a great king [who ruled] us Israeli people [told our ancestors to] build a temple here, and now we are rebuilding it.
12 Amma domin kakanninmu sun ɓata wa Allah na sama rai, sai ya bari suka fāɗa cikin hannun Nebukadnezzar mutumin Kaldiya, sarkin Babilon, wanda ya rushe wannan haikali, ya kuma kwashe mutane zuwa Babilon.
“'But God, [who rules] in heaven, allowed [the armies of] Nebuchadnezzar, King of Babylonia, to destroy that temple, because our ancestors did things that caused God to become very angry. Nebuchadnezzar’s army took [many of] the [Israeli] people to Babylonia.
13 “Duk da haka, a shekara ta farko ta mulkin Sairus sarkin Babilon, Sarki Sairus ya ba da umarni cewa a sāke gina wannan gidan Allah.
“'However, during the first year that Cyrus the King of Babylon started to rule, he decreed that the temple of God should be rebuilt.
14 Ya kuma kwashe kwanonin zinariya da azurfa na gidan Allah daga haikalin Babilon waɗanda Nebukadnezzar ya kwasa daga haikali a Urushalima. Sa’an nan sarki Sairus ya ba wa wani mutum mai suna Sheshbazzar umarni wanda ya sa ya zama gwamna,
Cyrus returned [to the Jewish leaders] all the gold and silver cups that had been taken from the temple in Jerusalem and which had been put in the temple in Babylon. Those cups were given to a man named Sheshbazzar, whom King Cyrus had appointed to be the governor in Judah.
15 ya ce masa, ‘Ka kwashe kayan nan ka je ka zuba su a cikin haikalin Allah a Urushalima. Ka kuma sāke gina gidan Allah a wurin da yake a dā.’
“'The king instructed him to take the cups back to Jerusalem, to the place [from which they had previously been taken]. He also decreed that they should rebuild the temple at the place where it had been before. So Cyrus appointed Sheshbazzar to be the governor in Judah. He also sent all those things made of gold and silver, for Sheshbazzar to put in the new temple.
16 “Saboda haka Sheshbazzar ya so ya aza harsashin gina gidan Allah a Urushalima. Tun daga wancan lokaci har zuwa yau ana kan gina shi amma ba a gama ba.”
So Sheshbazzar did that. He came here to Jerusalem, and [supervised the men who] laid the foundation of the temple. And since that time, the people have been working on the temple, but it is not finished yet.’
17 Yanzu in sarki yana so, bari a duba cikin littattafan tarihi na sarakuna na Babilon a gani ko lalle sarki Sairus ya ba da umarni a sāke gina gidan Allah a Urushalima. Bari sarki yă aiko mana da abin da ya gani game da wannan abu.
“Therefore, your majesty, please order someone to search in the place in Babylon where the important records are kept, to find out whether [it is true that] King Cyrus decreed that God’s temple should be rebuilt in Jerusalem. Then you can tell us what you want us to do about this matter.”

< Ezra 5 >